< יחזקאל 35 >
ויהי דבר יהוה אלי לאמר׃ | 1 |
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
בן אדם שים פניך על הר שעיר והנבא עליו׃ | 2 |
“Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir; ka yi annabci a kansa
ואמרת לו כה אמר אדני יהוה הנני אליך הר שעיר ונטיתי ידי עליך ונתתיך שממה ומשמה׃ | 3 |
ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, Dutsen Seyir, zan kuma miƙa hannuna gāba da kai in mai da kai kango.
עריך חרבה אשים ואתה שממה תהיה וידעת כי אני יהוה׃ | 4 |
Zan mai da garuruwanka kufai za ka kuma zama kango. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
יען היות לך איבת עולם ותגר את בני ישראל על ידי חרב בעת אידם בעת עון קץ׃ | 5 |
“‘Domin ka riƙe ƙiyayya ta tun dā, ka kuma ba da mutanen Isra’ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, lokacin da adadin horonsu ya cika,
לכן חי אני נאם אדני יהוה כי לדם אעשך ודם ירדפך אם לא דם שנאת ודם ירדפך׃ | 6 |
saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sa a zub da jininka zan kuwa fafare ka. Da yake ba ka ƙi zub da jini ba, zub da jini zai fafare ka.
ונתתי את הר שעיר לשממה ושממה והכרתי ממנו עבר ושב׃ | 7 |
Zan mai da Dutsen Seyir kango in kuma yanke dukan waɗanda suke shiga da fita a cikinka.
ומלאתי את הריו חלליו גבעותיך וגיאותיך וכל אפיקיך חללי חרב יפלו בהם׃ | 8 |
Zan cika duwatsunka da matattu; waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi a kan tuddanka, da cikin kwarurukanka, da cikin dukan kwazazzabanka.
שממות עולם אתנך ועריך לא תישבנה וידעתם כי אני יהוה׃ | 9 |
Zan mai da kai kango har abada; ba za a zauna a cikin garuruwanka ba. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
יען אמרך את שני הגוים ואת שתי הארצות לי תהיינה וירשנוה ויהוה שם היה׃ | 10 |
“‘Domin kun ce, “Waɗannan al’ummai biyu da ƙasashe za su zama namu za mu kuma mallake su,” ko da yake Ni Ubangiji ina a can,
לכן חי אני נאם אדני יהוה ועשיתי כאפך וכקנאתך אשר עשיתה משנאתיך בם ונודעתי בם כאשר אשפטך׃ | 11 |
saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sāka maka gwargwadon fushi da kuma kishin da ka nuna a ƙiyayyarsu da ka yi zan kuma sanar da kaina a cikinsu sa’ad da na hukunta ka.
וידעת כי אני יהוה שמעתי את כל נאצותיך אשר אמרת על הרי ישראל לאמר שממה לנו נתנו לאכלה׃ | 12 |
Sa’an nan za ka san cewa Ni Ubangiji na ji duk abubuwan banzan da ka faɗa a kan duwatsun Isra’ila. Ka ce, “An mai da su kango an kuma ba mu su mu cinye.”
ותגדילו עלי בפיכם והעתרתם עלי דבריכם אני שמעתי׃ | 13 |
Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai.
כה אמר אדני יהוה כשמח כל הארץ שממה אעשה לך׃ | 14 |
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa yayinda dukan duniya take farin ciki, zan mai da kai kango.
כשמחתך לנחלת בית ישראל על אשר שממה כן אעשה לך שממה תהיה הר שעיר וכל אדום כלה וידעו כי אני יהוה׃ | 15 |
Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’”