< תהילים 85 >

למנצח לבני קרח מזמור רצית יהוה ארצך שבת שבות יעקב׃ 1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub.
נשאת עון עמך כסית כל חטאתם סלה׃ 2
Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. (Sela)
אספת כל עברתך השיבות מחרון אפך׃ 3
Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka.
שובנו אלהי ישענו והפר כעסך עמנו׃ 4
Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
הלעולם תאנף בנו תמשך אפך לדר ודר׃ 5
Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?
הלא אתה תשוב תחינו ועמך ישמחו בך׃ 6
Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?
הראנו יהוה חסדך וישעך תתן לנו׃ 7
Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka.
אשמעה מה ידבר האל יהוה כי ידבר שלום אל עמו ואל חסידיו ואל ישובו לכסלה׃ 8
Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta.
אך קרוב ליראיו ישעו לשכן כבוד בארצנו׃ 9
Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
חסד ואמת נפגשו צדק ושלום נשקו׃ 10
Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba.
אמת מארץ תצמח וצדק משמים נשקף׃ 11
Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa, adalci kuma yă duba daga sama.
גם יהוה יתן הטוב וארצנו תתן יבולה׃ 12
Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.
צדק לפניו יהלך וישם לדרך פעמיו׃ 13
Adalci na tafiya a gabansa yana shirya hanya domin ƙafafunsa.

< תהילים 85 >