< ישעה 7 >
ויהי בימי אחז בן יותם בן עזיהו מלך יהודה עלה רצין מלך ארם ופקח בן רמליהו מלך ישראל ירושלם למלחמה עליה ולא יכל להלחם עליה | 1 |
Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.
ויגד לבית דוד לאמר נחה ארם על אפרים וינע לבבו ולבב עמו כנוע עצי יער מפני רוח | 2 |
Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza.
ויאמר יהוה אל ישעיהו צא נא לקראת אחז אתה ושאר ישוב בנך אל קצה תעלת הברכה העליונה--אל מסלת שדה כובס | 3 |
Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki.
ואמרת אליו השמר והשקט אל תירא ולבבך אל ירך משני זנבות האודים העשנים האלה--בחרי אף רצין וארם ובן רמליהו | 4 |
Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.
יען כי יעץ עליך ארם--רעה אפרים ובן רמליהו לאמר | 5 |
Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa,
נעלה ביהודה ונקיצנה ונבקענה אלינו ונמליך מלך בתוכה את בן טבאל | 6 |
“Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.”
כה אמר אדני יהוה לא תקום ולא תהיה | 7 |
Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “‘Ba zai faru ba, ba zai auku ba,
כי ראש ארם דמשק וראש דמשק רצין ובעוד ששים וחמש שנה יחת אפרים מעם | 8 |
gama kan Aram shi ne Damaskus, kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin. Cikin shekaru sittin da biyar za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba.
וראש אפרים שמרון וראש שמרון בן רמליהו אם לא תאמינו כי לא תאמנו | 9 |
Kan Efraim shi ne Samariya, kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya. In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba, ba za ku dawwama ba.’”
ויוסף יהוה דבר אל אחז לאמר | 10 |
Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce,
שאל לך אות מעם יהוה אלהיך העמק שאלה או הגבה למעלה (Sheol ) | 11 |
“Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.” (Sheol )
ויאמר אחז לא אשאל ולא אנסה את יהוה | 12 |
Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.”
ויאמר שמעו נא בית דוד המעט מכם הלאות אנשים כי תלאו גם את אלהי | 13 |
Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure?
לכן יתן אדני הוא לכם--אות הנה העלמה הרה וילדת בן וקראת שמו עמנו אל | 14 |
Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel.
חמאה ודבש יאכל--לדעתו מאוס ברע ובחור בטוב | 15 |
In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.
כי בטרם ידע הנער מאס ברע--ובחר בטוב תעזב האדמה אשר אתה קץ מפני שני מלכיה | 16 |
Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango.
יביא יהוה עליך ועל עמך ועל בית אביך ימים אשר לא באו למיום סור אפרים מעל יהודה את מלך אשור | 17 |
Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.”
והיה ביום ההוא ישרק יהוה לזבוב אשר בקצה יארי מצרים ולדבורה--אשר בארץ אשור | 18 |
A wannan rana Ubangiji zai yi feɗuwa yă kira ƙudaje daga rafuffuka masu nisa na Masar da kuma ƙudan zuma daga ƙasar Assuriya.
ובאו ונחו כלם בנחלי הבתות ובנקיקי הסלעים ובכל הנעצוצים ובכל הנהללים | 19 |
Za su zo su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, a kan dukan ƙayayyuwa da dukan rammukan ruwa.
ביום ההוא יגלח אדני בתער השכירה בעברי נהר במלך אשור את הראש ושער הרגלים וגם את הזקן תספה | 20 |
A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi, sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku.
והיה ביום ההוא יחיה איש עגלת בקר ושתי צאן | 21 |
A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai.
והיה מרב עשות חלב--יאכל חמאה כי חמאה ודבש יאכל כל הנותר בקרב הארץ | 22 |
Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma.
והיה ביום ההוא--יהיה כל מקום אשר יהיה שם אלף גפן באלף כסף לשמיר ולשית יהיה | 23 |
A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can.
בחצים ובקשת יבוא שמה כי שמיר ושית תהיה כל הארץ | 24 |
Mutane za su je can da baka da kibiyoyi, gama ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne za su rufe ƙasar.
וכל ההרים אשר במעדר יעדרון--לא תבוא שמה יראת שמיר ושית והיה למשלח שור ולמרמס שה | 25 |
Game da dukan tuddai da dā ake nome da garemani kuwa, ba za ku ƙara je wurin ba saboda tsoron ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya; za su zama wuraren da ake kai shanu a sake su su yi ta yawo da kansu, tumaki kuma su yi ta gudu.