< אֶל־הָרוֹמִיִּים 3 >

ועתה מה הוא יתרון היהודי ומה היא תועלת המילה׃ 1
To ina fifikon da bayahude yake dashi? Kuma ina ribar kaciya?
הרבה מכל פנים בראשון כי הפקדו בידם דברי אלהים׃ 2
Akwai muhimmancinsu ta kowacce hanya. Tun farko dai, yahudawa ne aka dankawa wahayi daga Allah.
כי מה הוא אם מקצתם לא האמינו היבטל חסרון אמונתם את אמונת אלהים׃ 3
Idan wasu yahudawa basu bada gaskiya ba fa? Rashin bangaskiyarsu zai hana amincin Allah aiki?
חלילה אבל יהי האל הוא הנאמן וכל האדם כזב ככתוב למען תצדק בדברך תזכה בשפטך׃ 4
Bazai taba zama haka ba. Maimakon haka, bari Allah ya zama mai gaskiya, ko da kowanne mutum makaryaci ne. Kamar yadda aka rubuta, “Domin a nuna kai mai adalci cikin maganganunka, kuma kayi nasara a lokacin da aka kawo ka gaban shari'a.”
ואם עולתנו תרומם את צדקת האלהים מה נאמר הכי יש עול באלהים המשלח חרון אפו לפי דרך בני אדם אנכי מדבר׃ 5
Amma idan rashin adalcinmu ya nuna adalcin Allah, to me zamu ce? Allah ba marar adalci ba ne, wanda ke aiwatar da fushinsa, ko kuwa? Ina magana bisa ga tunanin mutuntaka.
חלילה שאם כן איך ישפט האלהים את העולם׃ 6
Bazai taba zama haka ba. Domin idan haka ne ta yaya Allah zai shar'anta duniya?
כי אם על ידי כזבי תרבה ותפרץ אמת אלהים לתהלתו למה זה אני אשפט עוד כחוטא׃ 7
Amma idan gaskiyar Allah ta wurin karyata ta habaka yabonsa, To me yasa ake shar'anta ni a matsayin mai zunubi?
ולא נעשה כדבר מחרפינו ומקצת מוציאי דבה עלינו לאמר הנה אמרים נעשה הרע למען יצא הטוב אשר דינם יבא עליהם בצדק׃ 8
To me zai hana ace kamar yadda ake fadin zancen karya a kanmu, wasu kuma sun dauka cewa mun fadi hakan, “Bari muyi mugunta, domin nagarta tazo?” Hukuncin su halal ne.
ועתה מה הוא היש לנו מעלה יתרה לא במאומה כבר הוכחנו כי גם היהודים גם היונים כלם הם תחת החטא׃ 9
To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi.
ככתוב אין צדיק אין גם אחד׃ 10
Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya.
אין משכיל אין דרש את אלהים׃ 11
Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah.
הכל סר יחדו נאלחו אין עשה טוב אין גם אחד׃ 12
Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya.
קבר פתוח גרונם לשונם יחליקון חמת עכשוב תחת שפתימו׃ 13
Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu.
אשר אלה פיהם מלא ומררות׃ 14
Bakunansu cike suke da la'ana da daci.
רגליהם ימהרו לשפך דם׃ 15
Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini.
שד ושבר במסלותם׃ 16
Tafarkinsu wahala ce da lalacewa.
ודרך שלום לא ידעו׃ 17
Wadannan mutane basu san hanyar salama ba.
אין פחד אלהים לנגד עיניהם׃ 18
Babu tsoron Allah a idanunsu.”
ואנחנו ידענו כי כל מה שאמרה התורה מדברת אל אלה אשר תחת התורה למען יסכר כל פה והיה כל העולם מחיב לפני אלהים׃ 19
To mun san dai duk abin da shari'a tace, shari'a na magana ne da wadanda ke karkashinta, domin a rufe kowanne baki, domin dukan duniya ta bada amsa a gaban Allah.
יען אשר ממעשי התורה לא יצדק לפניו כל בשר כי על ידי התורה דעת החטא׃ 20
Domin a gabansa babu wanda zai barata ta wurin ayukan shari'a. Domin ta wurin shari'a ne sanin zunubi yazo.
ועתה בבלי תורה צדקת אלהים לאור יצאה אשר העידו עליה התורה והנביאים׃ 21
Amma yanzu ba tare da shari'a ba an bayyana sanin adalcin Allah, wanda shari'a da annabawa suke shaidawa.
והיא צדקת אלהים באמונת ישוע המשיח אל כל ועל כל אשר האמינו בו כי אין הבדל׃ 22
Wato, adalcin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ga dukkan wadanda ke bada gaskiya. Domin babu bambanci:
כי כלם חטאו וחסרי כבוד אלהים המה׃ 23
Domin duk sun yi zunubi sun kuma kasa kaiwa ga darajar Allah,
ונצדקו חנם בחסדו על ידי הפדות אשר היתה במשיח ישוע׃ 24
Da alherinsa an baratar da mu ta wurin fansar dake cikin Yesu Almasihu.
אשר שמו האלהים לפנינו לכפרת על ידי האמונה בדמו להראות את צדקתו אחרי אשר העביר את החטאים שנעשו לפנים בעת חמלת אלהים׃ 25
Amma Allah ya bayar da Yesu Almasihu wanda yake hadayar fansa ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya mika Almasihu a matsayin tabbacin hukuncinsa, sabo da kuma ketarewar zunubanmu na baya
להראות את צדקתו בעת הזאת להיותו צדיק ומצדיק את בן אמונת ישוע׃ 26
cikin hakurinsa. Duk wannan ya faru ne domin a bayyana adalcinsa cikin wannan zamani, domin ya tabbatar da kansa mai hukunci, kuma ya nuna shine mai baratar da kowa saboda bangaskiya cikin Yesu.
ועתה איה ההתהללות הלא נשבתה ועל ידי תורת מה העל ידי תורת המעשים לא כי על ידי תורת האמונה׃ 27
To ina fahariya? An fitar da ita. A kan wane dalilin? Don ayyuka? A'a, amma ta dalilin bangaskiya.
לכן נחשב כי באמונה יצדק האדם בבלי מעשי תורה׃ 28
Domin wannan muka kammala cewar ana baratar da mutum ta wurin bangaskiya ba tare da ayyukan shari'a ba.
או האלהים רק אלהי היהודים הלא גם אלהי הגוים אכן גם אלהי הגוים הוא׃ 29
Ko kuwa Allah Allahn yahudawa ne kadai? Shi ba Allahn al'ummai bane? I, na al'ummai ne kuma.
כי אחד האלהים המצדיק את המולים מתוך האמונה ואת הערלים על ידי האמונה׃ 30
Idan dai lallai Allah daya ne, zai baratar da mai kaciya ta wurin bangaskiya, da marar kaciya kuma ta wurin bangaskiya.
ועתה המבטלים אנחנו את התורה על ידי האמונה חלילה אך מקימים אנחנו את התורה׃ 31
Mun kawar da shari'a kenan ta wurin bangaskiya? ba zai taba kasancewa haka ba. Maimako ma, muna inganta shari'a kenan.

< אֶל־הָרוֹמִיִּים 3 >