< לוּקָס 8 >

ויהי אחרי כן ויעבר מעיר אל עיר ומכפר אל כפר קורא ומבשר את מלכות האלהים ושנים העשר אתו׃ 1
Bayan haka, Yesu da almajiransa goma sha biyu, su ka zagaya cikin birane da kauyuka dabam dabam, suna wa'azi da shelar labari mai dadi game da mulkin Allah,
ונשים אשר נרפאו מרוחות רעות ומחליים מרים הנקראה מגדלית אשר גרשו ממנה שבעה שדים׃ 2
mata da yawa wadanda Yesu ya warkar daga aljanu da cututtuka iri iri suna tafiya tare da su. A cikinsu akwai Maryamu wadda a ke ce da ita Magadaliya, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta,
ויוחנה אשת כוזא סוכן הורדוס ושושנה ואחרות רבות אשר שרתהו מנכסיהן׃ 3
da Yuwana matar Kuza wakilin Hirudus, da Suzanatu da kuma wasu mata da yawa. Daga abin hannunsu suka tanada masu.
ויהי בהתאסף המון עם רב אשר יצאו אליו מעיר ועיר וידבר במשל׃ 4
Wata rana aka tara taron mutane da yawa, saboda mutane su na zuwa daga birane da yawa domin su ga Yesu. Ya yi magana dasu cikin misali.
הזורע יצא לזרע את זרעו ובזרעו נפל מן הזרע על יד הדרך וירמס ועוף השמים אכלו׃ 5
“Wani mai shuka ya tafi domin ya shuka iri. Sa'adda ya ke yafa iri, wadansu iri suka fada a kan hanya. Sai mutane suka tattake su, tsuntsaye kuma suka tsince wadansu suka cinye.
ויש אשר נפל על הסלע ויצמח וייבש כי לא היתה לו לחה׃ 6
Wadansu kuma suka fada a kan duwatsu inda babu kasa da yawa. Da suka tsaro suka fara girma, sai nan da nan suka bushe saboda babu laima a wurin.
ויש אשר נפל בתוך הקצים ויצמחו הקצים עמו וימעכהו׃ 7
Wadansu irin kuma suka fada inda yake da kayayuwa. Tsiretsiren kayayuwan suka fito tare da irin da aka shuka, suka shake su yadda basu iya yin girma ba.
ויש אשר נפל על האדמה הטובה ויצמח ויעש פרי מאה שערים כזאת דבר ויזעק מי אשר אזנים לו לשמע ישמע׃ 8
Amma wadansu irin suka fada a kan kasa mai kyau, suka yi girma sosai suka ba da anfani da yawa, har rubi dari.” Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, sai ya yi kira gare su, “Duk mai kunnen ji, bari ya ji.”
וישאלהו תלמידיו לאמר מה המשל הזה׃ 9
Sai almajiran Yesu suka tambaye shi ya gaya ma su ma'anar labarin.
ויאמר לכם נתן לדעת את סודות מלכות האלהים ולאחרים במשלים למען בראתם לא יראו ובשמעם לא יבינו׃ 10
ya ce da su, “Ku aka ba dama ku gane boyayyun abubuwa, na mulkin Allah. Amma ga sauran mutane ina yi masu magana cikin misalai, 'Domin ko da sun gani ba za su gane ba, kuma ko da sun ji ba za su fahimta ba.”
וזה הוא המשל הזרע דבר אלהים הוא׃ 11
To ga ma'anar misalin. Irin shi ne maganar Allah.
ואשר על יד הדרך הם השמעים ואחר כן בא השטן ונשא את הדבר מלבם פן יאמינו ונושעו׃ 12
Irin da ya fada a kan hanya sune mutanen da suka ji maganar Allah amma daga baya sai shedan ya zo ya dauke maganar daga cikin hankulansu, domin kada su bada gaskiya su tsira.
ואשר על הסלע הם המקבלים בשמחה את הדבר בשמעם ושרש אין להם רק לשעה מאמינים ובעת הנסיון יסגו אחור׃ 13
Sa'annan, wadanda suka fada kan duwatsu sune mutanen da, da zarar sun ji maganar, sukan karbe ta da murna, amma ba su da sauyu; su kan bada gaskiya na dan lokaci kadan kawai, da zaran gwaji ya same su sai su ridda.
ואשר נפל בין הקצים הם השמעים והוליכם להם וימכו בדאגות ובעשר ובתאות החיים ופרי לא ישוו למו׃ 14
Irin da suka fada cikin kayayuwa, sune mutanen da suka ji maganar, amma da suka ci gaba da rayuwa, sai suka bari matsalolin rayuwa kamar dukiya da jin dadin rayuwa suka fi karfinsu, sai ya zama ba su iya bada 'ya'yan da suka yi girma ba.
ואשר באדמה הטובה הם השמרים בלב טוב וטהור את הדבר אשר שמעו ועשים פרי בתוחלת׃ 15
Amma irin da suka fada a kan kasa mai kyau, wadannan sune mutanen da suka ji maganar, suka karbe ta da gaskiya da zuciya daya, sun rike ta kam-kam, suna jimrewa wurin ba da 'ya'ya.
ואין איש מדליק נר אשר יכסה אותו בכלי או ישימהו תחת המטה כי אם על המנורה יעלהו למען יראו כל באי הבית את האור׃ 16
Ba mai kunna fitila, ya rufe ta da kasko, ko su sa ta a karkashin gado. Amma sai a sa ta a wurin zaman ta domin duk wanda ya shigo ya iya ganin hasken ta.
כי אין דבר נעלם אשר לא יגלה ואין גנוז אשר לא יודע ובא לאור׃ 17
Babu abin da yake a boye wanda ba za a tone shi ba, ko wani asiri da ba za ya fito fili a san shi ba.
לכן ראו איך תשמעון כי כל אשר יש לו נתון ינתן לו וכל אשר אין לו גם את אשר הוא חשב להיות לו יקח ממנו׃ 18
Ku yi hankali da yadda kuke ji, domin duk mai abu, shi za a kara wa, kuma duk mara abu, dan kadan da yake tunani yana da shi ma, za a dauke.”
ויבאו אליו אמו ואחיו ולא יכלו לגשת אליו מפני העם׃ 19
Sai mahafiyar Yesu da 'yan'uwansa, su ka zo wurinsa, amma ba su iya zuwa ko kusa da shi ba saboda taron jama'a.
ויגד לו לאמר אמך ואחיך עמדים בחוץ והם חפצים לראותך׃ 20
Sai wani ya gaya masa, “Ga mahaifiyarka da 'yan'uwanka, su na tsayuwa a waje, su na son ganin ka.”
ויען ויאמר אליהם אמי ואחי הם השמעים ועשים את דבר האלהים׃ 21
Amma Yesu ya amsa ya ce ma su, “Mahaifiyata da 'yan'uwana sune wadanda suke jin maganar Allah, suke yin biyayya da ita.”
ויהי היום וירד אל אניה הוא ותלמידיו ויאמר אליהם נעברה אל עבר הים וישוטו הימה׃ 22
Wata rana kuma Yesu ya shiga cikin jirgin ruwa, shi da almajiransa. Ya ce masu, “Ina so mu je dayan ketaren tafkin.” Sai su ka fara tafiya domin su ketare tafkin.
ויהי בלכתם באניה וישכב ויישן ורוח סערה ירדה על הים וישטפו עליהם המים ויהיו בסכנה׃ 23
Amma sa'adda su ke tafiya sai Yesu ya yi barci, sai wata iska mai karfi ta taso cikin tafkin, nan da nan sai jirgin ya fara cika da ruwa, kuma su na cikin hatsari.
ויגשו ויעירו אותו לאמר מורה מורה אבדנו ויעור ויגער ברוח ובמשברי ים וישתקו ותהי דממה׃ 24
Sai almajiran Yesu su ka zo su ka tashe shi daga barci. Suka ce da shi, “Ya Shugaba! Ya Shugaba! Za mu mutu!” Sai ya tashi ya umarci iskar, sai iskar mai hauka da tumbatsar ruwan sun tsaya tsit.
ויאמר אליהם איה אמונתכם וייראו ויתמהו ויאמרו איש אל רעהו מי אפוא הוא המצוה גם את הרוחות ואת המים וישמעו לו׃ 25
Daga nan sai ya ce da su, “Ina bangaskiyar ku?” Almajiran suka tsorata suka yi mamakin abin da ya faru nan take. Suka ce wa junansu, “Wanene wannan wanda har zai ba iska da ruwa umarni kuma su yi masa biyayya?”
ויעברו ויבאו אל ארץ הגדריים אשר ממול הגליל׃ 26
Suka zo yankin Garasinawa, wanda ke kusa da Gallili.
ויצא אל היבשה ויפגשהו איש מן העיר אשר שדים בו מימים רבים ובגד לא לבש ובבית לא ישב כי אם בקברים׃ 27
Sa'adda Yesu ya sauka kasa, sai wani mutum daga wannan yankin ya tarbe shi. Wannan mutum kuwa yana da aljanu. Mutumin ya dade ba ya sa tufafi, kuma ba ya zama a gida. Maimakon haka, sai a cikin kabarbura ya ke zama.
וירא את ישוע ויפל לפניו ויקרא בקול גדול מה לי ולך ישוע בן אל עליון מבקש אני ממך אשר לא תענני׃ 28
Sa'adda ya ga Yesu, mutumin ya yi ihu da karfi, ya rusuna a gabansa da babban murya ya ce, “Me zan yi da kai, Yesu, Dan Allah Madaukaki? Ina rokonka, kada ka ba ni azaba!”
כי צוה את הרוח הטמא לצאת מן האיש כי ימים רבים חטף אתו ונאסר בזיקים ונשמר בכבלים והיה בנתקו את המוסרות ונדחף ביד השד אל המדברות׃ 29
Domin Yesu ya umarci aljanun su fita daga cikinsa, domin sau da dama aljanun sukan kama shi. Ko an daure mutumin da sarkoki an kuma tsare shi, yakan tsuttsunke su, kazaman ruhohin sukan kora shi cikin jeji.
וישאל אתו ישוע לאמר מה שמך ויאמר לגיון שמי כי שדים רבים נכנסו בו׃ 30
Sa'annan Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Sai ya ba da amsa, “Suna na dubbai.” Ya ce haka ne domin aljanu da yawa sun shiga wannan mutum.
ויתחנן לו לבלתי צות אתם לרדת אל התהום׃ (Abyssos g12) 31
Aljanun suka yi ta rokon Yesu kada ya ummarce su su shiga cikin rami mai zurfi. (Abyssos g12)
ויהי שם עדר חזירים רבים על המרעה בהר ויתחננו לו כי יניח להם לבוא אל תוכם וינח להם׃ 32
Akwai babban garken aladu su na kiwo a kan tsauni kusa da wurin. Aljanun suka roki Yesu da ya barsu su shiga cikin aladun, shi kuwa ya yarda masu.
ויצאו השדים מן האדם ההוא ויבאו בחזירים וישתער העדר מן המורד אל הים ויטבע׃ 33
Aljanun suka bar mutumin suka shiga cikin aladun, sai garken aladun suka gangara kwari suka fada cikin tafkin, suka nutse.
וינוסו הרעים כראותם את אשר נעשה ויגידו הדבר בעיר ובכפרים׃ 34
Lokacin da mutanen da su ke kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu! Suka ba da rahoton abin da ya faru ga mutanen cikin gari da na wannan kewayen.
ויצאו לראת את אשר נעשה ויבאו אל ישוע וימצאו שם את האדם אשר יצאו ממנו השדים ישב לרגלי ישוע מלבש וטוב שכל וייראו׃ 35
Don haka, mutanen da suka ji haka suka tafi domin su ga abin da ya faru, suka zo wurin da Yesu yake, suka ga mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa. Suka ga ya na sanye da tufafi, kuma ya na cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.
ויספרו להם הראים איך נרפא אחוז השדים׃ 36
Mutanen da suka ga abin da ya faru, suka gaya wa wadansu yadda aka warkar da mutumin da aljanu suke iko da shi.
ויבקשו ממנו כל המון חבל הגדריים ללכת מאתם כי אימה גדולה נפלה עליהם וירד אל האניה וישב׃ 37
Sai dukan mutane wadanda suke cikin yankin Garasinawa da wadanda suke kewaye, suka roki Yesu da ya fita daga cikin yankin kasarsu domin sun ji tsoro kwarai da gaske. Daga nan Yesu da almajiransa suka shiga cikin jirgin ruwa suka koma.
ויבקש ממנו האיש אשר יצאו ממנו השדים לשבת אתו וישלח אתו ישוע באמרו׃ 38
Mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa, ya roki Yesu cewa, “Ka barni in tafi tare da kai!” Amma Yesu ya sallame shi cewa,
שוב לביתך וספר הגדלות אשר עשה לך האלהים וילך לו וישמע בכל העיר את הגדלות אשר עשה לו ישוע׃ 39
“Ka koma gida ka gaya wa mutanen ka abubuwa masu girma wadanda Allah ya yi maka.” Daga nan sai mutumin ya tafi yana ta gayawa dukan mutanen birnin game da abubuwan da Yesu ya yi masa.
ויהי בשוב ישוע ויקבל אתו העם כי כלם היו מחכים לו׃ 40
Sa'adda Yesu ya dawo, mutanen suka marabce shi, gama, dukansu suna jiransa.
והנה בא איש ושמו יאיר והוא ראש בית הכנסת ויפל לרגלי ישוע ויתחנן לו לבוא אתו אל ביתו׃ 41
Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, daya daga cikin shugabannin majami'a, ya zo kusa da Yesu ya rusuna da kansa a kasa. Ya roke shi domin ya zo gidansa,
כי בת יחידה כשתים עשרה שנה היתה לו והיא נוטה למות ויהי בלכתו שמה וידחקהו המון העם׃ 42
saboda diyarsa mai kimanin shekara goma sha biyu ta na bakin mutuwa, kuma ita kadai ce diya a gare shi. Amma sa'adda yake tafiya, taron mutane da yawa suna matsa shi.
ואשה זבת דם שתים עשרה שנה אשר הוציאה כל קנינה לרפאים ואין איש יכל לרפאתה׃ 43
Akwai wata mace a nan wadda take zubar jini har shekara goma sha biyu. Ta kashe kudinta duka a wurin likitoci, domin su warkar da ita amma ba wanda ya iya warkar da ita.
היא קרבה מאחריו ותגע בציצת בגדו וזוב דמה עמד פתאם׃ 44
Sai ta biyo ta bayan Yesu ta taba habar rigarsa. Nan take sai zubar jinin ya tsaya.
ויאמר ישוע מי זה נגע בי וכלם כחשו ויאמר פטרוס והעמדים אצלו מורה המון העם דחקים ולחצים אתך ואתה תאמר מי נגע בי׃ 45
Yesu ya ce, “Wanene ya taba ni?” Wadanda suke kewaye da shi, kowa ya ce bai taba shi ba, Bitrus ya ce, “Shugaba, mutane da yawa suna ta taruwa kewaye da kai suna ta matsowa kusa da kai.”
ויאמר ישוע נגע בי אדם כי ידעתי אשר יצאה ממני גבורה׃ 46
Amma Yesu ya ce, “Na sani, wani ya taba ni, domin iko ya fita daga wurina.”
ותרא האשה כי לא נסתרה ממנו ותחרד לקראתו ותפל לפניו ותגד באזני כל העם על מה נגעה בו ואיך נרפאה פתאם׃ 47
Sa'adda matar ta gane cewa ba za ta iya boyewa ba, sai ta zo wurinsa cikin tsoro. Ta durkusa a gaban Yesu, ta fada a gaban dukan jama'a dalilin da ya sa ta taba shi kuma nan da nan ta warke.
ויאמר אליה חזקי בתי אמונתך הושיעה לך לכי לשלום׃ 48
Sai ya ce da ita, “Diya, bangaskiyarki ta warkar da ke. Tafi cikin salama.”
עודנו מדבר ואיש בא מבית ראש הכנסת ויאמר מתה בתך אל תטריח את המורה׃ 49
Yana cikin yin magana, wani daga cikin gidan shugaban majami'ar ya zo, ya ce, “Diyarka ta riga ta mutu, kada ka dami malam.”
וישמע ישוע ויען ויאמר לו אל תירא אך האמן והיא תושע׃ 50
Amma sa'adda Yesu ya ji haka, sai ya ce da shi, “Kada ka ji tsoro. Ka bada gaskiya za ta rayu.”
ויבא הביתה ולא הניח לאיש לבוא אתו בלתי אם לפטרוס וליעקב וליוחנן ולאבי הילדה ולאמה׃ 51
Sa'adda ya zo gidan, bai bar kowa ya shiga gidan tare da shi ba sai Bitrus da Yahaya da Yakubu, da mahaifiyar yarinyar da babanta.
וכלם בכים וספדים לה ויאמר אל תבכו כי לא מתה אך ישנה היא׃ 52
Dukan mutane a wurin, suna ta kuka da karfi saboda sun damu da yarinyar ta mutu. Amma Yesu ya ce da su, “Ku dena kuka! Ba mutuwa ta yi ba! Barci ta ke yi kawai!”
וישחקו עליו באשר ידעו כי מתה׃ 53
Mutanen suka yi ma sa dariyan reni, saboda sun sani yarinyar ta mutu.
והוא אחז בידה ויקרא לאמר הילדה קומי׃ 54
Amma ya kama hannun ta yayi kira cewa, “Yarinya, na ce ki tashi!”
ותשב רוחה ותקם פתאם ויצו לתת לה לאכול׃ 55
Nan da nan ruhun ta ya dawo jikin ta sai ta tashi. Ya ce masu su ba ta wani abu ta ci.
וישתוממו אביה ואמה והוא צוה אתם לבלתי הגיד לאיש את אשר נעשה׃ 56
Iyayenta suka yi mamaki, amma Yesu ya ce da iyayen kada su gaya wa kowa abin da ya faru.

< לוּקָס 8 >