< תהילים 128 >
שיר המעלות אשרי כל-ירא יהוה-- ההלך בדרכיו | 1 |
Waƙar haurawa. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
יגיע כפיך כי תאכל אשריך וטוב לך | 2 |
Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.
אשתך כגפן פריה-- בירכתי ביתך בניך כשתלי זיתים-- סביב לשלחנך | 3 |
Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai’ya’ya a cikin gidanka;’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.
הנה כי-כן יברך גבר-- ירא יהוה | 4 |
Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.
יברכך יהוה מציון וראה בטוב ירושלם--כל ימי חייך | 5 |
Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,
וראה-בנים לבניך שלום על-ישראל | 6 |
bari kuma ka rayu ka ga’ya’ya’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.