< תהילים 9 >

למנצח על-מות לבן מזמור לדוד ב אודה יהוה בכל-לבי אספרה כל-נפלאותיך 1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
אשמחה ואעלצה בך אזמרה שמך עליון 2
Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka; zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
בשוב-אויבי אחור יכשלו ויאבדו מפניך 3
Abokan gābana sun ja da baya; suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka.
כי-עשית משפטי ודיני ישבת לכסא שופט צדק 4
Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi; ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci.
גערת גוים אבדת רשע שמם מחית לעולם ועד 5
Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye; ka shafe sunansu har abada abadin.
האויב תמו חרבות--לנצח וערים נתשת--אבד זכרם המה 6
Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu, ka tuttumɓuke biranensu; yadda ma ba aka ƙara tunaninsu.
ויהוה לעולם ישב כונן למשפט כסאו 7
Ubangiji yana mulki har abada; ya kafa kujerarsa don shari’a.
והוא ישפט-תבל בצדק ידין לאמים במישרים 8
Zai hukunta duniya da adalci; zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.
ויהי יהוה משגב לדך משגב לעתות בצרה 9
Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala.
ויבטחו בך יודעי שמך כי לא-עזבת דרשיך יהוה 10
Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
זמרו--ליהוה ישב ציון הגידו בעמים עלילותיו 11
Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona; yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata.
כי-דרש דמים אותם זכר לא-שכח צעקת עניים (ענוים) 12
Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala.
חננני יהוה--ראה עניי משנאי מרוממי משערי מות 13
Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini! Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,
למען אספרה כל-תהלתיך בשערי בת-ציון--אגילה בישועתך 14
don in furta yabanka cikin ƙofofin’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.
טבעו גוים בשחת עשו ברשת-זו טמנו נלכדה רגלם 15
Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu; aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye.
נודע יהוה--משפט עשה בפעל כפיו נוקש רשע הגיון סלה 16
An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa; an kama mugaye da aikin hannuwansu. Haggayiyon. (Sela)
ישובו רשעים לשאולה כל-גוים שכחי אלהים (Sheol h7585) 17
Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah. (Sheol h7585)
כי לא לנצח ישכח אביון תקות ענוים (עניים) תאבד לעד 18
Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba, ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.
קומה יהוה אל-יעז אנוש ישפטו גוים על-פניך 19
Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka.
שיתה יהוה מורה--להם ידעו גוים--אנוש המה סלה 20
Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. (Sela)

< תהילים 9 >