< ירמיה 33 >
ויהי דבר יהוה אל ירמיהו שנית והוא עודנו עצור בחצר המטרה לאמר | 1 |
Yayinda Irmiya yana a tsare a sansanin matsara, sai maganar Ubangiji ta zo masa sau na biyu cewa,
כה אמר יהוה עשה יהוה יוצר אותה להכינה--יהוה שמו | 2 |
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci duniya, Ubangiji wanda ya siffanta ta ya kuma kafa ta, Ubangiji ne sunansa.
קרא אלי ואענך ואגידה לך גדלות ובצרות לא ידעתם | 3 |
‘Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.’
כי כה אמר יהוה אלהי ישראל על בתי העיר הזאת ועל בתי מלכי יהודה--הנתצים אל הסללות ואל החרב | 4 |
Gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa game da gidaje a wannan birni da fadodin Yahuda da aka rurrushe domin a yi amfani da su a kan mahaurai da kuma takobi
באים להלחם את הכשדים ולמלאם את פגרי האדם אשר הכיתי באפי ובחמתי ואשר הסתרתי פני מהעיר הזאת על כל רעתם | 5 |
a yaƙi da Babiloniyawa. ‘Za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata. Zan ɓoye fuskata wa wannan birni saboda dukan muguntarsu.
הנני מעלה לה ארכה ומרפא ורפאתים וגליתי להם עתרת שלום ואמת | 6 |
“‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya.
והשבתי את שבות יהודה ואת שבות ישראל ובנתים כבראשנה | 7 |
Zan komo da Yahuda da Isra’ila daga bauta zan kuma sāke gina su kamar yadda suke a dā.
וטהרתים מכל עונם אשר חטאו לי וסלחתי לכול (לכל) עונותיהם אשר חטאו לי ואשר פשעו בי | 8 |
Zan tsarkake su daga dukan zunubin da suka yi mini zan kuma gafarta musu dukan zunubansu na yin mini tawaye.
והיתה לי לשם ששון לתהלה ולתפארת לכל גויי הארץ--אשר ישמעו את כל הטובה אשר אנכי עשה אותם ופחדו ורגזו על כל הטובה ועל כל השלום אשר אנכי עשה לה | 9 |
Sa’an nan birnin nan za tă sa in zama sananne, farin ciki, yabo da girma a gaban dukan al’ummai a duniya da suka ji abubuwa masu kyau da na yi mata; za su kuma yi mamaki su kuma yi rawan jiki saboda yalwar wadata da salamar da na ba ta.’
כה אמר יהוה עוד ישמע במקום הזה אשר אתם אמרים חרב הוא מאין אדם ומאין בהמה--בערי יהודה ובחצות ירושלם הנשמות מאין אדם ומאין יושב ומאין בהמה | 10 |
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Kuna cewa game da wannan wuri, “Kango ne, babu mutane ko dabbobi.” Duk da haka a cikin garuruwan Yahuda da titunan Urushalima da aka yashe, inda ba mutane ko dabbobi, za a sāke jin
קול ששון וקול שמחה קול חתן וקול כלה קול אמרים הודו את יהוה צבאות כי טוב יהוה כי לעולם חסדו מבאים תודה בית יהוה כי אשיב את שבות הארץ כבראשנה אמר יהוה | 11 |
sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “‘“Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.
כה אמר יהוה צבאות עוד יהיה במקום הזה החרב מאין אדם ועד בהמה ובכל עריו--נוה רעים מרבצים צאן | 12 |
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘A wannan wuri, kango da babu mutane ko dabbobi, cikin dukan garuruwansa za a sāke kasance da wurin kiwo don makiyaya su hutar da garkunansu.
בערי ההר בערי השפלה ובערי הנגב ובארץ בנימן ובסביבי ירושלם ובערי יהודה--עד תעברנה הצאן על ידי מונה אמר יהוה | 13 |
A cikin garuruwan ƙasar tudu, garuruwan yammancin gindin dutse da na Negeb, a yankin Benyamin, a cikin ƙauyuka kewayen Urushalima da kuma a cikin garuruwan Yahuda, garkuna za su sāke bi a ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,’ in ji Ubangiji.
הנה ימים באים נאם יהוה והקמתי את הדבר הטוב אשר דברתי אל בית ישראל ועל בית יהודה | 14 |
“‘Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan cika alkawarin alheri da na yi wa gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.
בימים ההם ובעת ההיא אצמיח לדוד צמח צדקה ועשה משפט וצדקה בארץ | 15 |
“‘A waɗannan kwanaki da kuma a wannan lokaci zan tā da Reshe mai adalci daga zuriyar Dawuda; zai yi abin da yake daidai da kuma gaskiya a ƙasar.
בימים ההם תושע יהודה וירושלם תשכון לבטח וזה אשר יקרא לה יהוה צדקנו | 16 |
A kwanakin nan zan ceci Yahuda Urushalima kuma za tă zauna lafiya. Sunan da za a kira ta shi ne, Ubangiji Adalcinmu.’
כי כה אמר יהוה לא יכרת לדוד--איש ישב על כסא בית ישראל | 17 |
Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra’ila ba,
ולכהנים הלוים לא יכרת איש מלפני מעלה עולה ומקטיר מנחה ועשה זבח--כל הימים | 18 |
ba kuwa firistoci waɗanda suke Lawiyawa za su rasa mutumin da zai ci gaba da tsaya a gabana don miƙa hadayun ƙonawa, ya ƙona hadayun hatsi ya kuma miƙa sadakoki ba.’”
ויהי דבר יהוה אל ירמיהו לאמור | 19 |
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
כה אמר יהוה אם תפרו את בריתי היום ואת בריתי הלילה ולבלתי היות יומם ולילה בעתם | 20 |
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ka tā da alkawarina na rana da kuma alkawarina na dare, har dare da rana ba za su ƙara bayyana a ƙayyadaddun lokutansu ba,
גם בריתי תפר את דוד עבדי מהיות לו בן מלך על כסאו ואת הלוים הכהנים משרתי | 21 |
to, sai a tā da alkawarina da Dawuda bawana da alkawarina da Lawiyawan da suke firistoci masu hidima a gabana, Dawuda kuma ba zai ƙara kasance da zuriyar da za tă yi mulki.
אשר לא יספר צבא השמים ולא ימד חול הים--כן ארבה את זרע דוד עבדי ואת הלוים משרתי אתי | 22 |
Zan sa zuriyar Dawuda bawana da kuma Lawiyawan da suke hidima a gabana su yi yawa kamar taurarin sararin sama da kuma yashin bakin tekun da ba a iya ƙidaya.’”
ויהי דבר יהוה אל ירמיהו לאמר | 23 |
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
הלוא ראית מה העם הזה דברו לאמר שתי המשפחות אשר בחר יהוה בהם וימאסם ואת עמי ינאצון מהיות עוד גוי לפניהם | 24 |
“Ba ka lura ba cewa waɗannan mutane suna cewa, ‘Ubangiji ya ƙi masarautai biyu da ya zaɓa’? Saboda haka suka rena mutanena ba sa ƙara ɗaukansu a matsayin al’umma.
כה אמר יהוה אם לא בריתי יומם ולילה--חקות שמים וארץ לא שמתי | 25 |
Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ban kafa alkawarina game da rana da kuma game da dare ba in kuma gyara dokokin sama da duniya ba,
גם זרע יעקוב ודוד עבדי אמאס מקחת מזרעו משלים אל זרע אברהם ישחק ויעקב כי אשוב (אשיב) את שבותם ורחמתים | 26 |
to zan ƙi zuriyar Yaƙub da na Dawuda bawana ba zan kuma zaɓi ɗaya daga cikin’ya’yansa maza ya yi mulki a kan zuriyar Ibrahim, Ishaku da Yaƙub ba. Gama zan mayar da wadatarsu in kuma yi musu jinƙai.’”