< マタイの福音書 13 >
A waccan rana Yesu ya fito daga gida ya zauna a gefen teku.
2 大なる群衆みもとに集りたれば、イエスは舟に乘りて坐したまひ、群衆はみな岸に立てり。
Taro mai yawan gaske kuwa suka kewaye shi, sai ya shiga cikin kwalekwale ya zauna. Dukan taron kuwa na tsaye a bakin tekun.
3 譬にて數多のことを語りて言ひたまふ、『視よ、種 播く者まかんとて出づ。
Sai Yesu ya fada masu abubuwa da yawa cikin misalai. Ya ce, “Wani mai shuka, ya tafi yayi shuka.
4 播くとき路の傍らに落ちし種あり、鳥きたりて啄む。
Da yayi shukar, wadansu irin suka fadi a kan hanya, sai tsunsaye suka zo suka cinye su.
5 土うすき磽地に落ちし種あり、土 深からぬによりて速かに萠え出でたれど、
Wadansu irin kuwa suka fadi a kan duwatsu, wurin da babu kasa. Nan da nan sai suka tsira, domin kasar babu zurfi.
Amma da rana ta taso, sai suka yankwane domin ba su yi saiwa ba, suka kuwa bushe suka zube.
Wasu irin kuwa suka fada a cikin kayayuwa. Kayayuwan kuwa suka shake su.
8 良き地に落ちし種あり、あるひは百 倍、あるひは六十 倍、あるひは三十 倍の實を結べり。
Wasu irin kuwa suka fada a wuri mai kyau suka ba da tsaba, wani ya ba da dari, wasu sitin, wasu kuma talatin.
Duk mai kunnen ji, bari ya ji.
10 弟子たち御許に來りて言ふ『なにゆゑ譬にて彼らに語り給ふか』
Almajiran suka zo suka ce ma Yesu, “Don me ka ke yi wa taron magana da misali?”
11 答へて言ひ給ふ『なんぢらは天國の奧義を知ることを許されたれど、彼らは許されず。
Yesu ya amsa ya ce masu, “An baku 'yanci ku fahimci asiran mulkin sama, amma gare su ba a bayar ba.
12 それ誰にても、有てる人は與へられて愈々 豐ならん。されど有たぬ人は、その有てる物をも取らるべし。
Domin wanda yake da shi, za a kara masa, zai kuma samu dayawan gaske. Amma duk wanda ba shi da shi, sai a dauke har ma abin da yake dashi.
13 この故に彼らには譬にて語る、これ彼らは見ゆれども見ず、聞ゆれども聽かず、また悟らぬ故なり、
Saboda haka na yi masu magana cikin misalai, amma ko da ya ke sun gani, duk da haka ba su gani ba. Kuma ko da yake sun ji, hakika ba su ji ba, balle ma su fahimta.
14 かくてイザヤの預言は、彼らの上に成就す。曰く、「なんぢら聞きて聞けども悟らず、見て見れども認めず。
A gare su ne annabcin Ishaya ya cika, wanda yake cewa, “Game da sauraro zaku saurara, amma ba za ku fahimta ba. Game da gani kuma za ku kalla, amma ba za ku gane ba.
15 この民の心は鈍く、耳は聞くに懶く、目は閉ぢたればなり。これ目にて見、耳にて聽き、心にて悟り、飜へりて、我に醫さるる事なからん爲なり」
Domin zuciyar mutanen nan ta duhunta, sun taurare ga saurare, kuma sun rufe idanunsu domin kada su gani da idanunsu, ko kuwa su ji da kunnuwansu, ko kuwa su fahimta da zukatansu, saboda su juyo kuma in warkar da su'.
16 されど汝らの目なんぢらの耳は、見るゆゑに聞くゆゑに、幸福なり。
Amma idanunku masu albarka ne, domin sun gani, haka ma kunnuwanku, domin sun ji.
17 まことに汝らに告ぐ、多くの預言者・義人は、汝らが見る所を見んとせしが見ず、なんぢらが聞く所を聞かんとせしが聞かざりしなり。
Hakika ina gaya muku, annabawa da mutane dayawa masu aldalci sun yi marmarin ganin abin da kuka gani, amma ba su sami ganin su ba. Sun yi marmarin jin abin da kuka ji, ba su kuwa ji su ba.
Ku saurari misalin nan na mai shuka.
19 誰にても天國の言をききて悟らぬときは、惡しき者きたりて、其の心に播かれたるものを奪ふ。路の傍らに播かれしとは斯かる人なり。
Idan wani ya ji maganar mulkin sama amma bai fahimce ta ba, sai mugun nan ya zo ya kwace abinda aka shuka a zuciyarsa. Wannan shine irin da aka shuka a kan hanya.
20 磽地に播かれしとは、御言をききて、直ちに喜び受くれども、
Shi wanda aka shuka akan duwatsu, shine wanda ya ji maganar ya kuma karbe ta da murna nan da nan.
21 己に根なければ暫し耐ふるのみにて、御言のために艱難あるひは迫害の起るときは、直ちに躓くものなり。
Duk da haka, bai yi karfi cikin ta ba kuma nan ba da dadaiwa ba. Da wahala da tsanani suka taso saboda maganar, sai ya yi tuntube nan da nan.
22 茨の中に播かれしとは、御言をきけども、世の心勞と財貨の惑とに、御言を塞がれて實らぬものなり。 (aiōn )
Shi wanda aka shuka a cikin kayayuwa wannan shine wanda ya ji maganar, amma dawainiyar duniya da kuma yaudarar dukiya suka shake maganar, sai ya kasa ba da 'ya'ya. (aiōn )
23 良き地に播かれしとは、御言をききて悟り、實を結びて、あるひは百 倍、あるひは六十 倍、あるひは三十 倍に至るものなり』
Shi wanda aka shuka a kasa mai kyau, wannan shine wanda ya ji maganar, ya kuma fahimce ta. Wannan shine wanda ba da 'ya'ya da gaske; wadansu ribi dari, wadansu sittin, wasu kuma talatin.”
24 また他の譬を示して言ひたまふ『天國は良き種を畑にまく人のごとし。
Yesu ya sake ba su wani misali, yana cewa “Za a kwatanta mulkin sama da wani mutum wanda ya shuka iri mai kyau a gona.
25 人々の眠れる間に、仇きたりて麥のなかに毒 麥を播きて去りぬ。
Amma da mutane suka yi barci, magabcin sa ya zo ya shuka ciyayi a cikin alkamar, ya kuwa yi tafiyarsa.
26 苗はえ出でて實りたるとき、毒 麥もあらはる。
Sa'adda suka yi toho suka kuma ba da tsaba, sai ciyayin suka bayyana.
27 僕ども來りて家主にいふ「主よ、畑に播きしは良き種ならずや、然るに如何にして毒 麥あるか」
Bayin mai gonar kuwa suka zo suka ce masa, maigida, ashe ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? ya ya aka yi ta kasance da ciyayi?
28 主人いふ「仇のなしたるなり」僕ども言ふ「さらば我らが往きて之を拔き集むるを欲するか」
Ya ce masu, “Magabci ne ya yi wannan”. Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?'
29 主人いふ「いな、恐らくは毒 麥を拔き集めんとて、麥をも共に拔かん。
Mai gonar ya ce, 'A'a, kada a garin tuge ciyayin, ku tuge tare da alkamar.
30 兩ながら收穫まで育つに任せよ。收穫のとき我かる者に「まづ毒 麥を拔きあつめて、焚くために之を束ね、麥はあつめて我が倉に納れよ」と言はん」』
Bari dukan su su girma tare har lokacin girbi, a lokacin girbin zan gaya wa masu girbin, “Ku tuge ciyayin da farko a daura su dami dami sai a kona su, amma a tara alkamar a kai rumbunana.'”
31 また他の譬を示して言ひたまふ『天國は一粒の芥種のごとし、人これを取りてその畑に播くときは、
Sai Yesu ya sake yin magana da su cikin misalai, yana cewa “Za a kwatanta mulkin sama da kwayar mustad, wanda wani mutum ya shuka a lambunsa.
32 萬の種よりも小けれど、育ちては他の野菜よりも大く、樹となりて、空の鳥きたり其の枝に宿るほどなり』
Wannan iri shine mafi kankanta cikin dukan iri. Amma bayan ya yi girma, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun. Ya zama itace, har ma tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa.”
33 また他の譬を語りたまふ『天國はパンだねのごとし、女これを取りて、三 斗の粉の中に入るれば、ことごとく脹れいだすなり』
Yesu ya sake fada masu wani misali. “Za a kwatanta mulkin sama da yisti da mace takan dauka ta kwaba gari da shi mudu uku har sai ya yi kumburi.”
34 イエスすべて此 等のことを、譬にて群衆に語りたまふ、譬ならでは何事も語り給はず。
Duk wadannan abubuwa Yesu ya fada wa taron cikin misalai. Babu abinda ya fada masu da ba a cikin misali ba.
35 これ預言者によりて云はれたる言の成就せん爲なり。曰く、『われ譬を設けて口を開き、世の創より隱れたる事を言ひ出さん』
Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, “Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya.”
36 ここに群衆を去らしめて、家に入りたまふ。弟子たち御許に來りて言ふ『畑の毒 麥の譬を我らに解きたまへ』
Sai Yesu ya bar taron ya shiga cikin gida. Amajiransa suka zo wurin sa suka ce, “Ka fasarta mana misalan nan a kan ciyayin da ke gonar”
37 答へて言ひ給ふ『良き種を播く者は人の子なり、
Yesu ya amsa kuma ya ce, “Shi wanda ya shuka iri mai kyau Dan Mutum ne.
38 畑は世界なり、良き種は天國の子どもなり、毒 麥は惡しき者の子どもなり、
Gonar kuwa duniya ce; iri mai kyau kuma sune 'ya'yan mulkin. Ciyayin kuma sune 'ya'yan mugun,
39 之を播きし仇は惡魔なり、收穫は世の終なり、刈る者は御使たちなり。 (aiōn )
magabcin da ya shuka su kuma shaidan ne. Girbin shine karshen duniya, kuma masu girbin sune mala'iku. (aiōn )
40 されば毒 麥の集められて火に焚かるる如く、世の終にも斯くあるべし。 (aiōn )
Saboda haka, kamar yadda aka tara ciyayin aka kona su da wuta, haka ma zai faru a karshen duniya. (aiōn )
41 人の子その使たちを遣さん。彼ら御國の中より凡ての顛躓となる物と不法をなす者とを集めて、
Dan Mutum zai aiki mala'ikunsa, kuma su tara dukan abubuwan da ke sa zunubi daga cikin mulkinsa, da kuma wadanda su ka yi aikin mugunta.
42 火の爐に投げ入るべし、其處にて哀哭・切齒することあらん。
Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora.
43 其のとき義人は父の御國にて日のごとく輝かん。耳ある者は聽くべし。
Sa'an nan ne mutane masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Bari mai kunnen ji, ya ji.
44 天國は畑に隱れたる寶のごとし。人 見出さば、之を隱しおきて、喜びゆき、有てる物をことごとく賣りて其の畑を買ふなり。
Mulkin sama kamar dukiya ce da ke boye a gona. Mutum ya samu sai ya boye ta, ya tafi cikin murna, ya sayar da mallakarsa kuma ya sayi filin.
Haka ma za a kwatanta mulkin sama da wani attajiri mai neman Lu'ulu'ai masu daraja.
46 價たかき眞珠 一つを見出さば、往きて有てる物をことごとく賣りて、之を買ふなり。
Da ya sami lu'ulu'u daya mai darajar gaske, ya je ya sayar da dukan mallakarsa ya kuma saye shi.
47 また天國は、海におろして各樣のものを集むる網のごとし。
Haka kuma, za a kwatanta mulkin sama da taru da aka jefa cikin teku, ya kuwa tara hallitu iri-iri.
48 充つれば岸にひきあげ、坐して良きものを器に入れ、惡しきものを棄つるなり。
Da ya cika, sai masuntan suka jawo shi bakin tekun. Sai suka zauna suka tara kyawawan abubuwan a taska, amma munanan abubuwan, suka watsar da su.
49 世の終にも斯くあるべし。御使たち出でて、義人の中より惡人を分ちて、 (aiōn )
Haka zai kasance a karshen duniya. Mala'iku za su zo su ware miyagu daga cikin masu adalci. (aiōn )
50 之を火の爐に投げ入るべし。其處にて哀哭・切齒することあらん。
Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora.
51 汝 等これらの事をみな悟りしか』彼 等いふ『然り』
Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, “I”.
52 また言ひ給ふ『この故に、天國のことを教へられたる凡ての學者は、新しき物と舊き物とをその倉より出す家主のごとし』
Sai Yesu ya ce masu, “Saboda haka kowane malamin attaura da ya zama almajirin mulkin sama, yana kamar mutum mai gida wanda ya zaro tsoho da sobon abu daga taskarsa.”
Daga nan, sa'adda Yesu ya kammala ba da wadanan misalai, sai ya tafi ya bar wurin.
54 己が郷にいたり、會堂にて教へ給へば、人々おどろきて言ふ『この人はこの智慧と此 等の能力とを何處より得しぞ。
Sai Yesu ya shiga yankinsa ya koyar da mutane a masujadarsu. Saboda haka suka yi mamaki suna cewa, “Daga ina wannan mutumin ya sami hikimarsa da al'ajibai?
55 これ木匠の子にあらずや、其の母はマリヤ、其の兄弟はヤコブ、ヨセフ、シモン、ユダにあらずや。
Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba?
56 又その姉妹も皆われらと共にをるに非ずや。然るに此 等のすべての事は何處より得しぞ』
Ba 'yan'uwansa mata na tare da mu ba? To daga ina wannan mutumin ya sami dukan wadannnan abubuwa?
57 遂に人々かれに躓けり。イエス彼らに言ひたまふ『預言者は、おのが郷おのが家の外にて尊ばれざる事なし』
Suka bata rai saboda shi. Amma Yesu ya ce masu, “Ai annabi bai rasa daraja sai dai ko a garinsa da kuma cikin iyalinsa.
58 彼らの不 信仰によりて其處にては多くの能力ある業を爲し給はざりき。
Kuma bai yi al'ajibai dayawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.