< תהילים 76 >

למנצח בנגינת מזמור לאסף שיר נודע ביהודה אלהים בישראל גדול שמו׃ 1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce. A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.
ויהי בשלם סכו ומעונתו בציון׃ 2
Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.
שמה שבר רשפי קשת מגן וחרב ומלחמה סלה׃ 3
A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. (Sela)
נאור אתה אדיר מהררי טרף׃ 4
Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.
אשתוללו אבירי לב נמו שנתם ולא מצאו כל אנשי חיל ידיהם׃ 5
Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.
מגערתך אלהי יעקב נרדם ורכב וסוס׃ 6
A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.
אתה נורא אתה ומי יעמד לפניך מאז אפך׃ 7
Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?
משמים השמעת דין ארץ יראה ושקטה׃ 8
Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,
בקום למשפט אלהים להושיע כל ענוי ארץ סלה׃ 9
sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. (Sela)
כי חמת אדם תודך שארית חמת תחגר׃ 10
Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.
נדרו ושלמו ליהוה אלהיכם כל סביביו יובילו שי למורא׃ 11
Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.
יבצר רוח נגידים נורא למלכי ארץ׃ 12
Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.

< תהילים 76 >