< תהילים 72 >

לשלמה אלהים--משפטיך למלך תן וצדקתך לבן-מלך 1
Ta Solomon. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka.
ידין עמך בצדק וענייך במשפט 2
Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.
ישאו הרים שלום לעם וגבעות בצדקה 3
Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.
ישפט עניי-עם--יושיע לבני אביון וידכא עושק 4
Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.
ייראוך עם-שמש ולפני ירח דור דורים 5
Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai.
ירד כמטר על-גז כרביבים זרזיף ארץ 6
Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
יפרח-בימיו צדיק ורב שלום עד-בלי ירח 7
A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.
וירד מים עד-ים ומנהר עד-אפסי-ארץ 8
Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.
לפניו יכרעו ציים ואיביו עפר ילחכו 9
Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.
מלכי תרשיש ואיים מנחה ישיבו מלכי שבא וסבא אשכר יקריבו 10
Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai.
וישתחוו-לו כל-מלכים כל-גוים יעבדוהו 11
Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa.
כי-יציל אביון משוע ועני ואין-עזר לו 12
Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
יחס על-דל ואביון ונפשות אביונים יושיע 13
Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.
מתוך ומחמס יגאל נפשם וייקר דמם בעיניו 14
Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.
ויחי-- ויתן-לו מזהב שבא ויתפלל בעדו תמיד כל-היום יברכנהו 15
Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini.
יהי פסת-בר בארץ-- בראש הרים ירעש כלבנון פריו ויציצו מעיר כעשב הארץ 16
Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar; bari yă cika bisan tuddai. Bari’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon; bari yă bazu kamar ciyayi a gona.
יהי שמו לעולם-- לפני-שמש ינין (ינון) שמו ויתברכו בו כל-גוים יאשרוהו 17
Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka.
ברוך יהוה אלהים--אלהי ישראל עשה נפלאות לבדו 18
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.
וברוך שם כבודו-- לעולם וימלא כבודו את-כל הארץ-- אמן ואמן 19
Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada; bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa.
כלו תפלות-- דוד בן-ישי 20
Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse.

< תהילים 72 >