< ישעה 27 >
ביום ההוא יפקד יהוה בחרבו הקשה והגדולה והחזקה על לויתן נחש ברח ועל לויתן נחש עקלתון והרג את התנין אשר בים | 1 |
A wannan rana, Ubangiji zai yi hukunci da takobi, takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna, zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe, dodon ruwa macijin nan mai murɗewa; zai kashe dodon nan na teku.
ביום ההוא כרם חמר ענו לה | 2 |
A wannan rana, “Ku rera game da gonar inabi mai ba da’ya’ya ku ce
אני יהוה נצרה לרגעים אשקנה פן יפקד עליה לילה ויום אצרנה | 3 |
Ni, Ubangiji na lura da ita; na yi ta yin mata banruwa. Na yi tsaronta dare da rana don kada wani yă yi mata ɓarna.
חמה אין לי מי יתנני שמיר שית במלחמה--אפשעה בה אציתנה יחד | 4 |
Ban yi fushi ba. Da a ce ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suke kalubalanta na mana! Zan fita in yi yaƙi da su; da na sa musu wuta duka.
או יחזק במעוזי יעשה שלום לי שלום יעשה לי | 5 |
Ko kuma bari su zo wurina don mafaka; bari su yi sulhu da ni, I, bari su yi sulhu da ni.”
הבאים ישרש יעקב יציץ ופרח ישראל ומלאו פני תבל תנובה | 6 |
A kwanaki masu zuwa Yaƙub zai yi saiwa, Isra’ila zai yi toho ya kuma yi fure ya cika dukan duniya da’ya’ya.
הכמכת מכהו הכהו אם כהרג הרגיו הרג | 7 |
Ubangiji ya buge shi kamar yadda ya bugi waɗanda suka buge shi? An kashe shi kamar yadda aka kashe waɗanda suka kashe shi?
בסאסאה בשלחה תריבנה הגה ברוחו הקשה ביום קדים | 8 |
Ta wurin yaƙi da zaman bauta ka hukunta shi, da tsananin tsawa kuma ka kore shi, kamar a ranar da iskar gabas ta hura.
לכן בזאת יכפר עון יעקב וזה כל פרי הסר חטאתו בשומו כל אבני מזבח כאבני גר מנפצות לא יקמו אשרים וחמנים | 9 |
A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub, wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa. Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu, har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare da za a bari a tsaye.
כי עיר בצורה בדד נוה משלח ונעזב כמדבר שם ירעה עגל ושם ירבץ וכלה סעפיה | 10 |
Birni mai katanga ya zama kufai, yasasshen mazauni, an yashe shi kamar hamada; a can’yan maruƙa suke kiwo, a can suke kwance; sun kakkaɓe rassanta ƙaf.
ביבש קצירה תשברנה נשים באות מאירות אותה כי לא עם בינות הוא--על כן לא ירחמנו עשהו ויצרו לא יחננו | 11 |
Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su mata kuma su zo su yi itacen wuta da su. Gama mutane ne marar azanci; saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba, Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba.
והיה ביום ההוא יחבט יהוה משבלת הנהר עד נחל מצרים ואתם תלקטו לאחד אחד בני ישראל | 12 |
A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya.
והיה ביום ההוא יתקע בשופר גדול ובאו האבדים בארץ אשור והנדחים בארץ מצרים והשתחוו ליהוה בהר הקדש בירושלם | 13 |
Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima.