< 使徒の働き 8 >

1 サウロは彼の殺さるるを可しとせり。その日エルサレムに在る教會に對ひて大なる迫害おこり、使徒たちの他は皆ユダヤ及びサマリヤの地方に散さる。
Bulus ya amince da mutuwarsa. A wannan rana tsanani mai zafi ya fara tasowa akan Iklisiya da take a Urushalima, sai masu bangaskiya duka suka bazu ko ina a cikin garuruwan Yahudiya da Samariya, sai manzannin kadai aka bari.
2 敬虔なる人々ステパノを葬り、彼のために大に胸 打てり。
Amintattun mutane suka bizne Istifanus suka yi babban makoki game da shi.
3 サウロは教會をあらし、家々に入り男女を引出して獄に付せり。
Amma Shawulu ya yi wa Iklisiya mugunta kwarai, ya dinga shiga gida gida yana jawo mutane maza da mata, kuma yana kulle su cikin kurkuku.
4 ここに散されたる者ども歴 巡りて御言を宣べしが、
Duk da haka masu bangaskiyar nan da suka warwatsu suka tafi suka dinga yada wa'azin maganar.
5 ピリポはサマリヤの町に下りてキリストの事を傳ふ。
Filibus ya tafi can Samariya ya yi shelar Almasihu.
6 群衆ピリポの行ふ徴を見 聞して、心を一つにし、謹みて其の語る事どもを聽けり。
Da taron mutane suka ji kuma suka ga alamun da Filibus yake yi, sai suka mai da hankali dukansu domin su ji abinda yake fadi.
7 これ多くの人より、之に憑きたる穢れし靈、大聲に叫びて出で、また中風の者と跛者と多く醫されたるに因る。
Domin kazaman ruhohi sun fito daga cikin mutane da yawa da suka saurare shi suna kuka da kururuwa; nakasassun mutane dayawa da guragu suka warke.
8 この故にその町に大なる勸喜おこれり。
Kuma aka yi farin ciki mai girma a birnin.
9 ここにシモンといふ人あり、前にその町にて魔術を行ひ、サマリヤ人を驚かして自ら大なる者と稱へたり。
Amma akwai wani mutum a cikin birnin da ake kira Siman, wanda tun farko shi masafi ne da kuma dan dabo, yana yi wa mutanen Samariya abubuwan ban mamaki, yayin da yake kiran kansa wani mai muhimmanci.
10 小より大に至る凡ての人つつしみて之に聽き『この人は、いわゆる神の大能なり』といふ。
Dukan Samariyawa, manya da yara, suna sauraronsa, su kan ce, ''Wannan mutum shine ikon Allahn nan wanda ake kira mai girma.''
11 かく謹みて聽けるは、久しき間その魔術に驚かされし故なり。
Suna sauraron sa, domin ya dade yana yi masu abubuwan mamaki da tsafe-tsafensa.
12 然るにピリポが、神の國とイエス・キリストの御名とに就きて宣傳ふるを人々 信じたれば、男女ともにバプテスマを受く。
Amma da suka yi bangaskiya da wa'azin bisharar da Filibus yake yi game da mulkin Allah da sunan Yesu Almasihu, sai aka yi masu Baftisma dukansu maza da mata.
13 シモンも亦みづから信じ、バプテスマを受けて、常にピリポと偕に居り、その行ふ徴と、大なる能力とを見て驚けり。
Har shima Siman da kansa ya ba da gaskiya. Bayan an yi masa Baftisma ya cigaba da bin Filibus, da ya ga ana nuna alamu da manyan ayyuka, sai ya yi mamaki.
14 エルサレムに居る使徒たちは、サマリヤ人、神の御言を受けたりと聞きて、ペテロとヨハネとを遣したれば、
Da manzannin da ke Urushalima suka ji labarin Samariya ta karbi maganar Allah, sai suka aika masu Bitrus da Yahaya.
15 彼ら下りて人々の聖 靈を受けんことを祈れり。
Da suka iso, suka yi masu addu'a, domin su karbi Ruhu Mai Tsarki.
16 これ主イエスの名によりてバプテスマを受けしのみにて、聖 靈いまだ其の一人にだに降らざりしなり。
Domin har wannan lokaci, Ruhu Mai Tsarki bai sauko kan kowannensu ba; an dai yi masu baftisma ne kadai cikin sunan Ubangiji Yesu.
17 ここに二人のもの彼らの上に手を按きたれば、みな聖 靈を受けたり。
Sai Bitrus da Yahaya suka dora masu hannuwansu, sai suka karbi Ruhu Mai Tsarki.
18 使徒たちの按手によりて其の御靈を與へられしを見て、シモン金を持ち來りて言ふ、
Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi.
19 『わが手を按くすべての人の聖 靈を受くるやうに、此の權威を我にも與へよ』
Ya ce, “Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki.''
20 ペテロ彼に言ふ『なんぢの銀は汝とともに亡ぶべし、なんぢ金をもて神の賜物を得んと思へばなり。
Amma Bitrus yace masa, ''Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi.
21 なんぢは此の事に關係なく干與なし、なんぢの心、神の前に正しからず。
Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba.
22 然ればこの惡を悔改めて主に祈れ、なんぢが心の念あるひは赦されん。
Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka.
23 我なんぢが苦き膽汁と不義の繋とに居るを見るなり』
Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi.''
24 シモン答へて言ふ『なんぢらの言ふ所のこと一つも我に來らぬやう、汝ら我がために主に祈れ』
Siman ya amsa ya ce, ''Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni.''
25 かくて使徒たちは證をなし、主の御言を語りて後、サマリヤ人の多くの村に福音を宣傳へつつエルサレムに歸れり。
Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa.
26 然るに主の使ピリポに語りて言ふ『なんぢ起ちて南に向ひエルサレムよりガザに下る道に往け。そこは荒野なり』
Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, ''Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza'' (wannan hanyar yana cikin hamada.)
27 ピリポ起ちて往きたれば、視よ、エテオピヤの女王カンダケの權官にして、凡ての寳物を掌どる閹人エテオピヤ人あり、禮拜の爲にエルサレムに上りしが、
Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada.
28 歸る途すがら馬車に坐して預言者イザヤの書を讀みゐたり。
Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya.
29 御靈ピリポに言ひ給ふ『ゆきて此の馬車に近寄れ』
Ruhun ya ce wa Filibus, ''Ka je kusa da karussar nan.''
30 ピリポ走り寄りて、その預言者イザヤの書を讀むを聽きて言ふ『なんぢ其の讀むところを悟るか』
Sai Filibus ya gudu ya same shi, kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya, sai ya ce, ''Ka fahimci abin da kake karantawa?''
31 閹人いふ『導く者なくば、いかで悟り得ん』而してピリポに、乘りて共に坐せんことを請ふ。
Bahabashen ya ce. ''Yaya zan iya, idan ba wani ya bishe ni ba?'' Ya roki Filibus ya shigo cikin karussar ya zauna tare da shi.
32 その讀むところの聖書の文は是なり『彼は羊の屠場に就くが如く曳かれ、羔羊のその毛を剪る者のまへに默すがごとく口を開かず。
Wannan kuwa shine nassin da Bahabashen yake karantawa, ''An kai shi kamar tunkiya zuwa mayanka; shiru kuma, kamar dan rago a hannun masu sosayarsa, bai bude baki ba.
33 卑しめられて審判を奪はれたり、誰かその代の状を述べ得んや。その生命 地上より取られたればなり』
Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya.''
34 閹人こたへてピリポに言ふ『預言者は誰に就きて斯く云へるぞ、己に就きてか、人に就きてか、請ふ示せ』
Sai baban ya tambayi Filibus, ya ce, ''Na roke ka, gaya mani, game da wa annabin yake magana? Da kansa, ko kuwa wani mutum dabam?''
35 ピリポ口を開き、この聖 句を始としてイエスの福音を宣傳ふ。
Filibus ya fara magana; akan littafin Ishaya, ya kuwa yi masa wa'azi akan Yesu.
36 途を進むる程に水ある所に來りたれば、閹人いふ『視よ、水あり、我がバプテスマを受くるに何の障りかある』
Yayin da suke tafiya akan hanya, sai suka iso bakin wani kogi; Baban ya ce, “Duba, ga ruwa anan; me zai hana ayi mani baftisma?”
37 [なし]
Filibus ya ce,” Idan ka gaskanta da zuciya daya, ana iya yi maka baftisma.” Sai Bahabashen ya ce, “Na gaskata Yesu Almasihu shine Dan Allah.”
38 乃ち命じて馬車を止め、ピリポと閹人と二人ともに水に下りて、ピリポ閹人にバプテスマを授く。
Sai Bahabashen ya umarta a tsai da karussar. Sai suka zo wurin ruwa dukan su biyu, Filibus da baban, Filibus kuwa yayi masa baftisma.
39 彼ら水より上りしとき、主の靈ピリポを取去りたれば、閹人ふたたび彼を見ざりしが、喜びつつ其の途に進み往けり。
Yayin da suka fito daga cikin ruwan, Ruhun Ubangiji ya dauke Filibus; baban bai sake ganin shi ba, sai ya ci gaba da tafiyar sa yana murna.
40 かくてピリポはアゾトに現れ、町々を經て福音を宣傳へつつカイザリヤに到れり。
Amma Filibus ya bayyana a Azotus. Ya ratsa wannan yankin yana wa'azin bishara a dukan garuruwan, har sa'anda ya iso Kaisariya.

< 使徒の働き 8 >