< שופטים 21 >
ואיש ישראל נשבע במצפה לאמר איש ממנו לא יתן בתו לבנימן לאשה | 1 |
Mutanen Isra’ila sun riga sun yi rantsuwa a Mizfa cewa, “Ba ɗayanmu da zai ba da’yarsa aure ga mutumin Benyamin.”
ויבא העם בית אל וישבו שם עד הערב לפני האלהים וישאו קולם ויבכו בכי גדול | 2 |
Sai mutanen suka tafi Betel, inda suka zauna a gaban Allah har yamma, suna tā da muryoyinsu suna kuka mai zafi.
ויאמרו--למה יהוה אלהי ישראל היתה זאת בישראל להפקד היום מישראל שבט אחד | 3 |
Suka ce, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, “Me ya sa wannan abu ya faru da Isra’ila? Don me kabila ɗaya daga Isra’ila za tă ɓace a yau?”
ויהי ממחרת וישכימו העם ויבנו שם מזבח ויעלו עלות ושלמים | 4 |
Kashegari da sassafe mutane suka gina bagade suka miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama.
ויאמרו בני ישראל מי אשר לא עלה בקהל מכל שבטי ישראל אל יהוה כי השבועה הגדולה היתה לאשר לא עלה אל יהוה המצפה לאמר--מות יומת | 5 |
Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji ba?” Gama an yi rantsuwa cewa duk wanda ya kāsa zuwa taro a gaban Ubangiji a Mizfa lalle a kashe shi.
וינחמו בני ישראל אל בנימן אחיו ויאמרו נגדע היום שבט אחד מישראל | 6 |
To, Isra’ilawa suka yi juyayin’yan’uwansu, mutanen Benyamin. “Yau an hallaka kabila daga cikin Isra’ila.
מה נעשה להם לנותרים לנשים ואנחנו נשבענו ביהוה לבלתי תת להם מבנותינו לנשים | 7 |
Yaya za mu ba wa waɗanda suka rage mata, da yake mun riga mun yi rantsuwa a gaban Ubangiji, ba za mu ba su ɗaya daga’ya’yanmu su aura ba?”
ויאמרו--מי אחד משבטי ישראל אשר לא עלה אל יהוה המצפה והנה לא בא איש אל המחנה מיביש גלעד--אל הקהל | 8 |
Sa’an nan suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji a Mizfa ba?” Sai su gane cewa babu wani daga Yabesh Gileyad da ya zo sansani don taron.
ויתפקד העם והנה אין שם איש מיושבי יבש גלעד | 9 |
Gama da aka yi ƙidaya mutane, sai aka gane cewa babu wani daga mutanen Yabesh Gileyad da yake a can.
וישלחו שם העדה שנים עשר אלף איש--מבני החיל ויצוו אותם לאמר לכו והכיתם את יושבי יבש גלעד לפי חרב והנשים והטף | 10 |
Saboda haka sai taron ya umarci jarumai dubu goma sha biyu su je Yabesh Gileyad su karkashe waɗanda suke zaune a can, duk da mata da yara.
וזה הדבר אשר תעשו כל זכר וכל אשה ידעת משכב זכר--תחרימו | 11 |
Suka ce musu, “Ga abin da za ku yi. Ku karkashe duk namiji da kowace macen da ta riga ta san namiji.”
וימצאו מיושבי יביש גלעד ארבע מאות נערה בתולה אשר לא ידעה איש למשכב זכר ויבאו אותם אל המחנה שלה אשר בארץ כנען | 12 |
Suka samu a cikin mutanen da suke zaune a Yabesh Gileyad mata ɗari huɗu da ba su taɓa kwana da namiji ba, suka kwashe su zuwa sansani a Shilo a Kan’ana.
וישלחו כל העדה וידברו אל בני בנימן אשר בסלע רמון ויקראו להם שלום | 13 |
Sa’an nan dukan taro suka aika wa mutanen Benyamin da suke a Dutsen Rimmon cewa yaƙi ya ƙare, yanzu sai salama.
וישב בנימן בעת ההיא ויתנו להם הנשים אשר חיו מנשי יבש גלעד ולא מצאו להם כן | 14 |
Saboda haka mutanen Benyamin suka komo a lokacin aka kuma ba su matan Yabesh Gileyad nan da aka bari da rai. Amma matan ba su ishe su duka ba.
והעם נחם לבנימן כי עשה יהוה פרץ בשבטי ישראל | 15 |
Mutanen kuwa suka yi juyayi saboda mutanen Benyamin, domin Ubangiji ya yi gibi a cikin kabilan Isra’ila.
ויאמרו זקני העדה מה נעשה לנותרים לנשים כי נשמדה מבנימן אשה | 16 |
Shugabannin taron suka ce, “Da matan Benyamin da aka hallaka, yaya za mu yi da mazan da suka ragu da ba su sami mata ba?”
ויאמרו ירשת פליטה לבנימן ולא ימחה שבט מישראל | 17 |
Suka ce, “Dole mutanen Benyamin da suka ragu su sami gādo, domin kada wata kabila a Isra’ila ta ɓace.
ואנחנו לא נוכל לתת להם נשים--מבנותינו כי נשבעו בני ישראל לאמר ארור נתן אשה לבנימן | 18 |
Ba za mu iya ba su’yan matanmu su zama matansu ba, da yake mu Isra’ilawa mun riga mun yi wannan rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne wanda ya ba da’yarsa aure ga mutum Benyamin.’
ויאמרו הנה חג יהוה בשלו מימים ימימה אשר מצפונה לבית אל מזרחה השמש למסלה העלה מבית אל שכמה--ומנגב ללבונה | 19 |
Sai suka tuna, akwai bikin Ubangiji da sukan yi shekara-shekara a Shilo ya yi kusa. Shilo yana arewancin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.”
ויצו (ויצוו) את בני בנימן לאמר לכו וארבתם בכרמים | 20 |
Saboda haka suka cewa mutanen Benyamin, “Ku je ku ɓuya a gonakin inabi
וראיתם והנה אם יצאו בנות שילו לחול במחלות ויצאתם מן הכרמים וחטפתם לכם איש אשתו מבנות שילו והלכתם ארץ בנימן | 21 |
ku lura. Sa’ad da’yan matan Shilo suka fito waje don su yi rawa, ku fito a guje daga gonakin inabi, kowannenku yă kama wa kansa mata daga cikin’yan matan Shilo, ku tafi ƙasar Benyamin.
והיה כי יבאו אבותם או אחיהם לרוב (לריב) אלינו ואמרנו אליהם חנונו אותם--כי לא לקחנו איש אשתו במלחמה כי לא אתם נתתם להם כעת תאשמו | 22 |
Sa’ad da iyayensu maza ko’yan’uwansu suka kawo mana ƙara, za mu ce musu, ‘Ku yi mana alheri ku bar su, domin ba mu samo musu mata ba lokacin yaƙi, ku kuma marasa laifi ne, tun da yake ba ku ba da’ya’yan matanku gare su ba.’”
ויעשו כן בני בנימן וישאו נשים למספרם מן המחללות אשר גזלו וילכו וישובו אל נחלתם ויבנו את הערים וישבו בהם | 23 |
Haka mutanen Benyamin suka yi. Yayinda’yan matan suke rawa, kowane mutum ya kama ɗaya ya yi gaba da ita ta zama matarsa. Sa’an nan suka komo ƙasar gādonsu suka sāke giggina garuruwan suka kuwa zauna a cikinsu.
ויתהלכו משם בני ישראל בעת ההיא איש לשבטו ולמשפחתו ויצאו משם איש לנחלתו | 24 |
A lokacin, Isra’ilawa sun bar wurin suka tafi gida zuwa ga kabilansu da zuriyoyinsu, kowane zuwa gādonsa.
בימים ההם אין מלך בישראל איש הישר בעיניו יעשה | 25 |
A kwanakin Isra’ila ba ta da sarki; kowa ya yi abin da ya ga dama.