< 1 Cronache 16 >
1 Così introdussero e collocarono l'arca di Dio al centro della tenda eretta per essa da Davide; offrirono olocausti e sacrifici di comunione a Dio.
Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah.
2 Terminati gli olocausti e i sacrifici di comunione, Davide benedisse il popolo in nome del Signore.
Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji.
3 Distribuì a tutti gli Israeliti, uomini e donne, una pagnotta, una porzione di carne e una schiacciata d'uva.
Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace.
4 Egli stabilì che alcuni leviti stessero davanti all'arca del Signore come ministri per celebrare, ringraziare e lodare il Signore, Dio di Israele.
Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.
5 Erano Asaf il capo, Zaccaria il suo secondo, Uzzièl, Semiramot, Iechièl, Mattatia, Eliàb, Benaià, Obed-Edom e Ieièl, che suonavano strumenti musicali, arpe e cetre; Asaf suonava i cembali.
Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna,
6 I sacerdoti Benaià e Iacazièl con le trombe erano sempre davanti all'arca dell'alleanza di Dio.
Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.
7 Proprio in quel giorno Davide per la prima volta affidò ad Asaf e ai suoi fratelli questa lode al Signore:
A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.
8 Lodate il Signore, acclamate il suo nome; manifestate ai popoli le sue gesta.
Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
9 Cantate in suo onore, inneggiate a lui, ripetete tutti i suoi prodigi.
Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.
10 Gloriatevi sul suo santo nome; gioisca il cuore di quanti ricercano il Signore.
Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
11 Cercate il Signore e la sua forza, ricercate sempre il suo volto.
Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.
12 Ricordate i prodigi che egli ha compiuti, i suoi miracoli e i giudizi della sua bocca.
Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke,
13 Stirpe di Israele suo servo, figli di Giacobbe, suoi eletti,
Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.
14 egli, il Signore, è il nostro Dio; in tutta la terra fanno legge i suoi giudizi.
Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya.
15 Si ricorda sempre dell'alleanza, della parola data a mille generazioni,
Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
16 dell'alleanza conclusa con Abramo, del giuramento fatto a Isacco,
alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku.
17 confermato a Giacobbe come statuto, a Israele come alleanza perenne:
Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari.
18 «A te darò il paese di Canaan, come tua parte di eredità».
“Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.”
19 Eppure costituivano un piccolo numero; erano pochi e per di più stranieri nel paese.
Sa’ad da suke kima, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,
20 Passarono dall'una all'altra nazione, da un regno a un altro popolo.
suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga wannan mulki zuwa wancan.
21 Egli non tollerò che alcuno li opprimesse; per essi egli castigò i re:
Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna.
22 «Non toccate i miei consacrati, non maltrattate i miei profeti».
“Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.”
23 Cantate al Signore, abitanti di tutta la terra; annunziate ogni giorno la sua salvezza.
Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana.
24 Proclamate fra i popoli la sua gloria, fra tutte le nazioni i suoi prodigi.
Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.
25 Difatti grande è il Signore, degnissimo di lode e tremendo sopra tutti gli dei.
Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
26 Tutti gli dei venerati dai popoli sono un nulla; il Signore, invece, ha formato il cielo.
Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai.
27 Splendore e maestà stanno davanti a lui; potenza e bellezza nel suo santuario.
Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.
28 Date per il Signore, stirpi dei popoli, date per il Signore gloria e onore.
Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,
29 Date per il Signore gloria al suo nome; con offerte presentatevi a lui. Prostratevi al Signore in sacri ornamenti.
ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.
30 Tremate davanti a lui, abitanti di tutta la terra; egli fissò il mondo sì che non crolli.
Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba.
31 Gioiscano i cieli ed esulti la terra; si dica fra i popoli: «Il Signore regna».
Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”
32 Frema il mare con quanto contiene; tripudi la campagna con quanto è in essa.
Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri; bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!
33 Gridino di giubilo gli alberi della foresta di fronte al Signore, perché viene per giudicare la terra.
Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya.
34 Lodate il Signore, perché è buono, perché la sua grazia dura sempre.
Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce.
35 Dite: «Salvaci, Dio della nostra salvezza; raccoglici, liberaci dalle genti sì che possiamo celebrare il tuo santo nome, gloriarci della tua lode.
Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”
36 Sia benedetto il Signore, Dio di Israele, di secolo in secolo». E tutto il popolo disse: «Amen, alleluia».
Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”
37 Quindi Davide lasciò Asaf e i suoi fratelli davanti all'arca dell'alleanza del Signore, perché officiassero davanti all'arca secondo il rituale quotidiano;
Dawuda ya bar Asaf da’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.
38 lasciò Obed-Edom figlio di Idutun, e Cosà, insieme con sessantotto fratelli, come portieri.
Ya kuma bar Obed-Edom da’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi.
39 Egli incaricò della Dimora del Signore che era sull'altura di Gàbaon il sacerdote Zadòk e i suoi fratelli,
Dawuda ya bar Zadok firist da’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon
40 perché offrissero olocausti al Signore sull'altare degli olocausti per sempre, al mattino e alla sera, e compissero quanto è scritto nella legge che il Signore aveva imposta a Israele.
don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila.
41 Con loro erano Eman, Idutun e tutti gli altri scelti e designati per nome perché lodassero il Signore, perché la sua grazia dura sempre.
Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
42 Con loro avevano trombe e cembali per suonare e altri strumenti per il canto divino. I figli di Idutun erano incaricati della porta.
Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki.’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.
43 Infine tutto il popolo andò a casa e Davide tornò per salutare la sua famiglia.
Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka.