< מיכה 1 >

דבר יהוה אשר היה אל מיכה המרשתי בימי יותם אחז יחזקיה מלכי יהודה--אשר חזה על שמרון וירושלם 1
Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.
שמעו עמים כלם הקשיבי ארץ ומלאה ויהי אדני יהוה בכם לעד אדני מהיכל קדשו 2
Ku ji, ya ku mutane duka, ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki, bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku, daga haikalinsa mai tsarki.
כי הנה יהוה יצא ממקומו וירד ודרך על במותי (במתי) ארץ 3
Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa; zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya.
ונמסו ההרים תחתיו והעמקים יתבקעו כדונג מפני האש כמים מגרים במורד 4
Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa, kamar kaki a gaban wuta, kwaruruka kuma za su ɓace, kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.
בפשע יעקב כל זאת ובחטאות בית ישראל מי פשע יעקב הלוא שמרון ומי במות יהודה הלוא ירושלם 5
Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub, da kuma zunuban gidan Isra’ila ne. Mene ne laifin Yaƙub? Shin, ba Samariya ba ce? Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda? Shin, ba Urushalima ba ce?
ושמתי שמרון לעי השדה למטעי כרם והגרתי לגי אבניה ויסדיה אגלה 6
“Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji, wurin noman inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari in kuma bar harsashin gininta a bayyane.
וכל פסיליה יכתו וכל אתנניה ישרפו באש וכל עצביה אשים שממה כי מאתנן זונה קבצה ועד אתנן זונה ישובו 7
Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.”
על זאת אספדה ואילילה אילכה שילל (שולל) וערום אעשה מספד כתנים ואבל כבנות יענה 8
Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka; zan yi tafiya ba takalmi, zan tuɓe, in kuma yi tafiya tsirara. Zan yi kuka kamar dila, in yi baƙin ciki kamar mujiya.
כי אנושה מכותיה כי באה עד יהודה--נגע עד שער עמי עד ירושלם 9
Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne; ya bazu har Yahuda. Ya ma kai bakin ƙofar mutanena, har ma Urushalima da kanta.
בגת אל תגידו--בכו אל תבכו בבית לעפרה עפר התפלשתי (התפלשי) 10
Kada a faɗe shi a Gat; kada ma a yi kuka. A maimako haka, a yi birgima a cikin ƙura a Bet-Leyafra.
עברי לכם יושבת שפיר עריה בשת לא יצאה יושבת צאנן--מספד בית האצל יקח מכם עמדתו 11
Ku wuce tsirara da kuma kunya, ku mazaunan Shafir. Bet-Ezel tana makoki domin babu wani daga Za’anan da ya fito don yă taimaka.
כי חלה לטוב יושבת מרות כי ירד רע מאת יהוה לשער ירושלם 12
Mazaunan Marot sun ƙosa su ga alheri, amma Ubangiji ya sauko da azaba, har zuwa ƙofar Urushalima.
רתם המרכבה לרכש יושבת לכיש ראשית חטאת היא לבת ציון כי בך נמצאו פשעי ישראל 13
Ku da kuke zama a Lakish, ku ɗaura wa dawakai kekunan yaƙi. Gama ku kuka fara yin zunubi a Sihiyona, gama an sami laifofin Isra’ila a cikinku.
לכן תתני שלוחים על מורשת גת בתי אכזיב לאכזב למלכי ישראל 14
Saboda haka za ku ba da kyautan bankwana ga Moreshet Gat. Garin Akzib zai zama abin yaudara ga sarakunan Isra’ila.
עד הירש אבי לך יושבת מרשה עד עדלם יבוא כבוד ישראל 15
Ku mazaunan Maresha Ubangiji zai kawo wanda zai ci ku da yaƙi. Sarakunan Isra’ila za su gudu zuwa Adullam.
קרחי וגזי על בני תענוגיך הרחבי קרחתך כנשר כי גלו ממך 16
Ku aske kanku ƙwal don makoki, ku yi wa kanku ƙwalƙwal kamar ungulu. Gama za a ja’ya’yan da kuke farin ciki a kai su bauta.

< מיכה 1 >