< ישעה 45 >

כה אמר יהוה למשיחו לכורש אשר החזקתי בימינו לרד לפניו גוים ומתני מלכים אפתח--לפתח לפניו דלתים ושערים לא יסגרו 1
“Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi.
אני לפניך אלך והדורים אושר (אישר) דלתות נחושה אשבר ובריחי ברזל אגדע 2
Zan sha gabanka in baje duwatsu; zan farfashe ƙofofin tagulla in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe.
ונתתי לך אוצרות חשך ומטמני מסתרים למען תדע כי אני יהוה הקורא בשמך--אלהי ישראל 3
Zan ba ka dukiyar duhu, arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare, saboda ka san cewa ni ne Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.
למען עבדי יעקב וישראל בחירי ואקרא לך בשמך אכנך ולא ידעתני 4
Saboda sunan Yaƙub bawana, Isra’ila zaɓaɓɓena, na kira ka da suna na ba ka matsayin bangirma, ko da yake ba ka san ni ba.
אני יהוה ואין עוד זולתי אין אלהים אאזרך ולא ידעתני 5
Ni ne Ubangiji, kuma babu wani; in ban da ni babu wani Allah. Zan ƙarfafa ka, ko da yake ba ka san ni ba,
למען ידעו ממזרח שמש וממערבה כי אפס בלעדי אני יהוה ואין עוד 6
saboda daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta mutane za su san cewa babu wani in ban da ni. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
יוצר אור ובורא חשך עשה שלום ובורא רע אני יהוה עשה כל אלה 7
Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.
הרעיפו שמים ממעל ושחקים יזלו צדק תפתח ארץ ויפרו ישע וצדקה תצמיח יחד--אני יהוה בראתיו 8
“Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama; bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci. Bari ƙasa ta buɗe, bari ceto ya tsiro, bari adalci ya yi girma tare da shi; ni, Ubangijine, na sa ya faru.
הוי רב את יצרו--חרש את חרשי אדמה היאמר חמר ליצרו מה תעשה ופעלך אין ידים לו 9
“Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka, da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa. Yumɓu ya iya ce wa magini, ‘Me kake yi?’ Aikinka na iya cewa, ‘Ba shi da hannuwa’?
הוי אמר לאב מה תוליד ולאשה מה תחילין 10
Kaiton wanda yake cewa mahaifinsa, ‘Me ka manta?’ Ko kuwa ga mahaifiyarsa, ‘Me kin haifa?’
כה אמר יהוה קדוש ישראל ויצרו האתיות שאלוני על בני ועל פעל ידי תצוני 11
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa. Game da abubuwan da ke zuwa, kun tambaye ni game da’ya’yana, ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana?
אנכי עשיתי ארץ ואדם עליה בראתי אני ידי נטו שמים וכל צבאם צויתי 12
Ai, ni ne wanda ya yi duniya na kuma halicci mutum a kanta. Hannuwana ne sun miƙe sammai; na umarci rundunar sararin sama.
אנכי העירתהו בצדק וכל דרכיו אישר הוא יבנה עירי וגלותי ישלח--לא במחיר ולא בשחד אמר יהוה צבאות 13
Zan tā da Sairus cikin adalcina. Zan sa dukan hanyoyinsa su miƙe. Zai sāke gina birnina ya kuma’yantar da mutanena masu bautar talala, amma ba don wata haya ko lada ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
כה אמר יהוה יגיע מצרים וסחר כוש וסבאים אנשי מדה עליך יעברו ולך יהיו אחריך ילכו בזקים יעברו ואליך ישתחוו אליך יתפללו אך בך אל ואין עוד אפס אלהים 14
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kayayyakin Masar da hajar Kush, da waɗannan dogayen Sabenawa, za su ƙetaro zuwa wurinku za su kuma zama naku; za su bi bayanku, suna zuwa cikin sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su roƙe ku, suna cewa, ‘Tabbas Allah yana tare da ku, babu kuma wani; babu wani allah.’”
אכן אתה אל מסתתר--אלהי ישראל מושיע 15
Tabbatacce kai ne Allah wanda ya ɓoye kanka, Ya Allah da Mai Ceton Isra’ila.
בושו וגם נכלמו כלם יחדו הלכו בכלמה חרשי צירים 16
Dukan masu yin gumaka za su sha kunya; za su fita da kunya gaba ɗaya.
ישראל נושע ביהוה תשועת עולמים לא תבשו ולא תכלמו עד עולמי עד 17
Amma Ubangiji zai ceci Isra’ila da madawwamin ceto; ba za ku sāke shan kunya ko ƙasƙanci ba, har abada.
כי כה אמר יהוה בורא השמים הוא האלהים יצר הארץ ועשה הוא כוננה--לא תהו בראה לשבת יצרה אני יהוה ואין עוד 18
Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci sammai, shi ne Allah; shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya, ya kafa ta; bai halicce ta don ta zama ba kome ba, amma ya yi ta don a zauna a ciki, ya ce, “Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
לא בסתר דברתי במקום ארץ חשך--לא אמרתי לזרע יעקב תהו בקשוני אני יהוה דבר צדק מגיד מישרים 19
Ban yi magana asirce ba, daga wani wuri a ƙasar duhu ba; ban faɗa wa zuriyar Yaƙub, ‘Ku neme ni a banza ba.’ Ni, Ubangiji maganar gaskiya nake yi; na furta abin da yake daidai.
הקבצו ובאו התנגשו יחדו פליטי הגוים לא ידעו הנשאים את עץ פסלם ומתפללים אל אל לא יושיע 20
“Ku tattaru ku zo; ku taru, ku masu gudun hijira daga al’ummai. Masu jahilci ne waɗanda suke ɗaukan gumakan katakai suna yawo, waɗanda suke addu’a ga allolin da ba za su cece su ba.
הגידו והגישו אף יועצו יחדו מי השמיע זאת מקדם מאז הגידה הלוא אני יהוה ואין עוד אלהים מבלעדי--אל צדיק ומושיע אין זולתי 21
Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi, bari su yi shawara tare. Wa ya faɗa wannan tuntuni, wa ya yi shelar sa a kwanakin dā? Ba ni ba ne, Ubangiji? Kuma babu Allah in ban da ni, Allah mai adalci da kuma Mai Ceto; babu wani sai ni.
פנו אלי והושעו כל אפסי ארץ כי אני אל ואין עוד 22
“Ku juyo gare ni ku sami ceto, dukanku iyakokin duniya; gama ni ne Allah, kuma babu wani.
בי נשבעתי--יצא מפי צדקה דבר ולא ישוב כי לי תכרע כל ברך תשבע כל לשון 23
Da kaina na rantse, bakina ya furta cikin dukan mutunci kalmar da ba za a janye ba. A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa; ta wurina kowane harshe zai rantse.
אך ביהוה לי אמר צדקות ועז עדיו יבוא ויבשו כל הנחרים בו 24
Za su yi zance game da ni su ce, ‘A cikin Ubangiji kaɗai akwai adalci da kuma ƙarfafawa.’” Duk wanda ya yi fushi da shi zai zo wurinsa ya kuma sha kunya.
ביהוה יצדקו ויתהללו כל זרע ישראל 25
Amma a cikin Ubangiji dukan zuriyar Isra’ila za su sami adalci za su kuwa yi yabo.

< ישעה 45 >