< תהילים 66 >
למנצח שיר מזמור הריעו לאלהים כל-הארץ | 1 |
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura. Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!
זמרו כבוד-שמו שימו כבוד תהלתו | 2 |
Ku rera ɗaukaka ga sunansa; ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!
אמרו לאלהים מה-נורא מעשיך ברב עזך יכחשו לך איביך | 3 |
Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke! Ikonka da girma yake har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.
כל-הארץ ישתחוו לך--ויזמרו-לך יזמרו שמך סלה | 4 |
Dukan duniya sun rusuna a gabanka suna rera yabo gare ka, suna rera yabo ga sunanka.” (Sela)
לכו וראו מפעלות אלהים נורא עלילה על-בני אדם | 5 |
Ku zo ku ga abin da Allah ya yi, ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum!
הפך ים ליבשה--בנהר יעברו ברגל שם נשמחה-בו | 6 |
Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa.
משל בגבורתו עולם-- עיניו בגוים תצפינה הסוררים אל-ירימו (ירומו) למו סלה | 7 |
Yana mulki har abada ta wurin ikonsa, idanunsa suna duban al’ummai, kada’yan tawaye su tayar masa. (Sela)
ברכו עמים אלהינו והשמיעו קול תהלתו | 8 |
Ku yabi Allahnku, ya mutane, bari a ji ƙarar yabonsa;
השם נפשנו בחיים ולא-נתן למוט רגלנו | 9 |
ya adana rayukanmu ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi.
כי-בחנתנו אלהים צרפתנו כצרף-כסף | 10 |
Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa.
הבאתנו במצודה שמת מועקה במתנינו | 11 |
Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.
הרכבת אנוש לראשנו באנו-באש ובמים ותוציאנו לרויה | 12 |
Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.
אבוא ביתך בעולות אשלם לך נדרי | 13 |
Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa zan kuwa cika alkawurana gare ka,
אשר-פצו שפתי ודבר-פי בצר-לי | 14 |
alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa sa’ad da nake cikin wahala.
עלות מיחים אעלה-לך עם-קטרת אילים אעשה בקר עם-עתודים סלה | 15 |
Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. (Sela)
לכו-שמעו ואספרה כל-יראי אלהים אשר עשה לנפשי | 16 |
Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah; bari in faɗa muku abin da ya yi mini.
אליו פי-קראתי ורומם תחת לשוני | 17 |
Na yi kuka gare shi da bakina; yabonsa yana a harshena.
און אם-ראיתי בלבי-- לא ישמע אדני | 18 |
Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba;
אכן שמע אלהים הקשיב בקול תפלתי | 19 |
amma tabbatacce Allah ya saurara ya kuma ji muryata a cikin addu’a.
ברוך אלהים-- אשר לא-הסיר תפלתי וחסדו מאתי | 20 |
Yabo ga Allah, wanda bai ƙi addu’ata ba ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni!