< ישעה 48 >
שמעו זאת בית יעקב הנקראים בשם ישראל וממי יהודה יצאו הנשבעים בשם יהוה ובאלהי ישראל יזכירו--לא באמת ולא בצדקה | 1 |
“Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub, waɗanda ake kira da sunan Isra’ila suka kuma fito daga zuriyar Yahuda, ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila, amma ba da gaskiya ko adalci ba,
כי מעיר הקדש נקראו ועל אלהי ישראל נסמכו יהוה צבאות שמו | 2 |
ku da kuke kiran kanku’yan ƙasar birni mai tsarki kuna kuma dogara ga Allah na Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,
הראשנות מאז הגדתי ומפי יצאו ואשמיעם פתאם עשיתי ותבאנה | 3 |
na nanata abubuwan da suka riga suka faru tuntuni, bakina ya yi shelar su na kuma sanar da su; sai nan da nan na aikata, suka kuma faru.
מדעתי כי קשה אתה וגיד ברזל ערפך ומצחך נחושה | 4 |
Gama na san yadda kuke da taurinkai; jijiyoyin wuyanku ƙarafa ne, goshinku tagulla ne.
ואגיד לך מאז בטרם תבוא השמעתיך--פן תאמר עצבי עשם ופסלי ונסכי צום | 5 |
Saboda haka na faɗa waɗannan abubuwa tuntuni; kafin su faru na yi shelarsu gare ku saboda kada ku ce, ‘Gumakana ne suka yi su; siffar itacena da allahn zinariyana ne ya ƙaddara su.’
שמעת חזה כלה ואתם הלוא תגידו השמעתיך חדשות מעתה ונצרות ולא ידעתם | 6 |
Kun riga kun ji waɗannan abubuwa; kuka gan su duka. Ba za ku yarda da su ba? “Daga yanzu zuwa gaba zan faɗa muku sababbin abubuwa, na ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba.
עתה נבראו ולא מאז ולפני יום ולא שמעתם--פן תאמר הנה ידעתין | 7 |
Yanzu an halicce su, ba da daɗewa ba; ba ku riga kun ji game da su kafin yau ba. Saboda haka ba za ku ce, ‘I, na san da su ba.’
גם לא שמעת גם לא ידעת--גם מאז לא פתחה אזנך כי ידעתי בגוד תבגוד ופשע מבטן קרא לך | 8 |
Ba ku ji ko balle ku gane ba; tun da kunnenku bai buɗu ba. Tabbatacce na san yadda kun zama masu tayarwa; an kira ku’yan tawaye daga haihuwa.
למען שמי אאריך אפי ותהלתי אחטם לך--לבלתי הכריתך | 9 |
Saboda girman sunana na jinkirta fushina; saboda girman yabona na janye shi daga gare ku, don dai kada a yanke ku.
הנה צרפתיך ולא בכסף בחרתיך בכור עני | 10 |
Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba; na gwada ku cikin wutar wahala.
למעני למעני אעשה כי איך יחל וכבודי לאחר לא אתן | 11 |
Saboda girmana, saboda girmana, na yi haka. Yaya zan ƙyale a ƙazantar da kaina? Ba zan raba ɗaukakata da wani ba.
שמע אלי יעקב וישראל מקראי אני הוא אני ראשון אף אני אחרון | 12 |
“Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub, Isra’ila, wanda na kira cewa, Ni ne shi; ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe.
אף ידי יסדה ארץ וימיני טפחה שמים קרא אני אליהם יעמדו יחדו | 13 |
Hannuna ne ya kafa harsashen duniya, hannuna na dama kuma ya shimfiɗa sammai; sa’ad da na kira su, duka suka miƙe tsaye gaba ɗaya.
הקבצו כלכם ושמעו מי בהם הגיד את אלה יהוה אהבו--יעשה חפצו בבבל וזרעו כשדים | 14 |
“Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara, Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa? Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna zai aikata nufinsa a kan Babilon; hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa.
אני אני דברתי אף קראתיו הבאתיו והצליח דרכו | 15 |
Ni kaina, na faɗa; I, na kira shi. Zan kawo shi, zai kuma yi nasara a cikin aikinsa.
קרבו אלי שמעו זאת לא מראש בסתר דברתי--מעת היותה שם אני ועתה אדני יהוה שלחני--ורוחו | 16 |
“Ku zo kusa da ni ku kuma saurari wannan. “Daga farkon shela ban yi magana a ɓoye ba; a lokacin da ya faru, ina nan a wurin.” Yanzu kuwa Ubangiji Mai Iko Duka ya aiko ni, da Ruhunsa.
כה אמר יהוה גאלך קדוש ישראל אני יהוה אלהיך מלמדך להועיל מדריכך בדרך תלך | 17 |
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya koya muku abin da ya fi muku kyau, wanda ya muku hanyar da za ku bi.
לוא הקשבת למצותי ויהי כנהר שלומך וצדקתך כגלי הים | 18 |
Da a ce kawai za ku mai da hankali ga umarnaina, da salamarku ta zama kamar kogi, adalcinku kamar raƙuman teku.
ויהי כחול זרעך וצאצאי מעיך כמעתיו לא יכרת ולא ישמד שמו מלפני | 19 |
Da zuriyarku ta zama kamar yashi,’ya’yanku kamar tsabar hatsin da ba a iya ƙidayawa; da ba za a taɓa yanke sunansu balle a hallaka su daga gabana ba.”
צאו מבבל ברחו מכשדים בקול רנה הגידו השמיעו זאת הוציאוה עד קצה הארץ אמרו גאל יהוה עבדו יעקב | 20 |
Ku bar Babilon, ku gudu daga Babiloniyawa! Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki ku kuma furta shi. Ku aika shi zuwa iyakokin duniya; ku ce, “Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.”
ולא צמאו בחרבות הוליכם--מים מצור הזיל למו ויבקע צור--ויזבו מים | 21 |
Ba su ji ƙishi ba sa’ad da ya bishe su a cikin hamada; ya sa ruwa ya malalo dominsu daga dutse; ya tsage dutse ruwa kuwa ya kwararo.
אין שלום אמר יהוה לרשעים | 22 |
“Babu salama ga mugaye” in ji Ubangiji.