< תהילים 133 >
שיר המעלות לדוד הנה מה-טוב ומה-נעים-- שבת אחים גם-יחד | 1 |
Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma sa’ad da’yan’uwa suna zaman lafiya!
כשמן הטוב על-הראש-- ירד על-הזקן זקן-אהרן שירד על-פי מדותיו | 2 |
Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai, yana gangarawa a gemu, yana gangarawa a gemun Haruna, har zuwa wuyan rigunansa.
כטל-חרמון-- שירד על-הררי ציון כי שם צוה יהוה את-הברכה-- חיים עד-העולם | 3 |
Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.