< イザヤ書 32 >
1 茲にひとりの王あり 正義をもて統治め その君たちは公平をもて宰さどらん
Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci masu mulki kuma su yi mulki da adalci.
2 また人ありて風のさけどころ暴雨ののがれどころとなり 旱ける地にある水のながれのごとく 倦つかれたる地にある大なる岩陰の如くならん
Kowane mutum zai zama kamar wurin fakewa daga iska mafaka kuma daga hadari, kamar rafuffukan ruwa a hamada da kuma inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.
3 見るものの目はくらまず 聞ものの耳はかたぶけきくをうべし
Sa’an nan idanun waɗanda suka gani ba za su ƙara rufewa ba, kunnuwan waɗanda suka ji kuma za su saurara.
4 躁がしきものの心はさとりて知識をえ 吃者の舌はすみやけくあざやかに語るをうべし
Zuciya marasa haƙuri za su sani su kuma fahimta, harshen masu ana’ana kuma zai sāke su yi magana sosai.
5 愚かなる者はふたたび尊貴とよばるることなく 狡猾なる者はふたたび大人とよばるることなかるべし
Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba ko kuwa a ɗaukaka mazambaci.
6 そは愚なるものは愚なることをかたり その心に不義をかもし邪曲をおこなひ ヱホバにむかひて妄なることをかたり 饑たる者のこころを空しくし渇けるものの飮料をつきはてしむ
Gama wawa maganar wauta yakan yi, zuciyarsa ta cika da mugunta, yana aikata abubuwan rashin sanin Allah yana baza kurakurai game da Ubangiji; yana barin mayunwata da yunwa ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha.
7 狡猾なるものの用ゐる器はあしし 彼あしき企圖をまうけ虛僞のことばをもて苦しむ者をそこなひ 乏しき者のかたること正理なるも尚これを害へり
Matakan mazambaci mugaye ne, yana ƙulla mugayen shirye-shirye don yă hallaka talakawa da ƙarairayi, ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.
8 たふとき人はたふとき謀略をまうけ恒にたふとき事をおこなふ
Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki, kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki.
9 安逸にをる婦等よおきてわが聲をきけ 思煩ひなき女等よわが言に耳を傾けよ
Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ku tashi ku saurare ni; ku’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya, ku ji abin da zan faɗa!
10 思煩ひなきをんなたちよ一年あまりの日をすぎて摺きあわてん そは葡萄の収穫むなしく果ををさむる期きたるまじければなり
Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki; girbin’ya’yan inabi zai kāsa, girbin’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.
11 やすらかにをる婦等よふるひおそれよ おもひわづらひなき者よをののきあわてよ 衣をぬぎ裸體になりて腰に麁服をまとへ
Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi, ku sha wahala, ku’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya! Ku tuɓe rigunanku, ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.
12 かれら良田のため實りゆたかなる葡萄の樹のために胸をうたん
Ku bugi ƙirjinku don gonaki masu kyau don’ya’yan inabi
13 棘と荊わが民の地にはえ 樂みの邑なるよろこびの家々にもはえん
da kuma don ƙasar mutanena, da ƙasar da ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suka yi girma, I, ku yi kuka saboda dukan gidajen da dā ake biki da kuma domin wannan birnin da dā ake murna a ciki.
14 そは殿はすてられ にぎはひたる邑はあれすたれ オペルと櫓とはとこしへに洞穴となり 野の驢馬のたのしむところ羊のむれの草はむところとなるべし
Za a ƙyale kagarar, a gudu a bar birnin da dā ake hayaniya; mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada, jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna,
15 されど遂には靈うへより我儕にそそぎて 荒野はよき田となり 良田は林のごとく見ゆるとききたらん
sai an zubo Ruhu a kanmu daga sama, hamada kuma ta zama ƙasar mai taƙi, gona mai taƙi kuma ta zama kamar kurmi.
16 そのとき公平はあれのにすみ 正義はよき田にをらん
Aikin gaskiya zai zauna a hamada adalci kuma zai zauna a ƙasa mai taƙi.
17 かくて正義のいさをは平和 せいぎのむすぶ果はとこしへの平隱とやすきなり
Aikin adalci zai zama salama; tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.
18 わが民はへいわの家にをり 思ひわづらひなき住所にをり 安らかなる休息所にをらん
Mutanena za su zauna lafiya a wuraren salama, a gidaje masu kāriya, a wuraren hutun da babu fitina.
19 されどまづ雹ふりて林くだけ邑もことごとくたふるべし
Ko da yake ƙanƙara za tă fāɗo a jeji, a kuma rurrushe birni gaba ɗaya,
20 なんぢらもろもろの水のほとりに種をおろし 牛および驢馬の足をはなちおく者はさいはひなり
zai zama muku da albarka, ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi, kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku.