< שופטים 12 >
ויצעק איש אפרים ויעבר צפונה ויאמרו ליפתח מדוע עברת להלחם בבני עמון ולנו לא קראת ללכת עמך--ביתך נשרף עליך באש | 1 |
Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.”
ויאמר יפתח אליהם איש ריב הייתי אני ועמי ובני עמון מאד ואזעק אתכם ולא הושעתם אותי מידם | 2 |
Yefta ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya sosai da Ammonawa, ko da yake na kira ku, amma ba ku cece ni daga hannuwansu ba.
ואראה כי אינך מושיע ואשימה נפשי בכפי ואעברה אל בני עמון ויתנם יהוה בידי ולמה עליתם אלי היום הזה--להלחם בי | 3 |
Da na ga ba za ku taimake ni ba, sai na yi kasai da raina na kuwa haye don in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba ni nasara a kansu. To, don me kuka zo yau don ku yaƙe ni?”
ויקבץ יפתח את כל אנשי גלעד וילחם את אפרים ויכו אנשי גלעד את אפרים כי אמרו פליטי אפרים אתם--גלעד בתוך אפרים בתוך מנשה | 4 |
Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.”
וילכד גלעד את מעברות הירדן לאפרים והיה כי יאמרו פליטי אפרים אעברה ויאמרו לו אנשי גלעד האפרתי אתה ויאמר לא | 5 |
Mutanen Gileyad suka ƙwace mashigan Urdun masu zuwa Efraim, duk sa’ad da wani daga Efraim da ya tsira ya ce, “Bari in haye,” sai mutane Gileyad su ce “Kai mutumin Efraim ne?” In ya ce, “A’a,”
ויאמרו לו אמר נא שבלת ויאמר סבלת ולא יכין לדבר כן ויאחזו אותו וישחטוהו אל מעברות הירדן ויפל בעת ההיא מאפרים ארבעים ושנים אלף | 6 |
sai su ce, “To, ka ce, ‘Shibbolet.’” In ya ce, “Sibbolet,” saboda ba sa iya faɗin kalmar daidai, sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Aka kashe mutanen Efraim dubu arba’in da biyu a ta haka.
וישפט יפתח את ישראל שש שנים וימת יפתח הגלעדי ויקבר בערי גלעד | 7 |
Yefta ya shugabanci Isra’ila shekara shida. Sa’an nan Yefta mutumin Gileyad ya mutu, aka kuwa binne shi wani gari a Gileyad.
וישפט אחריו את ישראל אבצן מבית לחם | 8 |
Bayansa, Ibzan mutumin Betlehem, ya shugabanci Isra’ila.
ויהי לו שלשים בנים ושלשים בנות שלח החוצה ושלשים בנות הביא לבניו מן החוץ וישפט את ישראל שבע שנים | 9 |
Yana’ya’ya maza talatin da’ya’ya mata talatin. Ya ba da auren’ya’yansa mata ga waɗanda ba daga dangi ba, ga’ya’yansa maza kuwa ya kawo’yan mata talatin su zama matansu waje da danginsa. Ibzan ya shugabanci Isra’ila shekara bakwai.
וימת אבצן ויקבר בבית לחם | 10 |
Sa’an nan Ibzan ya mutu, aka kuwa binne shi Betlehem.
וישפט אחריו את ישראל אילון הזבולני וישפט את ישראל עשר שנים | 11 |
Bayansa, Elon mutumin Zebulun, ya shugabanci Isra’ila shekara goma.
וימת אילון הזבולני ויקבר באילון בארץ זבולן | 12 |
Sa’an nan Elon ya mutu, aka kuwa binne shi a Aiyalon a ƙasar Zebulun.
וישפט אחריו את ישראל עבדון בן הלל הפרעתוני | 13 |
Bayansa, Abdon ɗan Hillel, daga Firaton, ya shugabanci Isra’ila.
ויהי לו ארבעים בנים ושלשים בני בנים רכבים על שבעים עירם וישפט את ישראל שמנה שנים | 14 |
Yana da’ya’ya maza arba’in da’yan taɓa kunne talatin, waɗanda suka hau jakuna saba’in. Ya shugabanci Isra’ila shekara takwas.
וימת עבדון בן הלל הפרעתוני ויקבר בפרעתון בארץ אפרים בהר העמלקי | 15 |
Sa’an nan Abdon ɗan Hillel ya mutu, aka kuwa binne shi a Firaton a Efraim, a ƙasar tudu ta Amalekawa.