< זכריה 9 >
משא דבר יהוה בארץ חדרך ודמשק מנחתו כי ליהוה עין אדם וכל שבטי ישראל | 1 |
Annabci. Maganar Ubangiji tana gāba da ƙasar Hadrak za tă kuma sauko a kan Damaskus, gama idanun dukan mutane da na kabilan Isra’ila suna a kan Ubangiji,
וגם חמת תגבל בה צר וצידון כי חכמה מאד | 2 |
da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita, da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai.
ותבן צר מצור לה ותצבר כסף כעפר וחרוץ כטיט חוצות | 3 |
Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi; ta tara azurfa kamar ƙasa, zinariya kuma kamar tarin shara a tituna.
הנה אדני יורשנה והכה בים חילה והיא באש תאכל | 4 |
Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta, zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku, wuta kuma za tă cinye ta.
תרא אשקלון ותירא ועזה ותחיל מאד ועקרון כי הביש מבטה ואבד מלך מעזה ואשקלון לא תשב | 5 |
Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro; Gaza za tă yi birgima cikin azaba, haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya. Gaza za tă rasa sarkinta za a kuma gudu a bar Ashkelon.
וישב ממזר באשדוד והכרתי גאון פלשתים | 6 |
Baƙi za su mallaki Ashdod, kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa.
והסרתי דמיו מפיו ושקציו מבין שניו ונשאר גם הוא לאלהינו והיה כאלף ביהודה ועקרון כיבוסי | 7 |
Zan kawar da jini daga bakinsu, zan kuma cire abincin da aka haramta daga tsakanin haƙoransu. Waɗanda za a bari za su zama na Allahnmu, su kuma zama shugabanni a Yahuda, Ekron kuma za tă zama kamar Yebusiyawa.
וחניתי לביתי מצבה מעבר ומשב ולא יעבר עליהם עוד נגש כי עתה ראיתי בעיני | 8 |
Amma zan kāre gidana daga sojoji masu kai da kawowa. Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba, gama yanzu ina tsaro.
גילי מאד בת ציון הריעי בת ירושלם הנה מלכך יבוא לך צדיק ונושע הוא עני ורכב על חמור ועל עיר בן אתנות | 9 |
Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan’yar jaka.
והכרתי רכב מאפרים וסוס מירושלם ונכרתה קשת מלחמה ודבר שלום לגוים ומשלו מים עד ים ומנהר עד אפסי ארץ | 10 |
Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim, da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima, za a kuma karya bakan yaƙi. Zai yi shelar salama ga al’ummai. Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku, daga Kogi kuma zuwa ƙarshen duniya.
גם את בדם בריתך שלחתי אסיריך מבור אין מים בו | 11 |
Ke kuma, saboda jinin alkawarina da ke, zan’yantar da’yan kurkukunki daga rami marar ruwa.
שובו לבצרון אסירי התקוה גם היום מגיד משנה אשיב לך | 12 |
Ku koma maɓuya, ya ku’yan kurkuku masu sa zuciya; ko yanzu ma na sanar cewa zan mayar muku ninki biyu.
כי דרכתי לי יהודה קשת מלאתי אפרים ועוררתי בניך ציון על בניך יון ושמתיך כחרב גבור | 13 |
Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana, in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya. Zan tā da’ya’yanki maza, ya Sihiyona, gāba da’ya’yanki, ya Girka, in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi.
ויהוה עליהם יראה ויצא כברק חצו ואדני יהוה בשופר יתקע והלך בסערות תימן | 14 |
Sa’an nan Ubangiji zai bayyana a bisansu; kibiyarsa za tă wulga kamar walƙiya. Ubangiji Mai Iko Duka zai busa ƙaho; zai taho ta cikin guguwa daga kudu,
יהוה צבאות יגן עליהם ואכלו וכבשו אבני קלע ושתו המו כמו יין ומלאו כמזרק--כזויות מזבח | 15 |
Ubangiji Maɗaukaki kuma zai tsare su. Za su hallakar su kuma yi nasara da duwatsun majajjawa. Za su sha su yi kururuwa kamar sun sha ruwan inabi; za su cika kamar kwanon da ake amfani don a yayyafa jini a kusurwoyin bagade.
והושיעם יהוה אלהיהם ביום ההוא--כצאן עמו כי אבני נזר מתנוססות על אדמתו | 16 |
Ubangiji Allahnsu zai cece su a wannan rana gama su mutanensa ne da kuma garkensa. Za su haska a cikin ƙasarsa kamar lu’ulu’u a rawani.
כי מה טובו ומה יפיו--דגן בחורים ותירוש ינובב בתלות | 17 |
Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa! Hatsi zai sa samari su yi murna, sabon ruwan inabi kuma zai sa’yan mata su yi farin ciki.