< テサロニケ人への手紙第一 5 >

1 兄弟よ、時と期とに就きては汝らに書きおくるに及ばず。
To,’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku,
2 汝らは主の日の盜人の夜きたるが如くに來ることを、自ら詳細に知ればなり。
gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare.
3 人々の平和 無事なりと言ふほどに、滅亡にはかに彼らの上に來らん、妊める婦に産の苦痛の臨むがごとし、必ず遁るることを得じ。
Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
4 されど兄弟よ、汝らは暗に居らざれば、盜人の來るごとく其の日なんぢらに追及くことなし。
Amma ku,’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.
5 それ汝 等はみな光の子ども晝の子供なり。我らは夜に屬く者にあらず、暗に屬く者にあらず。
Dukanku’ya’yan haske ne da kuma’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne.
6 されば他の人のごとく眠るべからず、目を覺して愼むべし。
Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.
7 眠る者は夜 眠り、酒に醉ふ者は夜 醉ふなり。
Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.
8 されど我らは晝に屬く者なれば、信仰と愛との胸當を著け、救の望の兜をかむりて愼むべし。
Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
9 それ神は我らを怒に遭はせんとにあらず、主イエス・キリストに頼りて救を得させんと定め給へるなり。
Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
10 主の我等のために死に給へるは、我等をして寤めをるとも眠りをるとも己と共に生くることを得しめん爲なり。
Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.
11 此の故に互に勸めて各自の徳を建つべし、これ汝らが常に爲す所なり。
Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
12 兄弟よ、汝らに求む。なんぢらの中に勞し、主にありて汝らを治め、汝らを訓戒する者を重んじ、
To, muna roƙonku,’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi.
13 その勤勞によりて厚く之を愛し敬へ。また互に相 和ぐべし。
Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.
14 兄弟よ、汝らに勸む、妄なる者を訓戒し、落膽せし者を勵まし、弱き者を扶け、凡ての人に對して寛容なれ。
Muna kuma gargaɗe ku,’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.
15 誰も人に對し惡をもて惡に報いぬやう愼め。ただ相 互に、また凡ての人に對して常に善を追ひ求めよ。
Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.
16 常に喜べ、
Ku riƙa farin ciki kullum;
17 絶えず祈れ、
ku ci gaba da yin addu’a;
18 凡てのことを感謝せよ、これキリスト・イエスに由りて神の汝らに求め給ふ所なり。
ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
19 御靈を熄すな、
Kada ku danne aikin Ruhu.
20 預言を蔑すな、
Kada ku rena annabci,
21 凡てのこと試みて善きものを守り、
amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,
22 凡て惡の類に遠ざかれ。
ku ƙi kowace mugunta.
23 願はくは平和の神、みづから汝らを全く潔くし、汝らの靈と心と體とを全く守りて、我らの主イエス・キリストの來り給ふとき責むべき所なからしめ給はん事を。
Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
24 汝らを召したまふ者は眞實なれば、之を成し給ふべし。
Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
25 兄弟よ、我らのために祈れ。
’Yan’uwa, ku yi mana addu’a.
26 きよき接吻をもて凡ての兄弟の安否を問へ。
Ku gaggai da dukan’yan’uwa da sumba mai tsarki.
27 主によりて汝らに命ず、この書を凡ての兄弟に讀み聞かせよ。
Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan’yan’uwa.
28 願はくは主イエス・キリストの恩惠、なんぢらと偕に在らんことを。
Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku.

< テサロニケ人への手紙第一 5 >