< תהילים 68 >
למנצח לדוד מזמור שיר יקום אלהים יפוצו אויביו וינוסו משנאיו מפניו׃ | 1 |
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa; bari maƙiyansa su gudu a gabansa.
כהנדף עשן תנדף כהמס דונג מפני אש יאבדו רשעים מפני אלהים׃ | 2 |
Kamar yadda iska take hura hayaƙi, bari yă hura su haka; kamar yadda kaki kan narke a gaban wuta, bari mugaye su hallaka a gaban Allah.
וצדיקים ישמחו יעלצו לפני אלהים וישישו בשמחה׃ | 3 |
Amma bari adalai su yi murna su kuma yi farin ciki a gaban Allah; bari su yi murna da farin ciki.
שירו לאלהים זמרו שמו סלו לרכב בערבות ביה שמו ועלזו לפניו׃ | 4 |
Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai; sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
אבי יתומים ודין אלמנות אלהים במעון קדשו׃ | 5 |
Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
אלהים מושיב יחידים ביתה מוציא אסירים בכושרות אך סוררים שכנו צחיחה׃ | 6 |
Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance’yan kurkuku da waƙoƙi; amma’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.
אלהים בצאתך לפני עמך בצעדך בישימון סלה׃ | 7 |
Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah, sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi, (Sela)
ארץ רעשה אף שמים נטפו מפני אלהים זה סיני מפני אלהים אלהי ישראל׃ | 8 |
duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama, a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra’ila.
גשם נדבות תניף אלהים נחלתך ונלאה אתה כוננתה׃ | 9 |
Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah; ka rayar da gādonka da ya gāji.
חיתך ישבו בה תכין בטובתך לעני אלהים׃ | 10 |
Mutanenka suka zauna a cikinsa, kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta.
אדני יתן אמר המבשרות צבא רב׃ | 11 |
Ubangiji ya yi umarni, mutane masu yawa ne suka yi shelarsa,
מלכי צבאות ידדון ידדון ונות בית תחלק שלל׃ | 12 |
“Sarakuna da mayaƙa suka gudu a gaggauce; cikin sansani mutane sun raba ganima.
אם תשכבון בין שפתים כנפי יונה נחפה בכסף ואברותיה בירקרק חרוץ׃ | 13 |
Har yayinda kuke barci a cikin garken tumaki, an dalaye fikafikan kurciya da azurfa, fikafikanta da zinariya mai ƙyalli.”
בפרש שדי מלכים בה תשלג בצלמון׃ | 14 |
Sa’ad da Maɗaukaki ya watsar da sarakuna a cikin ƙasa, sai ya zama kamar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmon.
הר אלהים הר בשן הר גבננים הר בשן׃ | 15 |
Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne.
למה תרצדון הרים גבננים ההר חמד אלהים לשבתו אף יהוה ישכן לנצח׃ | 16 |
Don me kuke duba da kishi, ya duwatsu masu wuyan hawa, a kan dutsen da Allah ya zaɓa yă yi mulki, inda Ubangiji kansa zai zauna har abada?
רכב אלהים רבתים אלפי שנאן אדני בם סיני בקדש׃ | 17 |
Karusan Allah ninkin dubbai goma ne da kuma dubu dubbai; Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa.
עלית למרום שבית שבי לקחת מתנות באדם ואף סוררים לשכן יה אלהים׃ | 18 |
Sa’ad da ka hau bisa, ka bi da kamammu cikin tawagarka; ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga’yan tawaye, don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can.
ברוך אדני יום יום יעמס לנו האל ישועתנו סלה׃ | 19 |
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. (Sela)
האל לנו אל למושעות וליהוה אדני למות תוצאות׃ | 20 |
Allahnmu shi ne Allah wanda yake ceto; daga Ubangiji Mai Iko Duka kuɓuta yake zuwa daga mutuwa.
אך אלהים ימחץ ראש איביו קדקד שער מתהלך באשמיו׃ | 21 |
Tabbatacce Allah zai murƙushe kawunan abokan gābansa, rawanin gashi na waɗanda suke ci gaba cikin zunubansa.
אמר אדני מבשן אשיב אשיב ממצלות ים׃ | 22 |
Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku,
למען תמחץ רגלך בדם לשון כלביך מאיבים מנהו׃ | 23 |
don ku wanke ƙafafunku a cikin jinin maƙiyanku, yayinda harsunan karnukanku su sami rabonsu.”
ראו הליכותיך אלהים הליכות אלי מלכי בקדש׃ | 24 |
Jerin gwanonka ya zo a bayyane, ya Allah, jerin gwanon Allahna da Sarkina zuwa cikin wuri mai tsarki.
קדמו שרים אחר נגנים בתוך עלמות תופפות׃ | 25 |
A gaba akwai mawaƙa, a bayansu akwai makaɗa; tare da su akwai’yan mata suna bugan ganguna.
במקהלות ברכו אלהים יהוה ממקור ישראל׃ | 26 |
Ku yabi Allah cikin taro mai girma; yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila.
שם בנימן צעיר רדם שרי יהודה רגמתם שרי זבלון שרי נפתלי׃ | 27 |
Ga ƙaramar kabilar Benyamin, suna jagorance su, ga babbar ƙungiya shugabannin Yahuda, ga kuma shugabannin Zebulun da na Naftali.
צוה אלהיך עזך עוזה אלהים זו פעלת לנו׃ | 28 |
Ka bayyana ikonka, ya Allah; ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā.
מהיכלך על ירושלם לך יובילו מלכים שי׃ | 29 |
Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai.
גער חית קנה עדת אבירים בעגלי עמים מתרפס ברצי כסף בזר עמים קרבות יחפצו׃ | 30 |
Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi.
יאתיו חשמנים מני מצרים כוש תריץ ידיו לאלהים׃ | 31 |
Jakadu za su zo daga Masar; Kush za tă miƙa kanta ga Allah.
ממלכות הארץ שירו לאלהים זמרו אדני סלה׃ | 32 |
Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, (Sela)
לרכב בשמי שמי קדם הן יתן בקולו קול עז׃ | 33 |
gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya.
תנו עז לאלהים על ישראל גאותו ועזו בשחקים׃ | 34 |
Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari.
נורא אלהים ממקדשיך אל ישראל הוא נתן עז ותעצמות לעם ברוך אלהים׃ | 35 |
Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah!