< הושע 14 >

שובה ישראל עד יהוה אלהיך כי כשלת בעונך 1
Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku. Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku!
קחו עמכם דברים ושובו אל יהוה אמרו אליו כל תשא עון וקח טוב ונשלמה פרים שפתינו 2
Ku ɗauki magana tare da ku ku komo wurin Ubangiji. Ku ce masa, “Ka gafarta mana dukan zunubanmu ka kuma karɓe mu da alheri, don mu iya yabe ka da leɓunanmu.
אשור לא יושיענו על סוס לא נרכב ולא נאמר עוד אלהינו למעשה ידינו--אשר בך ירחם יתום 3
Assuriya ba za su iya cece mu ba; ba za mu hau dawakan yaƙi ba. Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’ wa abin da hannuwanmu suka yi ba, gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.”
ארפא משובתם--אהבם נדבה כי שב אפי ממנו 4
“Zan gyara ɓatancinsu in kuma ƙaunace su a sake, gama fushina ya juya daga gare su.
אהיה כטל לישראל יפרח כשושנה ויך שרשיו כלבנון 5
Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila zai yi fure kamar lili. Kamar al’ul na Lebanon zai sa saiwarsa zuwa ƙasa;
ילכו ינקותיו ויהי כזית הודו וריח לו כלבנון 6
tohonsa za su yi girma. Darajarsa za tă zama kamar itacen zaitun, ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon.
ישבו ישבי בצלו יחיו דגן ויפרחו כגפן זכרו כיין לבנון 7
Mutane za su sāke zauna a inuwarsa. Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi. Zai yi fure kamar kuringa, zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.
אפרים מה לי עוד לעצבים אני עניתי ואשורנו אני כברוש רענן--ממני פריך נמצא 8
Efraim zai ce, me kuma zai haɗa ni da gumaka? Zan amsa masa in kuma lura da shi. Ni kamar koren itacen fir ne; amincinka yana fitowa daga gare ni ne.”
מי חכם ויבן אלה נבון וידעם כי ישרים דרכי יהוה וצדקים ילכו בם ופשעים יכשלו בם 9
Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa. Hanyoyin Ubangiji daidai ne; masu adalci sukan yi tafiya a kansu, amma’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.

< הושע 14 >