< איוב 1 >
איש היה בארץ עוץ איוב שמו והיה האיש ההוא תם וישר וירא אלהים--וסר מרע | 1 |
A ƙasar Uz akwai wani mutum mai suna Ayuba. Mutum ne marar laifi kuma mai adalci; yana tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.
ויולדו לו שבעה בנים ושלוש בנות | 2 |
Yana da’ya’ya maza bakwai da’yan mata uku,
ויהי מקנהו שבעת אלפי צאן ושלשת אלפי גמלים וחמש מאות צמד בקר וחמש מאות אתונות ועבדה רבה מאד ויהי האיש ההוא גדול מכל בני קדם | 3 |
yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa.
והלכו בניו ועשו משתה בית איש יומו ושלחו וקראו לשלשת אחיתיהם לאכל ולשתות עמהם | 4 |
’Ya’yansa maza sukan yi biki a gidajensu, wannan yă yi yă ba wancan, sai su kira’yan’uwansu mata ukun su ci, su sha tare.
ויהי כי הקיפו ימי המשתה וישלח איוב ויקדשם והשכים בבקר והעלה עלות מספר כלם--כי אמר איוב אולי חטאו בני וברכו אלהים בלבבם ככה יעשה איוב כל הימים | 5 |
Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi.
ויהי היום--ויבאו בני האלהים להתיצב על יהוה ויבוא גם השטן בתוכם | 6 |
Wata rana mala’iku suka kawo kansu gaban Ubangiji, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su.
ויאמר יהוה אל השטן מאין תבא ויען השטן את יהוה ויאמר משוט בארץ ומהתהלך בה | 7 |
Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”
ויאמר יהוה אל השטן השמת לבך על עבדי איוב כי אין כמהו בארץ איש תם וישר ירא אלהים וסר מרע | 8 |
Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.”
ויען השטן את יהוה ויאמר החנם ירא איוב אלהים | 9 |
Sai Shaiɗan ya amsa ya ce, “Haka kawai Ayuba yake tsoron Allah?
הלא את (אתה) שכת בעדו ובעד ביתו ובעד כל אשר לו--מסביב מעשה ידיו ברכת ומקנהו פרץ בארץ | 10 |
Ba ka kāre shi da iyalinsa gaba ɗaya da duk mallakarsa ba? Ka Albarkaci ayyukan hannunsa yadda dabbobinsa duk sun cika ko’ina.
ואולם שלח נא ידך וגע בכל אשר לו--אם לא על פניך יברכך | 11 |
Ka ɗan miƙa hannunka ka raba shi da duk abin da yake da shi, ba shakka zai la’anta ka kana ji, kana gani.”
ויאמר יהוה אל השטן הנה כל אשר לו בידך--רק אליו אל תשלח ידך ויצא השטן מעם פני יהוה | 12 |
Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.” Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji.
ויהי היום ובניו ובנתיו אכלים ושתים יין בבית אחיהם הבכור | 13 |
Wata rana lokacin da’ya’yan Ayuba suke cikin biki a gidan babban ɗansa,
ומלאך בא אל איוב ויאמר הבקר היו חרשות והאתנות רעות על ידיהם | 14 |
sai ɗan aika ya zo wurin Ayuba ya ce masa, “Shanu suna huɗa, jakuna kuma suna kiwo nan kusa,
ותפל שבא ותקחם ואת הנערים הכו לפי חרב ואמלטה רק אני לבדי להגיד לך | 15 |
sai Sabenawa suka auka musu suka kwashe su suka tafi, suka karkashe masu yi maka aiki duka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
עוד זה מדבר וזה בא ויאמר אש אלהים נפלה מן השמים ותבער בצאן ובנערים ותאכלם ואמלטה רק אני לבדי להגיד לך | 16 |
Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Wutar Allah ta sauko daga sama ta ƙona dukan tumaki da masu lura da su, wato, bayinka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
עוד זה מדבר וזה בא ויאמר כשדים שמו שלשה ראשים ויפשטו על הגמלים ויקחום ואת הנערים הכו לפי חרב ואמלטה רק אני לבדי להגיד לך | 17 |
Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa sun auka wa raƙumanka sun kwashe su duka, suka kuma karkashe masu yi maka aiki, ni kaɗai ne na tsira na zo in gaya maka!”
עד זה מדבר וזה בא ויאמר בניך ובנותיך אכלים ושתים יין בבית אחיהם הבכור | 18 |
Yana cikin magana, sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “’Ya’yanka maza da mata suna biki, suna ci suna sha a gidan babban ɗanka,
והנה רוח גדולה באה מעבר המדבר ויגע בארבע פנות הבית ויפל על הנערים וימותו ואמלטה רק אני לבדי להגיד לך | 19 |
sai wata iska mai ƙarfi daga hamada ta auka ta rushe gidan, gidan kuwa ya fāɗi a kan’ya’yanka ya kashe su, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
ויקם איוב ויקרע את מעלו ויגז את ראשו ויפל ארצה וישתחו | 20 |
Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada
ויאמר ערם יצתי מבטן אמי וערם אשוב שמה--יהוה נתן ויהוה לקח יהי שם יהוה מברך | 21 |
ya ce, “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata, tsirara kuma zan koma. Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa; yabo ya tabbata ga Ubangiji.”
בכל זאת לא חטא איוב ולא נתן תפלה לאלהים | 22 |
Cikin wannan duka Ayuba bai yi wa Allah zunubi ta wurin ba shi laifi ba.