< נחום 2 >
עלה מפיץ על פניך נצור מצורה צפה דרך חזק מתנים אמץ כח מאד | 1 |
Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe. Ki tsare mafaka, ki yi gadin hanya ki sha ɗamara ki tattaro dukan ƙarfinki!
כי שב יהוה את גאון יעקב כגאון ישראל כי בקקום בקקים וזמריהם שחתו | 2 |
Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub, kamar ta Isra’ila, ko da yake masu washewa sun washe su suka kuma lalatar da inabinsu.
מגן גבריהו מאדם אנשי חיל מתלעים באש פלדת הרכב ביום הכינו והברשים הרעלו | 3 |
Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro.
בחוצות יתהוללו הרכב ישתקשקון ברחבות מראיהן כלפידים--כברקים ירוצצו | 4 |
Kekunan yaƙi sun zabura a tituna, suna kai da kawowa a dandali. Suna walƙiya kamar tocila suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.
יזכר אדיריו--יכשלו בהלכותם (בהליכתם) ימהרו חומתה והכן הסכך | 5 |
Ninebe ta tattara rundunarta, duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu. Sun ruga zuwa katangan birnin, sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata.
שערי הנהרות נפתחו וההיכל נמוג | 6 |
An buɗe ƙofofin rafuffukan sai wurin ya rurrushe.
והצב גלתה העלתה ואמהתיה מנהגות כקול יונים מתפפת על לבבהן | 7 |
An umarta cewa birnin za tă tafi bauta, za a kuma yi gaba da su. Bayi’yan mata suna kuka kamar tattabaru suna buga ƙirjinsu.
ונינוה כברכת מים מימי היא והמה נסים עמדו עמדו ואין מפנה | 8 |
Ninebe tana kama da tafki, wanda ruwanta yana yoyo. Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,” amma ba wanda ya waiga.
בזו כסף בזו זהב ואין קצה לתכונה--כבד מכל כלי חמדה | 9 |
A washe azurfa; a washe zinariya; dukiyarsu ba ta da iyaka, arzikinsu kuma ba ya ƙarewa.
בוקה ומבוקה ומבלקה ולב נמס ופק ברכים וחלחלה בכל מתנים ופני כלם קבצו פארור | 10 |
Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa, jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare!
איה מעון אריות ומרעה הוא לכפרים--אשר הלך אריה לביא שם גור אריה ואין מחריד | 11 |
Ina kogon zakokin nan yake yanzu, inda suka ciyar da’ya’yansu, inda zaki da zakanya sukan shiga, da’ya’yansu, ba mai damunsu
אריה טרף בדי גרותיו ומחנק ללבאתיו וימלא טרף חריו ומענתיו טרפה | 12 |
Zaki ya kashe abin da ya ishe’ya’yansa ya kuma murɗe wuyan dabbobi ya cika wurin zamansa da abin da ya kama ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.
הנני אליך נאם יהוה צבאות והבערתי בעשן רכבה וכפיריך תאכל חרב והכרתי מארץ טרפך ולא ישמע עוד קול מלאככה | 13 |
“Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ƙone kekunan yaƙinki, takobi kuma zai fafare’ya’yan zakokinki. Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba. Ba kuwa za a ƙara jin muryar’yan saƙonki ba.”