< הושע 13 >

כדבר אפרים רתת נשא הוא בישראל ויאשם בבעל וימת׃ 1
Sa’ad da Efraim ya yi magana, mutane sun yi rawan jiki; an girmama shi a cikin Isra’ila. Amma sai ya zama mai laifi na yin wa Ba’al sujada, ya kuwa mutu.
ועתה יוספו לחטא ויעשו להם מסכה מכספם כתבונם עצבים מעשה חרשים כלה להם הם אמרים זבחי אדם עגלים ישקון׃ 2
Yanzu sai yin zunubi a kai a kai suke; suna yin gumaka wa kansu daga azurfansu, da wayo suna sarrafa siffofi, dukansu aikin masu aikin hannu ne. Ana magana waɗannan mutane cewa, “Suna miƙa hadayar mutum su kuma sumbaci gumakan maruƙa.”
לכן יהיו כענן בקר וכטל משכים הלך כמץ יסער מגרן וכעשן מארבה׃ 3
Saboda haka za su zama kamar hazon safiya, kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe, kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka, kamar hayaƙin da yake fita daga taga.
ואנכי יהוה אלהיך מארץ מצרים ואלהים זולתי לא תדע ומושיע אין בלתי׃ 4
“Amma ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar. Ba za ku yarda da wani Allah ba sai ni, ba wani Mai Ceto in ban da ni.
אני ידעתיך במדבר בארץ תלאבות׃ 5
Na lura da ku a hamada, cikin ƙasar mai ƙunar zafi.
כמרעיתם וישבעו שבעו וירם לבם על כן שכחוני׃ 6
Sa’ad da na ciyar da su sun ƙoshi; sa’ad da suka ƙoshi, sai suka fara taƙama; sai suka manta da ni.
ואהי להם כמו שחל כנמר על דרך אשור׃ 7
Saboda haka zan hau kansu kamar zaki, zan ɓuya a bakin hanya kamar damisa.
אפגשם כדב שכול ואקרע סגור לבם ואכלם שם כלביא חית השדה תבקעם׃ 8
Kamar beyar da aka ƙwace mata’ya’yanta, zan fāɗa musu in ɓarke su. Kamar zaki zan cinye su; kamar naman jeji zan yayyage su.
שחתך ישראל כי בי בעזרך׃ 9
“An hallaka ku, ya Isra’ila, domin kun tayar mini, kun tayar wa mai taimakonku.
אהי מלכך אפוא ויושיעך בכל עריך ושפטיך אשר אמרת תנה לי מלך ושרים׃ 10
Ina sarkinku, da zai cece ku? Ina masu mulkinku cikin dukan garuruwanku, waɗanda kuka ce, ‘Ba mu sarki da shugabanni’?
אתן לך מלך באפי ואקח בעברתי׃ 11
Saboda haka cikin fushina na ba ku sarki, kuma cikin hasalata na ɗauke shi.
צרור עון אפרים צפונה חטאתו׃ 12
An yi ajiyar laifin Efraim, aka lissafta zunubansa.
חבלי יולדה יבאו לו הוא בן לא חכם כי עת לא יעמד במשבר בנים׃ 13
Naƙuda ta zo masa kamar a mace mai haihuwa, amma shi yaro ne marar hikima; sa’ad da lokaci ya kai, ba ya zuwa inda mahaifa ta buɗe.
מיד שאול אפדם ממות אגאלם אהי דבריך מות אהי קטבך שאול נחם יסתר מעיני׃ (Sheol h7585) 14
“Zan fanshe su daga ikon kabari; zan cece su daga mutuwa. Ina annobanki, ya mutuwa? Ina hallakarka, ya kabari? “Ba zan ji tausayi ba, (Sheol h7585)
כי הוא בין אחים יפריא יבוא קדים רוח יהוה ממדבר עלה ויבוש מקורו ויחרב מעינו הוא ישסה אוצר כל כלי חמדה׃ 15
ko da ma ya ci gaba cikin’yan’uwansa. Iskar gabas daga Ubangiji za tă zo, tana hurawa daga hamada; maɓulɓularsa za tă kafe rijiyarsa kuma ta bushe. Za a kwashi kaya masu daraja na ɗakin ajiyarsa ganima.
תאשם שמרון כי מרתה באלהיה בחרב יפלו עלליהם ירטשו והריותיו יבקעו׃ 16
Dole mutanen Samariya su ɗauki laifinsu, domin sun tayar wa Allahnsu. Za a kashe su da takobi; za a fyaɗa ƙananansu da ƙasa, za a ɓarke matansu masu ciki.”

< הושע 13 >