< דברי הימים ב 18 >

ויהי ליהושפט עשר וכבוד לרב ויתחתן לאחאב׃ 1
Yanzu fa Yehoshafat ya wadace ƙwarai yana kuma da girma, ya kuma haɗa kansa da Ahab ta wurin aure.
וירד לקץ שנים אל אחאב לשמרון ויזבח לו אחאב צאן ובקר לרב ולעם אשר עמו ויסיתהו לעלות אל רמות גלעד׃ 2
Bayan’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad.
ויאמר אחאב מלך ישראל אל יהושפט מלך יהודה התלך עמי רמת גלעד ויאמר לו כמוני כמוך וכעמך עמי ועמך במלחמה׃ 3
Ahab sarkin Isra’ila ya tambayi Yehoshafat sarkin Yahuda ya ce, “Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Ni kamar kai ne, kuma mutanena kamar naka ne; za mu tafi tare da kai a yaƙin.”
ויאמר יהושפט אל מלך ישראל דרש נא כיום את דבר יהוה׃ 4
Amma Yehoshafat ya kuma ce wa sarkin Isra’ila, “Da fari mu nemi bishewar Ubangiji.”
ויקבץ מלך ישראל את הנבאים ארבע מאות איש ויאמר אלהם הנלך אל רמת גלעד למלחמה אם אחדל ויאמרו עלה ויתן האלהים ביד המלך׃ 5
Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa duka, mutane ɗari huɗu, ya kuma tambaye su, “Mu tafi yaƙi a kan Ramot Gileyad ko kada mu tafi?” Suka amsa “Tafi, gama Allah zai ba da shi cikin hannun sarki.”
ויאמר יהושפט האין פה נביא ליהוה עוד ונדרשה מאתו׃ 6
Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?”
ויאמר מלך ישראל אל יהושפט עוד איש אחד לדרוש את יהוה מאתו ואני שנאתיהו כי איננו מתנבא עלי לטובה כי כל ימיו לרעה הוא מיכיהו בן ימלא ויאמר יהושפט אל יאמר המלך כן׃ 7
Sarki Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, “Akwai guda har yanzu mai suna Mikahiya ɗan Imla, za mu iya nemi nufin Ubangiji daga gare shi, sai dai ba na sonsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai kullum masifa.” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Kada sarki yă faɗa haka.”
ויקרא מלך ישראל אל סריס אחד ויאמר מהר מיכהו בן ימלא׃ 8
Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin ma’aikatansa ya ce, “A kawo Mikahiya ɗan Imla nan da nan.”
ומלך ישראל ויהושפט מלך יהודה יושבים איש על כסאו מלבשים בגדים וישבים בגרן פתח שער שמרון וכל הנביאים מתנבאים לפניהם׃ 9
Saye da rigunan sarakuna, sarki Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zaune a kan kujerunsu na mulki a masussuka ta ƙofar shigar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu.
ויעש לו צדקיהו בן כנענה קרני ברזל ויאמר כה אמר יהוה באלה תנגח את ארם עד כלותם׃ 10
To, fa, Zedekiya ɗan Kena’ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka sassoki Arameyawa sai sun hallaka.’”
וכל הנבאים נבאים כן לאמר עלה רמת גלעד והצלח ונתן יהוה ביד המלך׃ 11
Dukan sauran annabawan suka yi irin annabcin nan. Suka ce, “A haura zuwa Ramot Gileyad a yi nasara, gama Ubangiji zai ba da shi cikin hannun sarki.”
והמלאך אשר הלך לקרא למיכיהו דבר אליו לאמר הנה דברי הנבאים פה אחד טוב אל המלך ויהי נא דברך כאחד מהם ודברת טוב׃ 12
Ɗan saƙon da ya tafi don yă kawo Mikahiya kuwa ya ce masa, “Duba, kowannen a cikin annabawa ya yi faɗin nasara wa sarki. Don haka kai ma ka yi maganar da za tă gamshi sarki kamar yadda suka yi.”
ויאמר מיכיהו חי יהוה כי את אשר יאמר אלהי אתו אדבר׃ 13
Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji, zan faɗa masa kawai abin da Allahna ya faɗa.”
ויבא אל המלך ויאמר המלך אליו מיכה הנלך אל רמת גלעד למלחמה אם אחדל ויאמר עלו והצליחו וינתנו בידכם׃ 14
Da suka iso, sarki ya tambaye shi, “Mika, mu tafi mu yaƙi Ramot Gileyad, ko kada mu tafi?” Ya amsa, “Kai masa yaƙi za ka kuwa yi nasara, gama za a ba da su a hannunka.”
ויאמר אליו המלך עד כמה פעמים אני משביעך אשר לא תדבר אלי רק אמת בשם יהוה׃ 15
Sarki ya ce masa, “Sau nawa zan sa ka rantse don ka faɗa gaskiya a cikin sunan Ubangiji?”
ויאמר ראיתי את כל ישראל נפוצים על ההרים כצאן אשר אין להן רעה ויאמר יהוה לא אדנים לאלה ישובו איש לביתו בשלום׃ 16
Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila sun warwatsu a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyaya, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowanne yă tafi gida cikin salama.’”
ויאמר מלך ישראל אל יהושפט הלא אמרתי אליך לא יתנבא עלי טוב כי אם לרע׃ 17
Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka cewa bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni, in ba masifa ba?”
ויאמר לכן שמעו דבר יהוה ראיתי את יהוה יושב על כסאו וכל צבא השמים עמדים על ימינו ושמאלו׃ 18
Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka sai ka ji maganar Ubangiji. Na ga Ubangiji yana zama a kan kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye a damansa da hagunsa.
ויאמר יהוה מי יפתה את אחאב מלך ישראל ויעל ויפל ברמות גלעד ויאמר זה אמר ככה וזה אמר ככה׃ 19
Ubangiji kuwa ya ce, ‘Wa zai ruɗe Ahab sarki Isra’ila zuwa yaƙi da Ramot Gileyad da kuma zuwa mutuwarsa a can?’ “Wani ya ba da wata shawara, wani kuma wata dabam.
ויצא הרוח ויעמד לפני יהוה ויאמר אני אפתנו ויאמר יהוה אליו במה׃ 20
A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “Ubangiji ya yi tambaya, ‘Ta wace hanya?’
ויאמר אצא והייתי לרוח שקר בפי כל נביאיו ויאמר תפתה וגם תוכל צא ועשה כן׃ 21
“Ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’
ועתה הנה נתן יהוה רוח שקר בפי נביאיך אלה ויהוה דבר עליך רעה׃ 22
“To yanzu, Ubangiji ya sa ruhun ruɗu a bakunan waɗannan annabawanka. Ubangiji ya ƙayyade masifa dominka.”
ויגש צדקיהו בן כנענה ויך את מיכיהו על הלחי ויאמר אי זה הדרך עבר רוח יהוה מאתי לדבר אתך׃ 23
Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya haura ya mari Mikahiya a fuska. Ya ce, “Ta wace hanya ce ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai?”
ויאמר מיכיהו הנך ראה ביום ההוא אשר תבוא חדר בחדר להחבא׃ 24
Mikahiya ya amsa ya ce, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a can cikin ɗaki.”
ויאמר מלך ישראל קחו את מיכיהו והשיבהו אל אמון שר העיר ואל יואש בן המלך׃ 25
Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ɗauki Mikahiya ku aika da shi zuwa ga Amon mai mulkin birni da kuma ga Yowash ɗan sarki,
ואמרתם כה אמר המלך שימו זה בית הכלא והאכלהו לחם לחץ ומים לחץ עד שובי בשלום׃ 26
ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku jefa wannan mutum a kurkuku kada kuma ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa har sai na dawo lafiya.’”
ויאמר מיכיהו אם שוב תשוב בשלום לא דבר יהוה בי ויאמר שמעו עמים כלם׃ 27
Mikahiya ya furta ya ce, “Idan har ka dawo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana ta wurina ba.” Ya kuma ƙara da cewa, “Dukanku mutane, ku lura da maganata!”
ויעל מלך ישראל ויהושפט מלך יהודה אל רמת גלעד׃ 28
Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad.
ויאמר מלך ישראל אל יהושפט התחפש ובוא במלחמה ואתה לבש בגדיך ויתחפש מלך ישראל ויבאו במלחמה׃ 29
Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama in shiga yaƙin, amma ka sa kayanka na sarauta.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya ɓad da kama ya shiga cikin yaƙin.
ומלך ארם צוה את שרי הרכב אשר לו לאמר לא תלחמו את הקטן את הגדול כי אם את מלך ישראל לבדו׃ 30
To, fa, sarkin Aram ya umarce shugabannin keken yaƙinsa ya ce, “Kada ku yaƙi kowa, ƙarami ko babba, sai dai sarkin Isra’ila.”
ויהי כראות שרי הרכב את יהושפט והמה אמרו מלך ישראל הוא ויסבו עליו להלחם ויזעק יהושפט ויהוה עזרו ויסיתם אלהים ממנו׃ 31
Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙi suka ga Yehoshafat, sai suka yi tsammani, “Wannan ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juya don su yaƙe shi, amma Yehoshafat ya yi ihu, Ubangiji kuma ya taimake shi. Allah ya janye su daga gare shi,
ויהי כראות שרי הרכב כי לא היה מלך ישראל וישבו מאחריו׃ 32
gama sa’ad da shugabannin keken yaƙi suka ga cewa ba shi ne sarkin Isra’ila ba, sai suka daina binsa.
ואיש משך בקשת לתמו ויך את מלך ישראל בין הדבקים ובין השרין ויאמר לרכב הפך ידיך והוצאתני מן המחנה כי החליתי׃ 33
Amma wani ya harba kibiya haka kawai, sai kibiyar ta sami sarki Ahab na Isra’ila a kafaɗa tsakanin rigar yaƙinsa na ƙarfe da ƙarfen ƙirjinsa. Sai sarki ya ce wa mai tuƙan keken yaƙi, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin. An ji mini rauni.”
ותעל המלחמה ביום ההוא ומלך ישראל היה מעמיד במרכבה נכח ארם עד הערב וימת לעת בוא השמש׃ 34
Duk yini yaƙi ya yi ta cin gaba, sarkin Isra’ila kuwa ya jingina kansa a cikin keken yaƙinsa yana duban Arameyawa har yamma. Sa’an nan a fāɗuwar rana sai ya mutu.

< דברי הימים ב 18 >