< תהילים 12 >
למנצח על-השמינית מזמור לדוד ב הושיעה יהוה כי-גמר חסיד כי-פסו אמונים מבני אדם | 1 |
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda. Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.
שוא ידברו--איש את-רעהו שפת חלקות--בלב ולב ידברו | 2 |
Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu.
יכרת יהוה כל-שפתי חלקות-- לשון מדברת גדלות | 3 |
Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,
אשר אמרו ללשננו נגביר--שפתינו אתנו מי אדון לנו | 4 |
masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”
משד עניים מאנקת אביונים עתה אקום יאמר יהוה אשית בישע יפיח לו | 5 |
“Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”
אמרות יהוה אמרות טהרות כסף צרוף בעליל לארץ מזקק שבעתים | 6 |
Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai.
אתה-יהוה תשמרם תצרנו מן-הדור זו לעולם | 7 |
Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.
סביב רשעים יתהלכון כרם זלות לבני אדם | 8 |
Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.