< דברים 32 >
האזינו השמים ואדברה ותשמע הארץ אמרי פי׃ | 1 |
Ku saurara, ya ku sammai, zan yi magana; bari duniya ta ji maganar bakina.
יערף כמטר לקחי תזל כטל אמרתי כשעירם עלי דשא וכרביבים עלי עשב׃ | 2 |
Bari koyarwata tă zubo kamar ruwan sama kalmomina kuma su sauko kamar raɓa, kamar yayyafi a kan sabuwar ciyawa, kamar ruwan sama mai yawa a kan tsirai marasa ƙarfi.
כי שם יהוה אקרא הבו גדל לאלהינו׃ | 3 |
Zan yi shelar sunan Ubangiji. Ku yabi girman Allahnmu!
הצור תמים פעלו כי כל דרכיו משפט אל אמונה ואין עול צדיק וישר הוא׃ | 4 |
Shi Dutse ne, ayyukansa cikakku ne, dukan hanyoyinsa kuwa masu adalci ne. Allah mai aminci, wanda ba ya yin rashi gaskiya, shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
שחת לו לא בניו מומם דור עקש ופתלתל׃ | 5 |
Sun aikata mugunta a gabansa; saboda abin kunyarsu, su ba’ya’yansa ba ne, amma wata muguwar tsara ce, karkatacciya.
ה ליהוה תגמלו זאת עם נבל ולא חכם הלוא הוא אביך קנך הוא עשך ויכננך׃ | 6 |
Haka za ku biya Ubangiji, Ya ku wawaye da kuma mutane marasa hikima? Shi ba Ubanku ba ne, Mahaliccinku, wanda ya yi ku, ya kuma siffanta ku?
זכר ימות עולם בינו שנות דור ודור שאל אביך ויגדך זקניך ויאמרו לך׃ | 7 |
Ku tuna da kwanakin dā, ku tuna da tsararrakin da suka wuce tun tuni, Ku tambayi iyayenku, za su faɗa muku, dattawanku, za su kuma bayyana muku.
בהנחל עליון גוים בהפרידו בני אדם יצב גבלת עמים למספר בני ישראל׃ | 8 |
Sa’ad da Mafi Ɗaukaka ya ba da al’ummai gādonsu, sa’ad da ya raba dukan’yan adam, ya kafa iyakoki wa mutane bisa ga yawan’ya’yan Isra’ila maza.
כי חלק יהוה עמו יעקב חבל נחלתו׃ | 9 |
Gama rabon Ubangiji shi ne mutanensa, Yaƙub shi ne rabon gādonsa.
ימצאהו בארץ מדבר ובתהו ילל ישמן יסבבנהו יבוננהו יצרנהו כאישון עינו׃ | 10 |
A cikin hamada ya same shi, a jeji marar amfani, inda namomi suke kuka. Ya tsare shi, ya kuma lura da shi; ya bi da shi kamar ƙwayar idonsa,
כנשר יעיר קנו על גוזליו ירחף יפרש כנפיו יקחהו ישאהו על אברתו׃ | 11 |
kamar gaggafar da take yawo a kan sheƙarta tana rufe’ya’yanta, ta buɗe fikafikanta don tă kwashe su tă ɗauke su a kafaɗunta.
יהוה בדד ינחנו ואין עמו אל נכר׃ | 12 |
Ubangiji kaɗai ya jagorance shi; babu wani baƙon gunkin da yake tare da shi.
ירכבהו על במותי ארץ ויאכל תנובת שדי וינקהו דבש מסלע ושמן מחלמיש צור׃ | 13 |
Ya sa shi ya hau ƙwanƙolin dutse ya ciyar da shi da amfanin gona. Ya shayar da shi da zuma daga dutse, da kuma mai daga dutsen ƙanƙara,
חמאת בקר וחלב צאן עם חלב כרים ואילים בני בשן ועתודים עם חלב כליות חטה ודם ענב תשתה חמר׃ | 14 |
da kindirmo da madara daga shanu da tumaki da ƙibabbun tumaki da awaki, da zaɓaɓɓun ragunan Bashan da kuma ƙwayoyin alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi ja wur mai kumfa.
וישמן ישרון ויבעט שמנת עבית כשית ויטש אלוה עשהו וינבל צור ישעתו׃ | 15 |
Yeshurun ya yi ƙiba, ya yi kauri; cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul. Ya yashe Allahn da ya yi shi, ya ƙi Dutse Cetonsa.
יקנאהו בזרים בתועבת יכעיסהו׃ | 16 |
Suka sa shi kishi saboda baƙin allolinsu, suka husata shi da gumakan banƙyamarsu.
יזבחו לשדים לא אלה אלהים לא ידעום חדשים מקרב באו לא שערום אבתיכם׃ | 17 |
Suka yi hadaya ga aljanu, waɗanda ba Allah ba, ga allolin da ba su sani ba, ga allolin da aka shigo da su daga baya, allolin da kakanninku ba su ji tsoronsu ba.
צור ילדך תשי ותשכח אל מחללך׃ | 18 |
Kuka rabu da Dutsen da ya zama mahaifi gare ku; kuka manta da Allahn da ya haife ku.
וירא יהוה וינאץ מכעס בניו ובנתיו׃ | 19 |
Ubangiji ya ga wannan ya kuma ƙi su, domin’ya’yansa maza da mata sun husata shi.
ויאמר אסתירה פני מהם אראה מה אחריתם כי דור תהפכת המה בנים לא אמן בם׃ | 20 |
Ya ce, “Zan ɓoye fuskata daga gare su, in ga ƙarshensu; gama su muguwar tsara ce,’ya’ya ne marasa aminci.
הם קנאוני בלא אל כעסוני בהבליהם ואני אקניאם בלא עם בגוי נבל אכעיסם׃ | 21 |
Sun sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba, suka kuma husata ni da gumakansu na wofi. Zan sa su yi kishi ta wurin waɗanda ba mutane ba; zan sa su yi fushi ta wurin al’ummar da ba ta da sani.
כי אש קדחה באפי ותיקד עד שאול תחתית ותאכל ארץ ויבלה ותלהט מוסדי הרים׃ (Sheol ) | 22 |
Gama fushina ya kama wuta, tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za tă cinye duniya da girbinta, tă kuma sa wuta a tussan duwatsu. (Sheol )
אספה עלימו רעות חצי אכלה בם׃ | 23 |
“Zan tula masifu a kansu in kuma gama kibiyoyina a kansu.
מזי רעב ולחמי רשף וקטב מרירי ושן בהמות אשלח בם עם חמת זחלי עפר׃ | 24 |
Zan aika da yunwa mai tsanani a kansu, zazzaɓi mai zafi da muguwar annoba; zan aika da haƙoran namun jeji a kansu, da dafin mesa masu ja da ciki.
מחוץ תשכל חרב ומחדרים אימה גם בחור גם בתולה יונק עם איש שיבה׃ | 25 |
Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su, a cikin gidajensu kuma tsoro zai mamaye su.’Yan maza da’yan mata za su hallaka, haka ma jarirai da maza masu furfura.
אמרתי אפאיהם אשביתה מאנוש זכרם׃ | 26 |
Na ce zan watsar da su in sa a manta da su a tunanin’yan adam.
לולי כעס אויב אגור פן ינכרו צרימו פן יאמרו ידינו רמה ולא יהוה פעל כל זאת׃ | 27 |
Amma ina tsoron tsokanar abokin gāba, don kada abokan gāba su kāsa ganewa har su ce, ‘Hannunmu ne ya yi nasara; ba Ubangiji ne ya aikata dukan wannan ba.’”
כי גוי אבד עצות המה ואין בהם תבונה׃ | 28 |
Al’ummai ne marasa azanci, babu ganewa a cikinsu.
לו חכמו ישכילו זאת יבינו לאחריתם׃ | 29 |
A ce su masu hikima ne har su gane wannan su gane abin da ƙarshensu zai zama!
איכה ירדף אחד אלף ושנים יניסו רבבה אם לא כי צורם מכרם ויהוה הסגירם׃ | 30 |
Yaya mutum guda zai kore dubu, mutum biyu su sa dubu goma su gudu, sai ko Dutsensu ya sayar da su, sai ko Ubangiji ya bashe su.
כי לא כצורנו צורם ואיבינו פלילים׃ | 31 |
Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne, abokan gābanmu sun san da haka.
כי מגפן סדם גפנם ומשדמת עמרה ענבמו ענבי רוש אשכלת מררת למו׃ | 32 |
Kuringarsu ta fito daga kuringar Sodom ne, daga gonakin Gomorra kuma.’Ya’yan inabinsu dafi ne, nonnansu masu ɗaci ne.
חמת תנינם יינם וראש פתנים אכזר׃ | 33 |
Ruwan inabinsu dafin macizai ne, mugun dafin gamshaƙa ne.
הלא הוא כמס עמדי חתם באוצרתי׃ | 34 |
“Ban jibge wannan a ma’ajiya na kuma yimƙe shi a taskokina ba?
לי נקם ושלם לעת תמוט רגלם כי קרוב יום אידם וחש עתדת למו׃ | 35 |
Sakayya nawa ne, zan kuwa ɗau fansa. A cikin lokaci, ƙafarsu za tă yi santsi; ranar masifarsu ta yi kusa hallakarsu kuma tana gaggautawa a kansu.”
כי ידין יהוה עמו ועל עבדיו יתנחם כי יראה כי אזלת יד ואפס עצור ועזוב׃ | 36 |
Ubangiji zai shari’anta mutanensa yă kuma ji tausayin bayinsa sa’ad da ya ga ƙarfinsu ya ƙare babu kowa kuma da ya rage, bawa ko’yantacce.
ואמר אי אלהימו צור חסיו בו׃ | 37 |
Zai ce, “To, ina allolinsu, dutsen da suka yi mafaka a ciki,
אשר חלב זבחימו יאכלו ישתו יין נסיכם יקומו ויעזרכם יהי עליכם סתרה׃ | 38 |
allolin da suka ci kitsen hadayunsu suka kuma sha ruwan inabin hadayunsu? Ku sa su tashi su taimake ku mana! Bari su ba ku mafaka!
ראו עתה כי אני אני הוא ואין אלהים עמדי אני אמית ואחיה מחצתי ואני ארפא ואין מידי מציל׃ | 39 |
“Ku duba yanzu cewa ni ne Shi! Ba wani allah in ban da ni. Nakan kashe in kuma rayar, nakan sa rauni in kuma warkar, ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.
כי אשא אל שמים ידי ואמרתי חי אנכי לעלם׃ | 40 |
Na ɗaga hannu sama na kuma furta. Muddin ina raye har abada,
אם שנותי ברק חרבי ותאחז במשפט ידי אשיב נקם לצרי ולמשנאי אשלם׃ | 41 |
sa’ad da na wasa takobi mai walƙiya hannuna kuwa ya cafke shi don yin hukunci, zan ɗau fansa a kan abokan gābana in sāka wa waɗanda suke ƙina.
אשכיר חצי מדם וחרבי תאכל בשר מדם חלל ושביה מראש פרעות אויב׃ | 42 |
Zan sa kibiyoyina su bugu da jini, yayinda takobina yana cin nama, jinin kisassu da na kamammu, kawunan shugabannin abokan gāba.”
הרנינו גוים עמו כי דם עבדיו יקום ונקם ישיב לצריו וכפר אדמתו עמו׃ | 43 |
Ku yi farin ciki, ya ku al’ummai, tare da mutanensa, gama zai rama ɗau fansar jinin bayinsa; zai ɗau fansa a kan abokan gābansa yă kuma yi kafara domin ƙasarsa da mutanensa.
ויבא משה וידבר את כל דברי השירה הזאת באזני העם הוא והושע בן נון׃ | 44 |
Sai Musa ya zo da Yoshuwa ɗan Nun suka faɗa dukan waɗannan kalmomi wannan waƙa a kunnen mutane.
ויכל משה לדבר את כל הדברים האלה אל כל ישראל׃ | 45 |
Sa’ad da Musa ya gama karanta waɗannan kalmomi ga dukan Isra’ila,
ויאמר אלהם שימו לבבכם לכל הדברים אשר אנכי מעיד בכם היום אשר תצום את בניכם לשמר לעשות את כל דברי התורה הזאת׃ | 46 |
ya ce musu, “Ku riƙe dukan kalmomin da na furta muku a yau, don ku umarce’ya’yanku su lura, su yi biyayya da dukan kalmomin wannan doka.
כי לא דבר רק הוא מכם כי הוא חייכם ובדבר הזה תאריכו ימים על האדמה אשר אתם עברים את הירדן שמה לרשתה׃ | 47 |
Ba kalmomi kurum ba ne dominku, amma har ranku ma. Ta wurinsu za ku yi tsawon rai a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.”
וידבר יהוה אל משה בעצם היום הזה לאמר׃ | 48 |
A wannan rana Ubangiji ya ce wa Musa,
עלה אל הר העברים הזה הר נבו אשר בארץ מואב אשר על פני ירחו וראה את ארץ כנען אשר אני נתן לבני ישראל לאחזה׃ | 49 |
“Ka hau Duwatsun Abarim zuwa Dutsen Nebo a Mowab, tsallake daga Yeriko, ka hangi Kan’ana, ƙasar da nake ba wa Isra’ilawa gādo.
ומת בהר אשר אתה עלה שמה והאסף אל עמיך כאשר מת אהרן אחיך בהר ההר ויאסף אל עמיו׃ | 50 |
A can kan dutsen da ka hau za ka mutu a kuma tara ka ga mutanenka, kamar yadda ɗan’uwanka Haruna ya mutu a Dutsen Hor aka kuma tara shi ga mutanensa.
על אשר מעלתם בי בתוך בני ישראל במי מריבת קדש מדבר צן על אשר לא קדשתם אותי בתוך בני ישראל׃ | 51 |
Wannan kuwa domin ku biyu kun fid da aminci gare ni a gaban Isra’ilawa a ruwan Meriba ta Kadesh, a Hamadar Zin kuma saboda ba ku riƙe tsarkina a cikin Isra’ilawa ba.
כי מנגד תראה את הארץ ושמה לא תבוא אל הארץ אשר אני נתן לבני ישראל׃ | 52 |
Saboda haka, za ka ga ƙasar daga nesa kawai; ba za ka shiga ƙasar da nake ba wa mutanen Isra’ila ba.”