< ירמיה 45 >
הדבר אשר דבר ירמיהו הנביא אל ברוך בן נריה--בכתבו את הדברים האלה על ספר מפי ירמיהו בשנה הרבעית ליהויקים בן יאשיהו מלך יהודה לאמר | 1 |
Ga abin da Irmiya annabi ya faɗa wa Baruk ɗan Neriya a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, bayan Baruk ya rubuta maganar da Irmiya ya shibta masa a kan littafi cewa,
כה אמר יהוה אלהי ישראל עליך ברוך | 2 |
“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana ce maka, Baruk.
אמרת אוי נא לי כי יסף יהוה יגון על מכאבי יגעתי באנחתי ומנוחה לא מצאתי | 3 |
Ka ce, ‘Kaitona! Ubangiji ya ƙara baƙin ciki da wahalata; na gaji da nishe-nishe ban kuma huta ba.’”
כה תאמר אליו כה אמר יהוה הנה אשר בניתי אני הרס ואת אשר נטעתי אני נתש ואת כל הארץ היא | 4 |
Ubangiji ya ce, “Ka faɗa masa wannan, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan rushe abin da na gina in kuma tumɓuke abin da na dasa, a duk fāɗin ƙasar.
ואתה תבקש לך גדלות אל תבקש כי הנני מביא רעה על כל בשר נאם יהוה ונתתי לך את נפשך לשלל על כל המקמות אשר תלך שם | 5 |
Ya kamata ka nemi manyan abubuwa wa kanka? Kada ka neme su. Gama zan aukar da masifa a kan dukan mutane, in ji Ubangiji, amma duk inda ka tafi zan bar ka ka kuɓutar da ranka.’”