< תְהִלִּים 17 >
תְּפִלָּ֗ה לְדָ֫וִ֥ד שִׁמְעָ֤ה יְהוָ֨ה ׀ צֶ֗דֶק הַקְשִׁ֥יבָה רִנָּתִ֗י הַאֲזִ֥ינָה תְפִלָּתִ֑י בְּ֝לֹ֗א שִׂפְתֵ֥י מִרְמָֽה׃ | 1 |
Addu’a ce ta Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci; ka saurari kukata. Ka kasa kunne ga addu’ata, ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya.
מִ֭לְּפָנֶיךָ מִשְׁפָּטִ֣י יֵצֵ֑א עֵ֝ינֶ֗יךָ תֶּחֱזֶ֥ינָה מֵישָׁרִֽים׃ | 2 |
Bari fiffitawata tă zo daga gare ka; bari idanunka su ga abin da yake daidai.
בָּ֘חַ֤נְתָּ לִבִּ֨י ׀ פָּ֘קַ֤דְתָּ לַּ֗יְלָה צְרַפְתַּ֥נִי בַל־תִּמְצָ֑א זַ֝מֹּתִ֗י בַּל־יַעֲבָר־פִּֽי׃ | 3 |
Ko ka duba zuciyata, ka kuma bincike ni da dare, ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba; na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.
לִפְעֻלֹּ֣ות אָ֭דָם בִּדְבַ֣ר שְׂפָתֶ֑יךָ אֲנִ֥י שָׁ֝מַ֗רְתִּי אָרְחֹ֥ות פָּרִֽיץ׃ | 4 |
Game da ayyukan mutane kuwa, ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina daga hanyoyin tashin hankali.
תָּמֹ֣ךְ אֲ֭שֻׁרַי בְּמַעְגְּלֹותֶ֑יךָ בַּל־נָמֹ֥וטּוּ פְעָמָֽי׃ | 5 |
Sawuna sun kama hanyoyinka ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba.
אֲנִֽי־קְרָאתִ֣יךָ כִֽי־תַעֲנֵ֣נִי אֵ֑ל הַֽט־אָזְנְךָ֥ לִ֝֗י שְׁמַ֣ע אִמְרָתִֽי׃ | 6 |
Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini; ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata.
הַפְלֵ֣ה חֲ֭סָדֶיךָ מֹושִׁ֣יעַ חֹוסִ֑ים מִ֝מִּתְקֹומְמִ֗ים בִּֽימִינֶֽךָ׃ | 7 |
Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki, kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu da hannunka na dama.
שָׁ֭מְרֵנִי כְּאִישֹׁ֣ון בַּת־עָ֑יִן בְּצֵ֥ל כְּ֝נָפֶ֗יךָ תַּסְתִּירֵֽנִי׃ | 8 |
Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido; ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka
מִפְּנֵ֣י רְ֭שָׁעִים ז֣וּ שַׁדּ֑וּנִי אֹיְבַ֥י בְּ֝נֶ֗פֶשׁ יַקִּ֥יפוּ עָלָֽי׃ | 9 |
daga mugaye waɗanda suke kai mini hari, daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.
חֶלְבָּ֥מֹו סָּגְר֑וּ פִּ֝֗ימֹו דִּבְּר֥וּ בְגֵאֽוּת׃ | 10 |
Sun rufe zukatansu marar tausayi, da bakunansu suna magana da fariya.
אַ֭שֻּׁרֵינוּ עַתָּ֣ה סְבָבוּנִי (סְבָב֑וּנוּ) עֵינֵיהֶ֥ם יָ֝שִׁ֗יתוּ לִנְטֹ֥ות בָּאָֽרֶץ׃ | 11 |
Sun sa mini ido, yanzu sun kewaye ni, a shirye suke, su jefa ni a ƙasa.
דִּמְיֹנֹ֗ו כְּ֭אַרְיֵה יִכְסֹ֣וף לִטְרֹ֑וף וְ֝כִכְפִ֗יר יֹשֵׁ֥ב בְּמִסְתָּרֽ͏ִים׃ | 12 |
Suna kama da zaki mai yunwan abinci, kamar babban zaki mai fako a maɓuya.
קוּמָ֤ה יְהוָ֗ה קַדְּמָ֣ה פָ֭נָיו הַכְרִיעֵ֑הוּ פַּלְּטָ֥ה נַ֝פְשִׁ֗י מֵרָשָׁ֥ע חַרְבֶּֽךָ׃ | 13 |
Ka tashi, ya Ubangiji, ka yi arangama da su, ka durƙusar da su; ka cece ni daga mugaye ta wurin takobinka.
מִֽמְתִ֥ים יָדְךָ֨ ׀ יְהוָ֡ה מִֽמְתִ֬ים מֵחֶ֗לֶד חֶלְקָ֥ם בַּֽחַיִּים֮ וּצְפִינְךָ (וּֽצְפוּנְךָ֮) תְּמַלֵּ֪א בִ֫טְנָ֥ם יִשְׂבְּע֥וּ בָנִ֑ים וְהִנִּ֥יחוּ יִ֝תְרָ֗ם לְעֹולְלֵיהֽ͏ֶם׃ | 14 |
Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan, daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne. Kakan cika yunwan waɗanda kake so;’ya’yansu suna da isashe suna kuma ajiyar wadata wa’ya’yansu.
אֲנִ֗י בְּ֭צֶדֶק אֶחֱזֶ֣ה פָנֶ֑יךָ אֶשְׂבְּעָ֥ה בְ֝הָקִ֗יץ תְּמוּנָתֶֽךָ׃ | 15 |
Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.