< תהילים 57 >

למנצח אל תשחת לדוד מכתם בברחו מפני שאול במערה חנני אלהים חנני כי בך חסיה נפשי ובצל כנפיך אחסה עד יעבר הוות׃ 1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce.
אקרא לאלהים עליון לאל גמר עלי׃ 2
Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka, ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni.
ישלח משמים ויושיעני חרף שאפי סלה ישלח אלהים חסדו ואמתו׃ 3
Ya aika daga sama ya kuwa cece ni, yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; (Sela) Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.
נפשי בתוך לבאם אשכבה להטים בני אדם שניהם חנית וחצים ולשונם חרב חדה׃ 4
Ina tsakiyar zakoki; ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane, mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi, waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi.
רומה על השמים אלהים על כל הארץ כבודך׃ 5
Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
רשת הכינו לפעמי כפף נפשי כרו לפני שיחה נפלו בתוכה סלה׃ 6
Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna, damuwa ta sha ƙarfina. Sun haƙa rami a hanyata, amma su kansu suka fāɗa a cikinta. (Sela)
נכון לבי אלהים נכון לבי אשירה ואזמרה׃ 7
Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.
עורה כבודי עורה הנבל וכנור אעירה שחר׃ 8
Ka farka, raina! Ku farka, garaya da molo! Zan sa safe yă farka.
אודך בעמים אדני אזמרך בל אמים׃ 9
Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai a cikin mutane.
כי גדל עד שמים חסדך ועד שחקים אמתך׃ 10
Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai; amincinka na kaiwa sarari.
רומה על שמים אלהים על כל הארץ כבודך׃ 11
Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.

< תהילים 57 >