< ルカの福音書 1 >
1 我らの中に成りし事の物語につき、始よりの目撃者にして、
Mutane da dayawa sun yi kokarin rubutu akan abubuwan da suka cika a tsakaninmu,
2 御言の役者となりたる人々の、我らに傳へし其のままを書き列ねんと、手を著けし者あまたある故に、
kamar yanda suka danka mana su, wadanda tun daga farko suka zama shaidu da idanunsu kuma manzanni ne na sakon.
Sabili da haka, ni ma, bayan da na yi bincike da kyau akan yanayin wadannan abubuwa tun da farko na ga ya yi kyau in rubuta wadannan abubuwa bi da bi ya mafi girmaTiyofilas.
4 テオピロ閣下よ、汝の教へられたる事の慥なるを悟らせん爲に、これが序を正して書き贈るは善き事と思はるるなり。
Ya zama haka domin ka san gaskiyar abin da aka koya maka ne.
5 ユダヤの王ヘロデの時、アビヤの組の祭司に、ザカリヤという人あり。その妻はアロンの裔にて、名をエリサベツといふ。
A cikin zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, akwai wani firist mai suna Zakariya, daga yankin Abija. Matarsa daga cikin yaya mata na zuriyar Haruna ce, kuma sunan ta Alisabatu ne.
6 二人ながら神の前に正しくして、主の誡命と定規とを、みな缺なく行へり。
Dukan su biyu masu adalci ne a gaban Allah; marasa zargi a tafiyarsu cikin dukan dokoki da farilan Ubangiji.
7 エリサベツ石女なれば、彼らに子なし、また二人とも年 邁みぬ。
Amma ba su da da, domin Alisabatu ba ta haihuwa, kuma a wannan lokacin dukansu sun tsufa kwarai.
8 さてザカリヤその組の順番に當りて、神の前に祭司の務を行ふとき、
Ya zama kuma a lokacin da Zakariya yana gaban Allah, yana yin hidimar sa ta firist bisa ga tsari da ka'idar aikinsa.
9 祭司の慣例にしたがひて、籤をひき主の聖所に入りて、香を燒くこととなりぬ。
Bisa ga al'adar zaben firist da zai yi hidima, an zabe shi ta wurin kuri'a ya shiga cikin haikalin Ubangiji domin ya kona turare.
10 香を燒くとき、民の群みな外にありて祈りゐたり。
Dukan taron Jama'a suna addu'a a waje a sa'adda ake kona turaren.
11 時に主の使あらはれて、香壇の右に立ちたれば、
A lokacin, mala'ikan Ubangiji ya bayana a gare shi yana tsaye a gefen daman bagadi na turaren.
Zakariya ya firgita sa'adda ya gan shi; tsoro ya kama shi.
13 御使いふ『ザカリヤよ、懼るな、汝の願は聽かれたり。汝の妻エリサベツ男子を生まん、汝その名をヨハネと名づくべし。
Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya, domin an ji addu'ar ka. Matar ka Alisabatu za ta haifa maka da. Za ka kira sunansa Yahaya.
14 なんぢに喜悦と歡樂とあらん、又おほくの人もその生るるを喜ぶべし。
Za ka yi murna da farin ciki, kuma da yawa za su yi murna da haifuwarsa.
15 この子、主の前に大ならん、また葡萄酒と濃き酒とを飮まず、母の胎を出づるや聖 靈にて滿されん。
Domin zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba zai sha ruwan inabi ba ko wani abu mai sa maye, kuma zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun daga cikin cikin mahaifiyarsa.
16 また多くのイスラエルの子らを、主なる彼らの神に歸らしめ、
Kuma mutanen Isra'ila da yawa za su juya zuwa ga Ubangiji Allahnsu.
17 且エリヤの靈と能力とをもて、主の前に往かん。これ父の心を子に、戻れる者を義人の聰明に歸らせて、整へたる民を主のために備へんとてなり』
Zai yi tafiya a gaban Unbangiji a cikin ruhu da ikon Iliya. Zai yi haka domin ya juya zuciyar Ubanni zuwa ga 'ya'yansu, domin marasa biyayya su yi tafiya a cikin tafarkin adalai. Don ya shirya wa Ubangiji mutanen da aka shirya dominsa.”
18 ザカリヤ御使にいふ『何に據りてか此の事あるを知らん。我は老人にて、妻もまた年 邁みたり』
Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta yaya zan san wannan? Ga shi na tsufa kuma matata tana da shekaru da yawa.”
19 御使こたへて言ふ『われは神の御前に立つガブリエルなり、汝に語りてこの嘉き音信を告げん爲に遣さる。
Mala'ikan ya amsa ya ce masa, “Nine Jibra'ilu, wanda ke tsaye a gaban Allah. An aiko ni in gaya maka wannan labari mai dadi.
20 視よ、時いたらば必ず成就すべき我が言を信ぜぬに因り、なんぢ物 言へずなりて、此らの事の成る日までは語ること能はじ』
Kuma duba, za ka zama bebe, ba za ka iya magana ba, sai ran da wadannan abubuwa suka cika. Ya zama haka domin ba ka gaskanta da kalmomina ba, wadanda za su cika a daidai lokacin.”
21 民はザカリヤを俟ちゐて、其の聖所の内に久しく留るを怪しむ。
Sa'adda mutane suke jiran Zakariya. Sun yi mamaki yadda ya dauki lokaci sosai a cikin haikali.
22 遂に出で來りたれど語ること能はねば、彼らその聖所の内にて異象を見たることを悟る。ザカリヤは、ただ首にて示すのみ、なほ唖なりき。
Amma da ya fita, bai iya yin magana da su ba. Sun gane da cewa ya ga wahayi lokacin da yake cikin haikali. Ya ci gaba da yi masu alamu, ba ya magana.
Ya zama bayan da kwanakin hidimarsa suka kare, ya tafi gidansa.
24 此の後その妻エリサベツ孕りて、五月ほど隱れをりて言ふ、
Bayan kwanakin nan, matarsa Alisabatu ta samu juna biyu. Ta boye kanta har na watani biyar. Ta ce,
25 『主わが恥を人の中に雪がせんとて、我を顧み給ふときは、斯く爲し給ふなり』
“Wannan shi ne abin da Allah ya yi mani da ya dube ni domin ya dauke kunyata a gaban jama'a.”
26 その六月めに、御使ガブリエル、ナザレといふガリラヤの町にをる處女のもとに、神より遣さる。
A cikin watan ta na shidda, an aiki Mala'ika Jibra'ilu daga wurin Allah zuwa wani birni a Galili mai suna Nazarat,
27 この處女はダビデの家のヨセフといふ人と許嫁せし者にて、其の名をマリヤと云ふ。
zuwa ga wata budurwa wanda aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu. Shi dan zuriyar Dauda ne, kuma ana kiran budurwar Maryamu.
28 御使、處女の許にきたりて言ふ『めでたし、惠まるる者よ、主なんぢと偕に在せり』
Ya zo wurin ta ya ce, “A gaishe ki, ke da ki ke da tagomashi sosai! Ubangiji yana tare da ke.
29 マリヤこの言によりて心いたく騷ぎ、斯かる挨拶は如何なる事ぞと思ひ廻らしたるに、
Amma ta damu kwarai da wadannan kalmomi sai ta yi tunani ko wacce irin gaisuwa ce wannan.
30 御使いふ『マリヤよ、懼るな、汝は神の御前に惠を得たり。
Mala'ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, domin kin samu tagomashi a wurin Allah.
31 視よ、なんぢ孕りて男子を生まん、其の名をイエスと名づくべし。
Duba, za ki sami juna biyu, za ki haifi da. Za ki kira sunansa 'Yesu'.
32 彼は大ならん、至高者の子と稱へられん。また主たる神、これに其の父ダビデの座位をあたへ給へば、
Zai zama mai girma, kuma za a ce da shi Dan Allah Madaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dauda.
33 ヤコブの家を永遠に治めん。その國は終ることなかるべし』 (aiōn )
Zai yi mulkin dukkan gidan Yakubu har abada, kuma mulkinsa ba shi da iyaka.” (aiōn )
34 マリヤ御使に言ふ『われ未だ人を知らぬに、如何にして此の事のあるべき』
Maryamu ta ce wa mala'ikan, “Yaya wannan zai faru, tun da shike ni ban san namiji ba?”
35 御使こたへて言ふ『聖 靈なんぢに臨み、至高者の能力なんぢを被はん。此の故に汝が生むところの聖なる者は、神の子と稱へらるべし。
Mala'ikan ya amsa ya ce mata, “Ruhu Mai-tsarki zai sauko a kan ki, kuma ikon Madaukaki zai lullube ki. Sabili da haka, za a kira mai tsarkin da za ki haifa Dan Allah.
36 視よ、なんぢの親族エリサベツも、年 老いたれど、男子を孕めり。石女といはれたる者なるに、今は孕りてはや六月になりぬ。
Ki kuma duba, ga 'yar'uwarki Alisabatu ta samu juna biyu a tsufanta. Watannin ta shida kenan, ita wadda aka kira ta bakarariya.
Gama babu abin da ba shi yiwuwa a wurin Allah.”
38 マリヤ言ふ『視よ、われは主の婢女なり。汝の言のごとく、我に成れかし』つひに御使はなれ去りぬ。
Maryamu ta ce, “To, ni baiwar Ubangiji ce. Bari ya faru da ni bisa ga sakonka.” Sai mala'ikan ya bar ta.
39 その頃マリヤ立ちて山里に急ぎ往き、ユダの町にいたり、
Sai Maryamu ta tashi da sauri a cikin kwanakin nan, zuwa kasa mai duwatsu, zuwa wani birni a Yahudiya.
40 ザカリヤの家に入りてエリサベツに挨拶せしに、
Ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Alisabatu.
41 エリサベツその挨拶を聞くや、兒は胎内にて躍れり。エリサベツ聖 靈にて滿され、
Ya zama sa'adda Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, sai dan da ke cikinta ya yi tsalle, an cika Alisabatu kuma da Ruhu Mai Tsarki.
42 聲 高らかに呼はりて言ふ『をんなの中にて汝は祝福せられ、その胎の實もまた祝福せられたり。
Ta daga murya, ta ce, “Mai albarka kike a cikin mata, kuma mai albarka ne dan cikinki.
43 わが主の母われに來る、われ何によりてか之を得し。
Kuma don me ya faru da ni da uwar Ubangijina ta ziyarce ni?
44 視よ、なんぢの挨拶の聲、わが耳に入るや、我が兒、胎内にて喜びをどれり。
Kuma duba, da na ji karar gaisuwan ki sai dan ciki na ya yi tsalle domin murna.
45 信ぜし者は幸福なるかな、主の語り給ふことは必ず成就すべければなり』
Kuma mai albarka ce wadda ta gaskanta cewa abubuwan da aka alkawarta mata daga wurin Ubangiji za su cika.
Maryamu ta ce, “Zuciyata ta yabi Ubangiji,
kuma ruhu na ya yi murna da Allah mai ceto na.”
48 その婢女の卑しきをも顧み給へばなり。視よ、今よりのち萬 世の人われを幸福とせん。
Domin ya dubi kaskancin baiwarsa. Duba, daga yanzu, dukkan tsararraki za su ce da ni mai albarka.
49 全能者われに大なる事を爲したまへばなり。その御名は聖なり、
Domin shi madaukaki ya yi mani manyan abubuwa, kuma sunansa Mai Tsarki ne.
50 そのあはれみは代々かしこみ恐るる者に臨むなり。
Jinkansa ya tabbata daga tsara zuwa tsara wadanda suke girmama shi.
51 神は御腕にて權力をあらはし、心の念に高ぶる者を散し、
Ya nuna karfinsa da hannuwansa; ya warwatsa ma su girman kai game da tunanin zuciyarsu.
52 權勢ある者を座位より下し、いやしき者を高うし、
Ya nakasar da magada daga kursiyoyinsu, ya kuma fifita nakasassu.
53 飢ゑたる者を善き物に飽かせ、富める者を空しく去らせ給ふ。
Ya ciyar da mayunwata da abubuwa masu kyau, amma ya aiki attajirai wofi.
Ya ba da taimako ga bawan sa Isra'ila, domin ya tuna ya kuma nuna jinkai
55 アブラハムとその裔とに對するあはれみを永遠に忘れじとて、僕イスラエルを助けたまへり』 (aiōn )
(kamar yanda ya fada wa ubaninmu) ga Ibrahim da zuriyarsa har abada.” (aiōn )
56 かくてマリヤは、三月ばかりエルザベツと偕に居りて、己が家に歸れり。
Maryamu ta zauna da Alisabatu tsawon watanni uku sai ta koma gidanta.
57 さてエリサベツ産む期みちて男子を生みたれば、
Da lokaci yayi da Alisabatu za ta haifi danta, ta kuma haifi da namiji.
58 その最寄のもの親族の者ども、主の大なる憐憫をエリサベツに垂れ給ひしことを聞きて、彼とともに喜ぶ。
Makwabtanta da 'yan'uwanta sun ji cewa Ubangiji ya ribanbanya jinkansa akanta, sai suka yi murna tare da ita
59 八日めになりて、其の子に割禮を行はんとて人々きたり、父の名に因みてザカリヤと名づけんとせしに、
Ya zama akan rana ta takwas, sun zo domin a yi wa yaron kaciya. Da sun kira sunansa “Zakariya” kamar sunan ubansa,
amma mahaifiyarsa ta amsa ta ce, “A'a, za a kira shi Yahaya.”
61 かれら言ふ『なんぢの親族の中には此の名をつけたる者なし』
Suka ce mata, “Babu wani a cikin danginku wanda ake kira da wannan suna.”
62 而して父に首にて示し、いかに名づけんと思ふか、問ひたるに、
Sun nuna alama ga ubansa bisa ga yanda ya ke so a rada masa suna.
63 ザカリヤ書板を求めて『その名はヨハネなり』と書きしかば、みな怪しむ。
Ubansa ya nemi a ba shi allon rubutu, sai ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Dukan su suka yi mamaki kwarai da wannan.
64 ザカリヤの口たちどころに開け、舌ゆるみ、物いひて神を讃めたり。
Nan take, sai bakinsa ya bude kuma harshensa ya saki. Ya yi magana ya kuma yabi Allah.
65 最寄に住む者みな懼をいだき、又すべて此 等のこと徧くユダヤの山里に言ひ囃されたれば、
Tsoro ya kama dukan wadanda suke zama kewaye da su. Sai labarin ya bazu cikin dukan kasar duwatsu ta Yahudiya.
66 聞く者みな之を心にとめて言ふ『この子は如何なる者にか成らん』主の手かれと偕に在りしなり。
Kuma dukan wadanda suka ji su, sun ajiye su a cikin zuciyarsu, suna cewa, “To me wannan yaro zai zama ne?” Domin hannun Ubangiji yana nan tare da shi.
67 かくて父ザカリヤ聖 靈にて滿され預言して言ふ、
Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya sai ya yi anabci cewa,
68 『讃むべきかな、主イスラエルの神、その民をかへりみて贖罪をなし、
“Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra'ila domin ya zo ya taimaki mutanen sa kuma ya yi aikin ceto domin su.”
69 我らのために救の角を、その僕ダビデの家に立て給へり。
Ya ta da kahon ceto dominmu daga gidan bawansa Dauda, daga zuriyar Dauda bawansa,
70 これぞ古へより聖 預言者の口をもて言ひ給ひし如く、 (aiōn )
kamar yadda ya fada ta bakin annabawansa tsarkaka tun zamanin zamanai. (aiōn )
71 我らを仇より、凡て我らを憎む者の手より、取り出したまふ救なる。
Zai kawo mana ceto daga magabtan mu da kuma daga hannun makiyanmu.
72 我らの先祖に憐憫を垂れ、その聖なる契約を思し、
Zai yi haka domin ya nuna jinkai ga ubaninmu ya kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
73 我らの先祖アブラハムに立て給ひし御誓を忘れずして、
rantsuwar da ya fada wa ubanmu Ibrahim.
Ya rantse zai yardar mana, bayan da an kubutar da mu daga hannun makiyanmu, mu bauta masa ba tare da tsoro ba,
a cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakin ranmu.
76 幼兒よ、なんぢは至高者の預言者と稱へられん。これ主の御前に先だちゆきて、其の道を備へ、
I, kai kuma, yaro, za a kira ka annabi na Madaukaki, domin za ka tafi gaban fuskar Ubangiji ka shirya hanyoyinsa, ka shirya mutane domin zuwansa,
domin ba mutanensa ilimin ceto ta wurin gafarar zunubansu.
78 これ我らの神の深き憐憫によるなり。この憐憫によりて朝のひかり、上より臨み、
Wannan zai faru ne domin girman jinkan Allahnmu, sabili da hasken rana daga bisa za ya zo wurinmu,
79 暗黒と死の蔭とに坐する者をてらし、我らの足を平和の路にみちびかん』
domin haskakawa akan wadanda ke zaune a cikin duhu da kuma cikin inuwar mutuwa. Zai yi hakan nan domin ya kiyaye kafafunmu zuwa hanyar salama.
80 かくて幼兒は漸に成長し、その靈 強くなり、イスラエルに現るる日まで荒野にゐたり。
Yaron ya yi girma ya kuma zama kakkarfa a cikin ruhu, yana kuma cikin jeji sai ranar bayyanuwarsa ga Isra'ila.