< תהילים 87 >

לבני-קרח מזמור שיר יסודתו בהררי-קדש 1
Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.
אהב יהוה שערי ציון-- מכל משכנות יעקב 2
Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.
נכבדות מדבר בך-- עיר האלהים סלה 3
Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, (Sela)
אזכיר רהב ובבל-- לידעי הנה פלשת וצר עם-כוש זה ילד-שם 4
“Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’”
ולציון יאמר-- איש ואיש ילד-בה והוא יכוננה עליון 5
Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”
יהוה--יספר בכתוב עמים זה ילד-שם סלה 6
Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” (Sela)
ושרים כחללים-- כל-מעיני בך 7
Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”

< תהילים 87 >