< テモテへの手紙第二 4 >

1 われ神の前また生ける者と死にたる者とを審かんとし給ふキリスト・イエスの前にて、その顯現と御國とをおもひて嚴かに汝に命ず。
Ina bada wannan umarni a gaban Allah da Yesu Almasihu, wanda zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, kuma saboda bayyanuwarsa da mulkinsa:
2 なんぢ御言を宣傳へよ、機を得るも機を得ざるも常に勵め、寛容と教誨とを盡して責め、戒め、勸めよ。
Ka yi wa'azin Kalma. Ka himmantu a kai ko da zarafi ko ba zarafi. Ka tsautar, ka kwabar, ka gargadar, da dukan hakuri da koyarwa.
3 人々 健全なる教に堪へず、耳 痒くして私慾のまにまに己がために教師を増し加へ、
Gama lokaci na zuwa wanda mutane ba za su jure wa koyarwar kirki ba. Maimakon haka, zasu tattara wa kansu malamai bisa ga sha'awowin zuciyarsu. Za su rika fada masu abin da kunnuwansu ke so.
4 耳を眞理より背けて昔話に移る時 來らん。
Za su juya kunnuwansu daga koyarwar gaskiya, za su koma wa tatsunniyoyi na banza.
5 されど汝は何事にも愼み、苦難を忍び、傳道者の業をなし、なんぢの職を全うせよ。
Amma kai, sai ka natsu a cikin dukan abubuwa. Ka jure wa wahala; ka yi aikin mai bishara, ka cika hidimarka.
6 我は今 供物として血を灑がんとす、わが去るべき時は近づけり。
Gama ana-tsiyaye ni. Lokacin yin kaurata yayi.
7 われ善き戰鬪をたたかひ、走るべき道程を果し、信仰を守れり。
Na yi tsere na gaskiya; na kuma kammala tseren; na rike bangaskiya.
8 今よりのち義の冠冕わが爲に備はれり。かの日に至りて正しき審判 主なる主、これを我に賜はん、啻に我のみならず、凡てその顯現を慕ふ者にも賜ふべし。
An adana mani rawani na adalci, wanda Ubangiji, alkali mai adalci, zai ba ni a ranan nan. Ba ni kadai ba, amma kuma ga dukkan wadanda suke kaunar zuwansa.
9 なんぢ勉めて速かに我に來れ。
Ka yi iyakacin kokarinka ka zo wurina da sauri.
10 デマスは此の世を愛し、我を棄ててテサロニケに往き、クレスケンスはガラテヤに、テトスはダルマテヤに往きて、 (aiōn g165)
Domin Dimas ya yashe ni. Ya kaunaci wannan duniyar, ya tafi Tassalonika, Kariskis ya tafi Galatiya, Titus kuma ya tafi Dalmatiya. (aiōn g165)
11 唯ルカのみ我とともに居るなり。汝マルコを連れて共に來れ、彼は職のために我に益あればなり。
Luka ne kadai yake tare da ni. Ka nemo Markus ka zo tare da shi domin yana da amfani a gareni a cikin aikin.
12 我テキコをエペソに遣せり。
Na aiki Tikikus zuwa Afisus.
13 汝きたる時わがトロアスにてカルポの許に遺し置きたる外衣を携へきたれ、また書物、殊に羊皮紙のものを携へきたれ。
Ka kawo mani mayafin da na bari a Taruwasa wurin Karbus, idan za ka zo ka taho da shi, duk da littatafan nan, musanman takardun nan.
14 金 細工人アレキサンデル大に我を惱せり。主はその行爲に隨ひて彼に報いたまふべし。
Iskandari makerin dalma ya kulla mani makirci ba kadan ba. Ubangiji zai biya shi gwargwadon ayyukansa.
15 汝もまた彼に心せよ、かれは甚だしく我らの言に逆ひたり。
Kai ma ka yi hankali da shi, domin yana tsayyaya da maganganunmu sosai.
16 わが始の辯明のとき誰も我を助けず、みな我を棄てたり、願はくはこの罪の彼らに歸せざらんことを。
Da farkon kariyar kaina, babu wanda ya goyi bayana. Maimakon haka kowa ya guje ni. Bana so dai a lissafta wannan a kansu.
17 されど主われと偕に在して我を強めたまへり。これ我によりて宣教の全うせられ、凡ての異邦人のこれを聞かん爲なり。而して我は獅子の口より救ひ出されたり。
Amma Ubangiji ya kasance tare da ni, ya kuma karfafa ni, yadda ta wurina, shelar ta sami cika da kyau, domin dukan al'ummai su ji. An kwato ni daga bakin zaki.
18 また主は我を凡ての惡しき業より救ひ出し、その天の國に救ひ入れたまはん。願はくは榮光 世々 限りなく彼にあらん事を、アァメン。 (aiōn g165)
Allah zai kubutar ni daga dukan ayyukan mugunta, ya kuma cece ni domin mulkinsa na sama. Daukaka ta tabatta a gareshi har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
19 汝プリスカ及びアクラ、またオネシポロの家に安否を問へ。
Ka gayar da Briskilla, da Akila, da gidan Onisifurus.
20 エラストはコリントに留れり。トロピモは病ある故に我かれをミレトに遺せり。
Arastus ya nan zaune a Korinti, amma na bar Turufimus ya na zazzabi a Militus.
21 なんぢ勉めて冬のまへに我に來れ、ユブロ、プデス、リノス、クラウデヤ、及び凡ての兄弟、なんぢに安否を問ふ。
Ka yi iyakar kokarinka, ka zo kamin hunturu. Yubulus yana gayar da kai, haka ma Budis da Linus da Kalafidiya da dukan 'yan'uwa.
22 願はくは主なんぢの靈と偕に在し、御惠なんぢらと偕に在らんことを。
Bari Ubangiji ya kasance tare da ruhunka. Bari Alheri ya kasance da kai.

< テモテへの手紙第二 4 >