< תהילים 55 >

למנצח בנגינת משכיל לדוד ב האזינה אלהים תפלתי ואל-תתעלם מתחנתי 1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Ka ji addu’ata, ya Allah, kada ka ƙyale roƙona;
הקשיבה לי וענני אריד בשיחי ואהימה 2
ka ji ni ka kuma amsa mini. Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis
מקול אויב--מפני עקת רשע כי-ימיטו עלי און ובאף ישטמוני 3
hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina, saboda danniyar mugaye. Gama sukan jawo mini wahala, suna jin haushina suna ƙina.
לבי יחיל בקרבי ואימות מות נפלו עלי 4
Zuciyata tana wahala a cikina; tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina.
יראה ורעד יבא בי ותכסני פלצות 5
Tsoro da rawan jiki sun kama ni; razana ta sha kaina.
ואמר--מי-יתן-לי אבר כיונה אעופה ואשכנה 6
Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana! Ai, da na yi firiya na tafi na huta,
הנה ארחיק נדד אלין במדבר סלה 7
da na tafi can da nisa na zauna a hamada; (Sela)
אחישה מפלט לי-- מרוח סעה מסער 8
da na hanzarta na tafi wurin mafakata, nesa da muguwar iska da hadiri.”
בלע אדני פלג לשונם כי-ראיתי חמס וריב בעיר 9
Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu, gama na ga rikici da faɗa a cikin birni.
יומם ולילה--יסובבה על-חומתיה ואון ועמל בקרבה 10
Dare da rana suna yawo a kan katanga; mugun hali da zargi suna a cikinta.
הוות בקרבה ולא-ימיש מרחבה תך ומרמה 11
Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni; barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta.
כי לא-אויב יחרפני ואשא לא-משנאי עלי הגדיל ואסתר ממנו 12
Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi.
ואתה אנוש כערכי אלופי ומידעי 13
Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa,
אשר יחדו נמתיק סוד בבית אלהים נהלך ברגש 14
wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah.
ישימות (ישי מות) עלימו--ירדו שאול חיים כי-רעות במגורם בקרבם (Sheol h7585) 15
Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu. (Sheol h7585)
אני אל-אלהים אקרא ויהוה יושיעני 16
Amma na kira ga Allah, Ubangiji kuwa ya cece ni.
ערב ובקר וצהרים אשיחה ואהמה וישמע קולי 17
Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata.
פדה בשלום נפשי מקרב-לי כי-ברבים היו עמדי 18
Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni.
ישמע אל ויענם-- וישב קדם סלה אשר אין חליפות למו ולא יראו אלהים 19
Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, (Sela) mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah.
שלח ידיו בשלמיו חלל בריתו 20
Abokina ya kai wa abokansa hari; ya tā da alkawarinsa.
חלקו מחמאת פיו-- וקרב-לבו רכו דבריו משמן והמה פתחות 21
Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun, duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa; kalmominsa sun fi mai sulɓi, duk da haka takuba ne zārarru.
השלך על-יהוה יהבך-- והוא יכלכלך לא-יתן לעולם מוט-- לצדיק 22
Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.
ואתה אלהים תורדם לבאר שחת-- אנשי דמים ומרמה לא-יחצו ימיהם ואני אבטח-בך 23
Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye zuwa cikin ramin lalacewa; masu kisa da mutane masu ruɗu ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba. Amma ni dai, na dogara gare ka.

< תהילים 55 >