< תהילים 10 >
למה יהוה תעמד ברחוק תעלים לעתות בצרה | 1 |
Don me, ya Ubangiji, kake tsaya can da nesa? Me ya sa kake ɓoye kanka a lokutan wahala?
בגאות רשע ידלק עני יתפשו במזמות זו חשבו | 2 |
Cikin fariyarsa mugun mutum yakan cuci marasa ƙarfi, waɗanda yake kama cikin makircin da ya shirya.
כי-הלל רשע על-תאות נפשו ובצע ברך נאץ יהוה | 3 |
Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa; yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji.
רשע--כגבה אפו בל-ידרש אין אלהים כל-מזמותיו | 4 |
Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah; cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah.
יחילו דרכו בכל-עת--מרום משפטיך מנגדו כל-צורריו יפיח בהם | 5 |
Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara; yana da girman kai kuma dokokinka suna nesa da shi; yakan yi wa dukan abokan gābansa duban reni.
אמר בלבו בל-אמוט לדר ודר אשר לא-ברע | 6 |
Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni; kullum zan yi murna ba zan taɓa shiga wahala ba.”
אלה פיהו מלא--ומרמות ותך תחת לשונו עמל ואון | 7 |
Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana; wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.
ישב במארב חצרים--במסתרים יהרג נקי עיניו לחלכה יצפנו | 8 |
Yakan yi kwanto kusa da ƙauyuka; daga kwanton yakan kashe marar laifi. Yana kallon waɗanda za su shiga hannunsa a ɓoye.
יארב במסתר כאריה בסכה-- יארב לחטוף עני יחטף עני במשכו ברשתו | 9 |
Yakan yi kwanto a ɓoye kamar zaki. Yakan yi kwanto don yă kama marasa ƙarfi; yakan kama marasa ƙarfi yă ja su cikin ragarsa.
ודכה (ידכה) ישח ונפל בעצומיו חלכאים (חל כאים) | 10 |
Yakan ragargaza waɗanda suka shiga hannu, su fāɗi; sukan fāɗi a ƙarƙashin ƙarfinsa.
אמר בלבו שכח אל הסתיר פניו בל-ראה לנצח | 11 |
Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta; ya rufe fuskarsa ba ya gani.”
קומה יהוה--אל נשא ידך אל-תשכח עניים (ענוים) | 12 |
Ka tashi, Ubangiji! Ka hukunta miyagu, ya Allah. Kada ka manta da marasa ƙarfi.
על-מה נאץ רשע אלהים אמר בלבו לא תדרש | 13 |
Don me mugun mutum zai ƙi Allah? Don me yakan ce wa kansa, “Allah ba zai nemi hakki daga gare ni ba”?
ראתה כי-אתה עמל וכעס תביט-- לתת בידך עליך יעזב חלכה יתום אתה היית עוזר | 14 |
Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki; kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu. Marar taimako kan danƙa kansa gare ka; kai ne mai taimakon marayu
שבר זרוע רשע ורע תדרוש-רשעו בל-תמצא | 15 |
Ka karye hannun mugaye da kuma mugun mutum; ka nemi hakki daga gare shi saboda muguntar da ba za a gane ba.
יהוה מלך עולם ועד אבדו גוים מארצו | 16 |
Ubangiji Sarkin har abada abadin ne; al’ummai za su hallaka daga ƙasarsa.
תאות ענוים שמעת יהוה תכין לבם תקשיב אזנך | 17 |
Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala; kakan ƙarfafa su, ka kuma saurari kukansu,
לשפט יתום ודך בל-יוסיף עוד--לערץ אנוש מן-הארץ | 18 |
kana kāre marayu da waɗanda aka danne, domin mutum, wanda yake na duniya kada ƙara haddasa wata razana.