< 歴代誌Ⅰ 2 >

1 イスラエルの子等は左のごとしルベン、シメオン、レビ、ユダ、イツサカル、ゼブルン
Waɗannan su ne’ya’yan Isra’ila maza. Ruben, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Zebulun,
2 ダン、ヨセフ、ベニヤミン、ナフタリ、ガド、アセル
Dan, Yusuf, Benyamin, Naftali, Gad da Asher.
3 ユダの子等はエル、オナン、シラなり この三人はカナンの女バテシユアがユダによりて生たるなり ユダの長子エルはヱホバの前に惡き事をなしたれば之を殺したまへり
’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan da Shela. Waɗannan mutum uku Bat-shuwa mutuniyar Kan’ana ce ta haifa masa. Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.
4 ユダの媳タマルはユダによりてペレヅとゼラとを生りユダの子等は都合五人なりき
Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera. Yahuda ya haifi’ya’ya maza biyar ne.
5 ペレヅの子等はヘヅロンおよびハムル
’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.
6 ゼラの子等はジムリ、エタン、ヘマン、カルコル、ダラ都合五人
’Ya’yan Zera maza su ne, Zimri, Etan, Heman, Kalkol da Darda, su biyar ne.
7 カルミの子はアカル、アカルは詛はれし物につきて罪を犯してイスラエルを惱ませし者なり
’Ya’yan Karmi maza su ne, Akar wanda ya kawo masifa wa Isra’ila ta wurin yin abin da aka haramta.
8 エタンの子はアザリヤ
Ɗan Etan shi ne, Azariya.
9 ヘヅロンに生れたる子等はヱラメル、ラム、ケルバイ
’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne, Yerameyel, Ram da Kaleb.
10 ラム、アミナダブを生みアミナダブ、ナシヨンを生りナシヨンはユダの子孫の牧伯なり
Ram shi ne mahaifin Amminadab, Amminadab kuwa shi ne mahaifin Nashon, shugaban mutanen Yahuda.
11 ナシヨン、サルマを生みサルマ、ボアズを生み
Nashon shi ne mahaifin Salma, Salma shi ne mahaifin Bowaz,
12 ボアズ、オベデを生み、オベデ、ヱツサイを生り
Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse.
13 ヱツサイの生る者は長子はエリアブ その次はアミナダブ その三はシヤンマ
Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya,
14 その四はネタンエル その五はラダイ
na huɗun Netanel, na biyar Raddai,
15 その六はオゼム その七はダビデ
na shidan Ozem na bakwai kuma Dawuda.
16 かれらの姉妹はゼルヤとアビガル、ゼルヤの產る子はアビシヤイ、ヨアブ、アサヘルあはせて三人
’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel.’Ya’yan Zeruhiya maza guda uku su ne Abishai, Yowab da Asahel.
17 アビガルはアマサを產り アサの父はイシマエル人ヱテルといふ者なり
Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel.
18 ヘヅロンの子カレブはその妻アズバによりまたヱリオテによりて子を擧けたりその產る子等は左のごとし ヱシル、シヨバブおよびアルドン
Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon.
19 アズバ死たればカレブまたエフラタを娶れり エフラタ、カレブによりてホルを產り
Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur.
20 ホル、ウリを生み ウリ、ベザレルを生り
Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel.
21 その後ヘヅロンはギレアデの父マキルの女の所にいれりその之を娶れる時は六十歳なりき彼ヘヅロンによりてセグブを產り
Daga baya, Hezron ya kwana da’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub.
22 セグブ、ヤイルを生りヤイルはギレアデの地に邑二十三を有り
Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad.
23 然るにゲシユルおよびアラム彼等よりヤイルの邑々およびケナテとその郷里など都合六十の邑を取り是皆ギレアデの父マキルの子等なりき
(Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.
24 ヘヅロン、カレブエフテタに死て後ヘヅロンの妻アビヤその子アシユルを生りアシユルはテコアの父なり
Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa.
25 ヘヅロンの長子ヱラメルの子等は長子はラム 次はブナ、オレン、オゼム、アヒヤ
’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne, Ram shi ne ɗan fari, sai Buna, Oren, Ozem da Ahiya.
26 ヱラメルはまた他の妻をもてりその名をアタラといふ彼はオナムの母なり
Yerameyel yana da wata mata, wadda sunanta Atara; ita ce mahaifiyar Onam.
27 ヱラメルの長子ラムの子等はマアツ、ヤミン、エケル
’Ya’yan Ram maza ɗan farin Yerameyel su ne, Ma’az, Yamin da Eker.
28 オナムの子等はシヤンマイ、ヤダ、シヤンマイの子等はナダブおよびアビシユル
’Ya’yan Onam maza su ne, Shammai da Yada.’Ya’yan Shammai maza su ne, Nadab da Abishur.
29 アビシユルの妻の名はアビハイルといふ彼アバンおよびモリデを生り
Sunan matar Abishur ita ce Abihayil, wadda ta haifa masa Aban da Molid.
30 ナダブの子等はセレデおよびアツパイム、セレデは子なくして死り
’Ya’yan Nadab maza su ne, Seled da Affayim. Seled ya mutu babu yara.
31 アツパイムの子はイシ、イシの子はセシヤン、セシヤンの子はアヘライ
Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan. Sheshan shi ne mahaifin Alai.
32 シヤンマイの兄弟ヤダの子はヱテルおよびヨナタン、ヱテルは子なくして死り
’Ya’yan Yada maza, ɗan’uwan Shammai su ne, Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu babu yara.
33 ヨナタンの子等はペレテおよびザザ、ヱラメルの子孫は斯のごとし
’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel.
34 セシヤンは男子なくして惟女子ありしのみなるがセシヤンにヤルハと名くるエジプトの僕ありければ
Sheshan ba shi da’ya’ya maza, sai’ya’ya mata kawai. Yana da bawa mutumin Masar mai suna Yarha.
35 セシヤンその女をこの僕ヤルハに與へて妻となさしめたり彼ヤルハによりてアツタイを生り
Sheshan ya ba da’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai.
36 アツタイ、ナタンを生みナタン、ザバデを生み
Attai shi ne mahaifin Natan, Natan shi ne mahaifin Zabad,
37 ザバデ、エフラルを生み エフラル、オベデを生み
Zabad shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne mahaifin Obed,
38 オベデ、ヱヒウを生み ヱヒウ、アザリヤを生み
Obed shi ne mahaifin Yehu, Yehu shi ne mahaifin Azariya,
39 アザリヤ、ヘレヅを生み ヘレヅ、ヱレアサを生み
Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa,
40 ヱレアサ、シスマイを生み シスマイ、シヤルムを生み
Eleyasa shi ne mahaifin Sismai, Sismai shi ne mahaifin Shallum
41 シヤルム、ヱカミヤを生み ヱカミヤ、エリシヤマを生り
Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma shi ne mahaifin Elishama.
42 ヱラメルの兄弟カレブの子等はその長子をメシヤといふ是はジフの父なり ジフの子はマレシヤ、マレシヤはヘブロンの父なり
’Ya’yan Kaleb maza, ɗan’uwan Yerameyel su ne, Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif, da ɗansa Maresha, wanda shi ne mahaifin Hebron.
43 ヘブロンの子等はコラ、タツプア、レケム、シマ
’Ya’yan Hebron maza su ne, Kora, Taffuwa, Rekem da Shema.
44 シマはラハムを生り ラハムはヨルカムの父なり レケムはシヤンマイを生り
Shema shi ne mahaifin Raham, Raham kuma shi ne mahaifin Yorkeyam. Rekem shi ne mahaifin Shammai.
45 シヤンマイの子はマオン、マオンはベテスルの父なり
Ɗan Shammai shi ne Mawon, Mawon kuma shi ne mahaifin Bet-Zur.
46 カレブの妾エパでハラン、モザおよびガゼズを產り ハランはガゼズを生り
Efa ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Haran, Moza da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez.
47 ヱダイの子等はレゲム、ヨタム、ゲシヤン、ペレテ、エバ、シヤフ
’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af.
48 カレブの妾マアカはシベルおよびテルハナを生み
Ma’aka ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Sheber da Tirhana.
49 またマデマンナの父シヤフおよびマクベナとギベアの父シワを生り カレブの女子はアクサといふ
Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna da kuma Shewa, mahaifin Makbena da Gibeya.’Yar Kaleb ita ce Aksa.
50 カレブの子孫は左のごとしエフラタの長子ホルの子はキリアテヤリムの父シヨバル
Waɗannan su ne zuriyar Kaleb.’Ya’yan Hur maza, ɗan farin Efrata su ne, Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim,
51 ベテレヘムの父サルマおよびベテカデルの父ハレフ
Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader.
52 キリアタヤリムの父シヨバルの子等はハロエにメヌコテ人の半
Zuriyar Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim su ne, Harowe, rabin Manahatiyawa,
53 またキリアテヤリムの宗族はイテリ族プヒ族シユマ族ミシラ族 是等よりザレア族およびエシタオル族出たり
kuma gidan Kiriyat Yeyarim su ne, Itrayawa, Futiyawa, Shumatiyawa da Mishratiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.
54 サルマの子孫はベテレヘム、ネトバ族アタロテベテヨアブ、マナハテ族の半およびゾリ族
Zuriyar Salma su ne, Betlehem, Netofawa, Atrot Bet Yowab, rabin Manahatiyawa, Zoriyawa,
55 ならびにヤベヅに住る諸士の宗族すなはちテラテ族シメアテ族スカテ族是等はケニ人にしてレカブの家の先祖ハマテより出たる者なり
kuma gidan marubuta waɗanda suke zama a Yabez su ne, Tiratiyawa, Shimeyatiyawa da Sukatiyawa. Waɗannan su ne Keniyawa waɗanda suka zo daga Hammat, mahaifin gidan Rekab.

< 歴代誌Ⅰ 2 >