< תהילים 67 >
לַמְנַצֵּחַ בִּנְגִינֹת מִזְמוֹר שִֽׁיר׃ אֱֽלֹהִים יְחׇנֵּנוּ וִיבָרְכֵנוּ יָאֵֽר פָּנָיו אִתָּנוּ סֶֽלָה׃ | 1 |
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, (Sela)
לָדַעַת בָּאָרֶץ דַּרְכֶּךָ בְּכׇל־גּוֹיִם יְשׁוּעָתֶֽךָ׃ | 2 |
don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai.
יוֹדוּךָ עַמִּים ׀ אֱלֹהִים יוֹדוּךָ עַמִּים כֻּלָּֽם׃ | 3 |
Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.
יִשְׂמְחוּ וִירַנְּנוּ לְאֻמִּים כִּֽי־תִשְׁפֹּט עַמִּים מִישֹׁר וּלְאֻמִּים ׀ בָּאָרֶץ תַּנְחֵם סֶֽלָה׃ | 4 |
Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. (Sela)
יוֹדוּךָ עַמִּים ׀ אֱלֹהִים יוֹדוּךָ עַמִּים כֻּלָּֽם׃ | 5 |
Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe.
אֶרֶץ נָתְנָה יְבוּלָהּ יְבָרְכֵנוּ אֱלֹהִים אֱלֹהֵֽינוּ׃ | 6 |
Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.
יְבָרְכֵנוּ אֱלֹהִים וְיִֽירְאוּ אוֹתוֹ כׇּל־אַפְסֵי־אָֽרֶץ׃ | 7 |
Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.