< תהילים 49 >

למנצח לבני-קרח מזמור ב שמעו-זאת כל-העמים האזינו כל-ישבי חלד 1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku ji wannan, dukanku mutane; ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya,
גם-בני אדם גם-בני-איש-- יחד עשיר ואביון 2
babba da yaro mai arziki da talaka.
פי ידבר חכמות והגות לבי תבונות 3
Bakina zai yi maganar hikima; magana daga zuciyata za tă ba da ganewa.
אטה למשל אזני אפתח בכנור חידתי 4
Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina.
למה אירא בימי רע-- עון עקבי יסובני 5
Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni,
הבטחים על-חילם וברב עשרם יתהללו 6
waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu?
אח--לא פדה יפדה איש לא-יתן לאלהים כפרו 7
Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,
ויקר פדיון נפשם וחדל לעולם 8
kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa,
ויחי-עוד לנצח לא יראה השחת 9
da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.
כי יראה חכמים ימותו-- יחד כסיל ובער יאבדו ועזבו לאחרים חילם 10
Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.
קרבם בתימו לעולם-- משכנתם לדור ודר קראו בשמותם עלי אדמות 11
Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
ואדם ביקר בל-ילין נמשל כבהמות נדמו 12
Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
זה דרכם כסל למו ואחריהם בפיהם ירצו סלה 13
Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. (Sela)
כצאן לשאול שתו-- מות ירעם וירדו בם ישרים לבקר--וצירם (וצורם) לבלות שאול מזבל לו (Sheol h7585) 14
Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada. (Sheol h7585)
אך-אלהים--יפדה נפשי מיד-שאול כי יקחני סלה (Sheol h7585) 15
Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. (Sela) (Sheol h7585)
אל-תירא כי-יעשר איש כי-ירבה כבוד ביתו 16
Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;
כי לא במותו יקח הכל לא-ירד אחריו כבודו 17
gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.
כי-נפשו בחייו יברך ויודך כי-תיטיב לך 18
Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,
תבוא עד-דור אבותיו עד-נצח לא יראו-אור 19
zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
אדם ביקר ולא יבין נמשל כבהמות נדמו 20
Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.

< תהילים 49 >