< בראשית 28 >

ויקרא יצחק אל יעקב ויברך אתו ויצוהו ויאמר לו לא תקח אשה מבנות כנען 1
Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana.
קום לך פדנה ארם ביתה בתואל אבי אמך וקח לך משם אשה מבנות לבן אחי אמך 2
Tashi nan da nan ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan mahaifin mahaifiyarka Betuwel. Ka ɗauko wa kanka mata a can daga cikin’ya’ya matan Laban ɗan’uwan mahaifiyarka.
ואל שדי יברך אתך ויפרך וירבך והיית לקהל עמים 3
Bari Allah Maɗaukaki yă albarkace ka, yă kuma sa ka yi ta haihuwa ka riɓaɓɓanya har ka zama ƙungiyar jama’o’i.
ויתן לך את ברכת אברהם לך ולזרעך אתך--לרשתך את ארץ מגריך אשר נתן אלהים לאברהם 4
Bari Allah yă ba ka da kuma zuriyarka albarkar da ya ba wa Ibrahim, don ka amshi ƙasar da kake baƙunci, ƙasar da Allah ya ba wa Ibrahim.”
וישלח יצחק את יעקב וילך פדנה ארם--אל לבן בן בתואל הארמי אחי רבקה אם יעקב ועשו 5
Sa’an nan Ishaku ya sallami Yaƙub, ya kuwa tafi Faddan Aram, zuwa wurin Laban ɗan Betuwel mutumin Aram. Laban ne ɗan’uwan Rebeka, wadda take mahaifiyar Yaƙub da Isuwa.
וירא עשו כי ברך יצחק את יעקב ושלח אתו פדנה ארם לקחת לו משם אשה בברכו אתו--ויצו עליו לאמר לא תקח אשה מבנות כנען 6
Yanzu Isuwa ya san cewa Ishaku ya albarkaci Yaƙub ya kuma aike shi zuwa Faddan Aram don yă auri mata daga can, ya kuma san cewa sa’ad da ya albarkace shi, ya umarce shi cewa, “Kada ka auro wata mace daga cikin Kan’aniyawa,”
וישמע יעקב אל אביו ואל אמו וילך פדנה ארם 7
ya kuma san cewa Yaƙub ya yi biyayya da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa, ya kuwa tafi Faddan Aram.
וירא עשו כי רעות בנות כנען בעיני יצחק אביו 8
Sai Isuwa ya gane cewa matan Kan’aniyawa ba su gamshi mahaifinsa Ishaku ba;
וילך עשו אל ישמעאל ויקח את מחלת בת ישמעאל בן אברהם אחות נביות על נשיו--לו לאשה 9
saboda haka sai ya tafi wurin Ishmayel ya auri Mahalat,’yar’uwar Nebayiwot da kuma’yar Ishmayel ɗan Ibrahim, ban da matan da yake da su.
ויצא יעקב מבאר שבע וילך חרנה 10
Yaƙub ya bar Beyersheba ya kama hanyar Haran.
ויפגע במקום וילן שם כי בא השמש ויקח מאבני המקום וישם מראשתיו וישכב במקום ההוא 11
Sa’ad da ya kai wani wuri, sai ya dakata domin yă kwana, gama rana ta riga ta fāɗi. Ya ɗauki dutse daga cikin duwatsun wurin, ya sa shi ya zama matashin kansa, sa’an nan ya kwanta don yă yi barci.
ויחלם והנה סלם מצב ארצה וראשו מגיע השמימה והנה מלאכי אלהים עלים וירדים בו 12
Ya yi mafarki inda ya ga wata matakalar hawa, tsaye a ƙasa, kanta ta kai sama, mala’ikun Allah kuwa suna hawa, suna sauka a kanta.
והנה יהוה נצב עליו ויאמר אני יהוה אלהי אברהם אביך ואלהי יצחק הארץ אשר אתה שכב עליה--לך אתננה ולזרעך 13
A can bisantaUbangiji ya tsaya, ya kuma ce, “Ni ne Ubangiji Allah na mahaifinka Ibrahim da kuma Allah na Ishaku. Zan ba ka, kai da kuma zuriyarka, ƙasar da kake kwance a kai.
והיה זרעך כעפר הארץ ופרצת ימה וקדמה וצפנה ונגבה ונברכו בך כל משפחת האדמה ובזרעך 14
Zuriyarka za tă zama kamar ƙurar ƙasa, za ka kuma bazu zuwa yamma da kuma gabas, zuwa arewa da kuma kudu. Dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka da kuma ta wurin’ya’yanka.
והנה אנכי עמך ושמרתיך בכל אשר תלך והשבתיך אל האדמה הזאת כי לא אעזבך עד אשר אם עשיתי את אשר דברתי לך 15
Ina tare da kai, zan lura da kai duk inda ka tafi, zan kuma dawo da kai zuwa wannan ƙasa. Ba zan rabu da kai ba sai na cika abin da na yi maka alkawari.”
וייקץ יעקב משנתו ויאמר אכן יש יהוה במקום הזה ואנכי לא ידעתי 16
Sa’ad da Yaƙub ya farka daga barci, sai ya yi tunani ya ce, “Tabbatacce Ubangiji yana a wannan wuri, ban kuwa sani ba.”
ויירא ויאמר מה נורא המקום הזה אין זה כי אם בית אלהים וזה שער השמים 17
Ya ji tsoro, ya kuma ce, “Wane irin wuri ne mai banrazana haka! Lalle wannan gidan Allah ne, kuma nan ne ƙofar sama.”
וישכם יעקב בבקר ויקח את האבן אשר שם מראשתיו וישם אתה מצבה ויצק שמן על ראשה 18
Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa.
ויקרא את שם המקום ההוא בית אל ואולם לוז שם העיר לראשנה 19
Ya kira wannan wuri Betel ko da yake dā ana kiran birnin Luz ne.
וידר יעקב נדר לאמר אם יהיה אלהים עמדי ושמרני בדרך הזה אשר אנכי הולך ונתן לי לחם לאכל ובגד ללבש 20
Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa,
ושבתי בשלום אל בית אבי והיה יהוה לי לאלהים 21
har in dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubangiji zai zama Allahna
והאבן הזאת אשר שמתי מצבה--יהיה בית אלהים וכל אשר תתן לי עשר אעשרנו לך 22
kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.”

< בראשית 28 >