< תהילים 35 >
לדוד ריבה יהוה את יריבי לחם את לחמי׃ | 1 |
Ta Dawuda. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.
החזק מגן וצנה וקומה בעזרתי׃ | 2 |
Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni.
והרק חנית וסגר לקראת רדפי אמר לנפשי ישעתך אני׃ | 3 |
Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.”
יבשו ויכלמו מבקשי נפשי יסגו אחור ויחפרו חשבי רעתי׃ | 4 |
Bari waɗanda suke neman raina su sha kunya a kuma kunyatar da su; bari waɗanda suke shirya lalacewata su juya da baya su ruɗe.
יהיו כמץ לפני רוח ומלאך יהוה דוחה׃ | 5 |
Bari su zama kamar yayi a gaban iska, mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu;
יהי דרכם חשך וחלקלקות ומלאך יהוה רדפם׃ | 6 |
bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi, mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu.
כי חנם טמנו לי שחת רשתם חנם חפרו לנפשי׃ | 7 |
Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalili kuma babu dalili suka haƙa mini rami,
תבואהו שואה לא ידע ורשתו אשר טמן תלכדו בשואה יפל בה׃ | 8 |
bari lalaci yă kama su ba zato, bari tarkon da suka ɓoye yă kama su, bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu.
ונפשי תגיל ביהוה תשיש בישועתו׃ | 9 |
Sa’an nan raina zai cika da farin ciki a cikin Ubangiji in yi kuma murna a cikin cetonsa.
כל עצמותי תאמרנה יהוה מי כמוך מציל עני מחזק ממנו ועני ואביון מגזלו׃ | 10 |
Dukan raina zai ce, “Wane ne kamar ka, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu, matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.”
יקומון עדי חמס אשר לא ידעתי ישאלוני׃ | 11 |
Shaidu marasa imani sun fito; suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba.
ישלמוני רעה תחת טובה שכול לנפשי׃ | 12 |
Suna sāka alherin da na yi musu da mugunta suka bar raina da nadama.
ואני בחלותם לבושי שק עניתי בצום נפשי ותפלתי על חיקי תשוב׃ | 13 |
Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,
כרע כאח לי התהלכתי כאבל אם קדר שחותי׃ | 14 |
nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.
ובצלעי שמחו ונאספו נאספו עלי נכים ולא ידעתי קרעו ולא דמו׃ | 15 |
Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna; masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba. Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa.
בחנפי לעגי מעוג חרק עלי שנימו׃ | 16 |
Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a; Suna hararata da ƙiyayya.
אדני כמה תראה השיבה נפשי משאיהם מכפירים יחידתי׃ | 17 |
Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai? Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu, raina mai daraja daga waɗannan zakoki.
אודך בקהל רב בעם עצום אהללך׃ | 18 |
Zan yi godiya cikin taro mai girma; cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.
אל ישמחו לי איבי שקר שנאי חנם יקרצו עין׃ | 19 |
Kada ka bar maƙaryatan nan, su yi farin ciki a kaina; kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, su ji daɗin baƙin cikina.
כי לא שלום ידברו ועל רגעי ארץ דברי מרמות יחשבון׃ | 20 |
Ba sa maganar salama sukan ƙirƙiro zage-zagen ƙarya a kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar.
וירחיבו עלי פיהם אמרו האח האח ראתה עינינו׃ | 21 |
Sukan wage mini bakinsu suna cewa, “Allah yă ƙara! Da idanunmu mun gani.”
ראיתה יהוה אל תחרש אדני אל תרחק ממני׃ | 22 |
Ya Ubangiji, ka ga wannan; kada ka yi shiru. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji.
העירה והקיצה למשפטי אלהי ואדני לריבי׃ | 23 |
Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni! Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana.
שפטני כצדקך יהוה אלהי ואל ישמחו לי׃ | 24 |
Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka, Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina.
אל יאמרו בלבם האח נפשנו אל יאמרו בלענוהו׃ | 25 |
Kada ka bari su ce wa kansu, “Allah yă ƙara, dā ma abin da mun so ke nan!” Ko su ce, “Mun haɗiye shi.”
יבשו ויחפרו יחדו שמחי רעתי ילבשו בשת וכלמה המגדילים עלי׃ | 26 |
Bari dukan waɗanda suke farin ciki a kaina a wahalata su sha kunya su kuma ruɗe; bari dukan waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni su sha kunya da wulaƙanci.
ירנו וישמחו חפצי צדקי ויאמרו תמיד יגדל יהוה החפץ שלום עבדו׃ | 27 |
Bari waɗanda suke murna saboda nasarata su yi sowa don farin ciki da murna; bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji, wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.”
ולשוני תהגה צדקך כל היום תהלתך׃ | 28 |
Harshena zai yi zancen adalcinka da kuma yabonka dukan yini.