< ヨブ 記 17 >
1 わが氣息は已にくさり 我日すでに盡なんとし墳墓われを待つ
Na karaya, kwanakina sun kusa ƙarewa, kabari yana jirana.
2 まことに嘲弄者等わが傍に在り 我目は彼らの辨爭ふを常に見ざるを得ず
Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni; idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini.
3 願くは質を賜ふて汝みづから我の保證となりたまへ 誰か他にわが手をうつ者あらんや
“Ya Allah, ka ba ni abin da ka yi mini alkawari. Wane ne zai kāre ni?
4 汝彼らの心を閉て悟るところ無らしめたまへり 必ず彼らをして愈らしめたまはじ
Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba, saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.
5 朋友を交付して掠奪に遭しむる者は其子等の目潰るべし
In mutum ya juya wa abokansa baya don a ba shi wata lada’ya’yansa za su makance.
6 彼われを世の民の笑柄とならしめたまふ 我は面に唾せらるべき者となれり
“Allah ya sa na zama abin da kowa yake magana a kai wanda kowa yake tofa wa miyau a fuska.
7 かつまた我目は憂愁によりて昏み 肢體は凡て影のごとし
Idanuna ba sa gani sosai don baƙin ciki; jikina ya zama kamar inuwa kawai
8 義しき者は之に驚き 無辜者は邪曲なる者を見て憤ほる
Mutanen da suke masu adalci wannan abu ya ba su tsoro; marasa laifi sun tayar wa marasa tsoron Allah.
9 然ながら義しき者はその道を堅く持ち 手の潔淨き者はますます力を得るなり
Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu, waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi.
10 請ふ汝ら皆ふたたび來れ 我は汝らの中に一人も智き者あるを見ざるなり
“Amma ku zo dukanku, ku sāke gwadawa! Ba zan sami mutum ɗaya mai hikima ba a cikinku.
11 わが日は已に過ぎ わが計る所わが心に冀ふ所は已に敗れたり
Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci haka kuma abubuwan da zuciyata take so.
Mutanen nan sun juya rana ta zama dare. A tsakiyar duhu suka ce, ‘Haske yana kusa.’
13 我もし俟つところ有ば是わが家たるべき陰府なるのみ 我は黑暗にわが牀を展ぶ (Sheol )
In kabari ne begen da nake da shi kaɗai, in na shimfiɗa gadona a cikin duhu, (Sheol )
14 われ朽腐に向ひては汝はわが父なりと言ひ 蛆に向ひては汝は我母わが姉妹なりと言ふ
In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’ tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’
15 然ばわが望はいづくにかある 我望は誰かこれを見る者あらん
To, ina begena yake? Wane ne zai iya ganin wani bege domina?
16 是は下りて陰府の關に到らん 之と齊しく我身は塵の中に臥靜まるべし (Sheol )
Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne? Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?” (Sheol )