< תהילים 16 >
מכתם לדוד שמרני אל כי-חסיתי בך | 1 |
Miktam ne na Dawuda. Ka kiyaye ni, ya Allah, gama a cikinka nake samun mafaka.
אמרת ליהוה אדני אתה טובתי בל-עליך | 2 |
Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana; in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”
לקדושים אשר-בארץ המה ואדירי כל-חפצי-בם | 3 |
Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa, su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana.
ירבו עצבותם אחר מהרו בל-אסיך נסכיהם מדם ובל-אשא את-שמותם על-שפתי | 4 |
Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli. Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba ko in ambaci sunayensu da bakina.
יהוה מנת-חלקי וכוסי-- אתה תומיך גורלי | 5 |
Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na; ka kiyaye rabona,
חבלים נפלו-לי בנעמים אף-נחלת שפרה עלי | 6 |
Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi; tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.
אברך--את-יהוה אשר יעצני אף-לילות יסרוני כליותי | 7 |
Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara; ko da dare ma zuciyata kan koya mini.
שויתי יהוה לנגדי תמיד כי מימיני בל-אמוט | 8 |
Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.
לכן שמח לבי--ויגל כבודי אף-בשרי ישכן לבטח | 9 |
Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya,
כי לא-תעזב נפשי לשאול לא-תתן חסידך לראות שחת (Sheol ) | 10 |
domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. (Sheol )
תודיעני ארח חיים שבע שמחות את-פניך נעמות בימינך נצח | 11 |
Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.