< בראשית 5 >

זה ספר תולדת אדם ביום ברא אלהים אדם בדמות אלהים עשה אתו׃ 1
Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.
זכר ונקבה בראם ויברך אתם ויקרא את שמם אדם ביום הבראם׃ 2
Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”
ויחי אדם שלשים ומאת שנה ויולד בדמותו כצלמו ויקרא את שמו שת׃ 3
Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.
ויהיו ימי אדם אחרי הולידו את שת שמנה מאת שנה ויולד בנים ובנות׃ 4
Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויהיו כל ימי אדם אשר חי תשע מאות שנה ושלשים שנה וימת׃ 5
Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu.
ויחי שת חמש שנים ומאת שנה ויולד את אנוש׃ 6
Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh.
ויחי שת אחרי הולידו את אנוש שבע שנים ושמנה מאות שנה ויולד בנים ובנות׃ 7
Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויהיו כל ימי שת שתים עשרה שנה ותשע מאות שנה וימת׃ 8
Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.
ויחי אנוש תשעים שנה ויולד את קינן׃ 9
Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan.
ויחי אנוש אחרי הולידו את קינן חמש עשרה שנה ושמנה מאות שנה ויולד בנים ובנות׃ 10
Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויהיו כל ימי אנוש חמש שנים ותשע מאות שנה וימת׃ 11
Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.
ויחי קינן שבעים שנה ויולד את מהללאל׃ 12
Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel.
ויחי קינן אחרי הולידו את מהללאל ארבעים שנה ושמנה מאות שנה ויולד בנים ובנות׃ 13
Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata
ויהיו כל ימי קינן עשר שנים ותשע מאות שנה וימת׃ 14
Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu.
ויחי מהללאל חמש שנים וששים שנה ויולד את ירד׃ 15
Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared.
ויחי מהללאל אחרי הולידו את ירד שלשים שנה ושמנה מאות שנה ויולד בנים ובנות׃ 16
Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata
ויהיו כל ימי מהללאל חמש ותשעים שנה ושמנה מאות שנה וימת׃ 17
Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu.
ויחי ירד שתים וששים שנה ומאת שנה ויולד את חנוך׃ 18
Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok.
ויחי ירד אחרי הולידו את חנוך שמנה מאות שנה ויולד בנים ובנות׃ 19
Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויהיו כל ימי ירד שתים וששים שנה ותשע מאות שנה וימת׃ 20
Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu.
ויחי חנוך חמש וששים שנה ויולד את מתושלח׃ 21
Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela.
ויתהלך חנוך את האלהים אחרי הולידו את מתושלח שלש מאות שנה ויולד בנים ובנות׃ 22
Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויהי כל ימי חנוך חמש וששים שנה ושלש מאות שנה׃ 23
Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365.
ויתהלך חנוך את האלהים ואיננו כי לקח אתו אלהים׃ 24
Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
ויחי מתושלח שבע ושמנים שנה ומאת שנה ויולד את למך׃ 25
Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek.
ויחי מתושלח אחרי הולידו את למך שתים ושמונים שנה ושבע מאות שנה ויולד בנים ובנות׃ 26
Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויהיו כל ימי מתושלח תשע וששים שנה ותשע מאות שנה וימת׃ 27
Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu.
ויחי למך שתים ושמנים שנה ומאת שנה ויולד בן׃ 28
Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa.
ויקרא את שמו נח לאמר זה ינחמנו ממעשנו ומעצבון ידינו מן האדמה אשר אררה יהוה׃ 29
Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.”
ויחי למך אחרי הולידו את נח חמש ותשעים שנה וחמש מאת שנה ויולד בנים ובנות׃ 30
Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da’ya’ya maza da mata.
ויהי כל ימי למך שבע ושבעים שנה ושבע מאות שנה וימת׃ 31
Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu.
ויהי נח בן חמש מאות שנה ויולד נח את שם את חם ואת יפת׃ 32
Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.

< בראשית 5 >