< תהילים 88 >
שיר מזמור לבני-קרח למנצח על-מחלת לענות משכיל להימן האזרחי ב יהוה אלהי ישועתי-- יום-צעקתי בלילה נגדך | 1 |
Waƙa ce, Zabura ta’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannotmaskil na Heman dangin Ezra. Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka.
תבוא לפניך תפלתי הטה אזנך לרנתי | 2 |
Bari addu’ata ta zo a gabanka; ka kasa kunne ga kukata.
כי-שבעה ברעות נפשי וחיי לשאול הגיעו (Sheol ) | 3 |
Gama raina yana cike da wahala rayuwata tana gab da kabari. (Sheol )
נחשבתי עם-יורדי בור הייתי כגבר אין-איל | 4 |
An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami; ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.
במתים חפשי כמו חללים שכבי קבר-- אשר לא זכרתם עוד והמה מידך נגזרו | 5 |
An ware ni tare da matattu, kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari, waɗanda ba ka ƙara tunawa, waɗanda aka yanke daga taimakonka.
שתני בבור תחתיות במחשכים במצלות | 6 |
Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa cikin zurfafa mafi duhu.
עלי סמכה חמתך וכל-משבריך ענית סלה | 7 |
Hasalarka tana da nauyi a kaina; ka turmushe ni da dukan raƙumanka. (Sela)
הרחקת מידעי ממני שתני תועבות למו כלא ולא אצא | 8 |
Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta
עיני דאבה מני-עני קראתיך יהוה בכל-יום שטחתי אליך כפי | 9 |
idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka.
הלמתים תעשה-פלא אם-רפאים יקומו יודוך סלה | 10 |
Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? (Sela)
היספר בקבר חסדך אמונתך באבדון | 11 |
Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?
היודע בחשך פלאך וצדקתך בארץ נשיה | 12 |
An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira?
ואני אליך יהוה שועתי ובבקר תפלתי תקדמך | 13 |
Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.
למה יהוה תזנח נפשי תסתיר פניך ממני | 14 |
Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?
עני אני וגוע מנער נשאתי אמיך אפונה | 15 |
Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.
עלי עברו חרוניך בעותיך צמתותני | 16 |
Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni.
סבוני כמים כל-היום הקיפו עלי יחד | 17 |
Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum.
הרחקת ממני אהב ורע מידעי מחשך | 18 |
Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa.