< תהילים 82 >

מזמור לאסף אלהים נצב בעדת-אל בקרב אלהים ישפט 1
Zabura ta Asaf. Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.
עד-מתי תשפטו-עול ופני רשעים תשאו-סלה 2
“Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? (Sela)
שפטו-דל ויתום עני ורש הצדיקו 3
Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.
פלטו-דל ואביון מיד רשעים הצילו 4
Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.
לא ידעו ולא יבינו-- בחשכה יתהלכו ימוטו כל-מוסדי ארץ 5
“Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya.
אני-אמרתי אלהים אתם ובני עליון כלכם 6
“Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.
אכן כאדם תמותון וכאחד השרים תפלו 7
Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”
קומה אלהים שפטה הארץ כי-אתה תנחל בכל-הגוים 8
Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.

< תהילים 82 >